Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na tabbatar masa da cewa; ni ban yarda da wannan hasashen ba, na fi yarda da cewa; Ubangiji ne kawai yake saukar da ikonsa akaina, domin shi yake bayar wa, kuma shi yake hana wa, sai kuma tasirin addu'ar iyaye na dake bibiyar rayuwarta. Hajiya na mutu'kar ha'kurin zama da Zinaru domin rashin kunya take mata sosai! bata shakkar zaginta a ko'ina, ga gori kala-kala! duk ranar da Shukura tayi gangancin mayar mata da martani, to babu zaman lafiya a gidan, domin dukan tsiya take mata har sai ta fitar da mata da jini, 'karfi ne da ita sosai! wanda na tabbata da cewa; aljanun da take tare da ita ne suke tunzurata aikata munanan ayyuka! domin wasu lokutan na sha farkawa daga bacci na ganta a tsaye a kaina da wu'ka! sai nayi namijin 'ko'kari! nake fita daga dakin, wannan dalilin ya sa na daina kwana a d'akinta, sai dai duk ranar da take da wata bu'kata sai kawo kanta d'aki na. Ranar Asabar ban fita ba saboda ba na jin dadi, cikin baccin da nake na dinga jin hayaniya! a firgice! na tashi zaune, ina kiran sunan Allah. can na ji muryarta tana d'urawa Hajiya zagi! rai na a 'bace! na tashi na fita sai na same ta tsaye a kan Hajiyan tana nu na ta da yatsa sai rashin mutunci take mata, Hajiyan kanta a sunkuye sai share hawaye take, raina ya 'baci mutuk'a! mari na tsinka mata tare da yin ball da ita gurin! Hajiya ta rirri'ke ni tana bani hak'uri! ina sake kai mata duka da 'kafata! ji nake kamar na fashe da kuka saboda ba'kin ciki, tabbas auran Zinaru bai 'kare ni da komai ba sai tozarci! kai na tayo tana kuka ta ci kwalar riga ta ta dinga zagi na tana kuka wai dole sai na sake ta, ko kuma ta kashe ni. Nayi-nayi na k'wace! daga hannunta na kasa saboda ri'kon kamar ba nata ba, zagi na take ta uwa ta uba, bakinta duk ya tara wata irin kumfa! a lokacin na tsorata! sosai sai kawai na dinga karanta mata ayatul-kursiyu ina tofa mata a fuska! hakan yasa ta sassaura ri'kon da tayi min, na finkice! da sauri na nufi d'aki na. Kafin nayi wani yun'kuri! ta shigo dakin, ta buga 'kofar da k'arfi ta rufe! tayo kaina! da kokawa sosai ta kama ni! mu dinga bi kusurwa-kusurwa da ita, nayi mamakin 'karfinta dan ban samu galaba a kanta ba, da 'kyar! na samu na rarrashe ta na ce ta zauna muyi magana ta fahimta, ta ce itafa ba zata zauna ba sai na rubuta mata takardar saki. na ce ni ba zan sake ta ba har abada domin al'kawari nayi wa d'an uwanta. nan ta tabbatar min da cewa; wallahi sai ta kashe ni mutu'kar ban rabu da ita ba. jin haka sai jikina yayi sanyi na kalle ta tare da fad'in" Zaki iya kashe ni Zinaru? ta ce" 'Kwarai kuwa mutukar baka rubuta min takardar saki ba. na ce to shikkenan kiyi hakuri zanyi shawara ki bani kwana biyu. jin haka yasa ta sakar min wuyan riga ta fita daga d'akin tana numfarfashi! Kwana nayi ina tunanin hanyar da zan bi gurin ganin nayi wa tufkar hanci, tabbas Zinaru tana iya kashe ni tunda ta furta to hakan yake a zuciyarta, maslaha kawai na samu d'an uwanta da maganar domin mu tattauna. Alhaji Harazimi bai yi mamakin jin haka daga gare ni ba, ya ce." Abinda ya fi haka Zinaru za ta aikata, shiyasa na ce maka wasu lokotan ba ita take aikatawa wasu abubuwan ba, mutanan da suke tare da ita ne, amma ina 'kara neman alfarma a gurinka, wannan ita ce ta 'karshe idan abin ya ci tura to na baka wu'ka da nama ka sake ta domin ba zan bari ta cutar da kai ba. Na ce" Alhaji wace alfarma ce wannan?" Ya ce" Za mu d'auko malamai su yi mata ru'kiya idan Allah yasa an dace iskokin sun rabu da ita shikkenan, domin dana ta'ba tuntu'bar wani malami da maganar, nan yake tabbatar min da cewa; iskokin da suke tare da ita da wuya su rabu da ita saboda na gado ne, wallahi tun daga lokacin jikina yayi sanyi, domin ba zan manta ba, Mahaifiyarmu ma haka tayi ta fama dasu a lokotan baya, don dai ita tana da rik'o da addini ne shiyasa basa wahalar da ita sosai. Ajiyar zuciya na sauke na ce"Shikkenan Alhaji yanda ka ce hakan za 'ayi ina rokon Allah yasa ayi asa'a, domin ni kaina ina tausaya mata wallahi, gabad'aya daga ni har ita muna cikin tashin hankali da damuwa." To malamai uku ne suka rufu a kan Zinaru suna ta karatu har sai da suka sauke al'kur'ani mai girma kana suka fara karatun ru'kiya! a lokacin bacci ne ya kwashe ta wanda ta d'auki tsayin kwana uku ta nayi, domin ni har na tsorata da al'amarin, sai da na kira d'aya daga cikin malaman ya kwantar min da hankali, tare da fad'in" Insha Allahu za ta tashi. Washe gari kwana hud'u kenan, ta tashi idonta cike da kwansa! fuskarta duk ta zurma! gabad'aya ta fita daga hayyacinta, sosai ta bani tausayi don da kaina na had'a mata ruwan wanka na ri'ke hannunta muka shiga band'akin tare na taimaka mata tayi wankan. Kwanciya tayi kan gado bayan ta shirya jikinta tayi lamo! tare da tsirawa rufin d'akin ido, na ce" Kina jin yunwa ko?" kai ta d'aga min alamar Eh, na fita da sauri, na umarci Shukura ta shirya abinci ta kai mata, tare suka shiga da Hajiya suka duba jikinta kafin su fito jikinsu duk a sanyaye! domin duk wanda ya ga Zinaru a lokacin sai ya tausaya mata duba da yanda hallitun ta suka sauya. Sati biyu da faruwar al'amarin. ta warware sosai! kuma muna zaman lafiya domin wata hatsaniya bata sake faruwa ba, tsakaninta da Hajiya ma babu wata matsala. hakan ya sa hankali na ya kwanta, sosai na dinga godewa Allah. na cigaba da gudanar da harkokina na yau da gobe. Ranar talata ya kama kwana ashirin da biyar da yi mata Ru'kiyar muka nema ta muka rasa a gidan. hankali na a tashe na kira wayarta ina tambayarta. kai tsaye ta ce min ta na Swaziland ('kasar waje) gabana na fad'uwa na ce" Me ki ka je yi a can?" Ta ce" Aure za tayi tare da tsohon saurayinta wanda yake aiki a can.'' wani kuttun! bakin ciki ya tokare min a wuya, na ce "Zinaru da aure na za ki auri wani?" ta ce" Eh man, yanzu ai ka sake ni don dole! bana k'aunarka munafiki macuci kawai." Kashe wayar nayi sai kwai na zube a gurin tare da dafe kaina. "Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! ka kawai na kira, har na samu sassauci! na dauki waya na kira d'an uwanta na sheda masa halin da ake ciki. cikin 'bacin rai ya ce." Saddiku yanzu na tabbatar da cewa; idan da akwai iska a tare da Zinaru, to akwai hali, wallahi nayi iyakar bakin 'ko'kari na don haka na gaji, na gode sosai da alfarmar da kayi min, saboda haka ka rubuta takardar sakin yarinyar nan ka aiko min da ita, dama ni ne na

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});