Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Majanuni Book 4 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

domin kuwa shine abin alfaharin kowace 'ya mace, da kansa ya kai ni band'aki tare da had'a min ruwan wanka yana tattare hannun riga ya ce" Ko nayi miki wankan ne?" Kai na girgiza! alamar A'a na tsuguna sai kace wata sabuwar maijego gabana ciwo kawai yake min, ba tare da na kalle shi ba na ce" Ka d'an had'a min wani ruwan amma kada yayi zafi sosai. Da sauri ya had'a min ya taimaka min na shiga ruwan na zauna, rintse idona nayi sosai lokacin da zafin ruwan ke ratsa jikina, zugi da zafi suka sanya hawaye zubo min. Duk sai ya tashi hankalinsa yana ta bani hakuri, juye-juye kawai naka a ruwan kamar na fito, wata zuciyar ta hana ni, nasan cewa ruwan zafin shine zai dakusar da ciwon dake gurin. Hannunsa ya tsumbula cikin ruwan yana so ya ta'ba gurin "Ko dai na sa likita ta zo ta duba ki?" yana maganar yana so yasa hannanusa a gurin, ina kaucewa, na ce" A'a zai daina ciwon insha Allah. Ya ce." Ina so na gani ne domin hankalina ya kwanta. Kallonsa nayi naga da gaske yake maganarsa, na ce"A'a ba sai ka gani ba. Cikin wata irin murya mai taushi ya ce." Saboda me? bayan na zama wani jigo a rayuwarki, kin zama ni, na zama ke, meye abin jin kunya. Shiru nayi, domin bana tsammanin zan nuna masa. Ya fara 'kokarin tayar dani tsaye wai dole sai ya gani, kuka nasa tare da ri'ke bahon ruwan ina ture hannunsa da fad'in" Ka fita ni dai." Fita yayi ya bar ni a band'akin ba don ransa ya so ba. Na jima cikin ruwan d'umin. sannan nayi wankan tsarki! na fito na d'aure da towel mai girma a jikina. Ko da na fito baya cikin d'akin, amma ga kaya na nan, ya ajiye min a kan gado. Na shirya cikin atamafa java mai ruwan ganye kuma dinki yayi min cif! a jikina, mai kawai na shafa tare da fesa d'aya daga cikin turarunkansa dake jibge a kan madubi, na gabatar da sallar asubah da ta wuce ni, kafin na rarrafa na hau gado na kwanta bacci ne fal a cikin idona, ga wani irin ciwo da jikina keyi min, abu dai goma da ashirin! sun dabaibaye ni, jiya dai na yabawa aya za'kinta, har bana so na tuna gumurzun da mu kayi saboda tsigar jikina ce take tashi, amma na godewa Allah da ni'imar da yayi min, duk isar mace mutuncinta ta kai budurcinta gidan mijinta, na yi farin ciki da ya same ni cikakkiyar mace, kuma yanda na fahimta ya samu gamsuwa da ni ko ga irin addu'ar da yake min tare da d'aukar min al'kawari iri-iri, cikin zuciyata nake adduar Allah yasa hakan yake a zuciyarsa, don gaskiya bana k'aunar kishiya duk da na san umarni ne na Ubangiji amma ni kam na fi buk'atar na zauna ni kad'ai da mijina. Tare suka shigo d'akin da Hajiya, sai nayi saurin rufe idona, kunya nake ji kada ta fahimci wani abu ya faru. ashe zuwa yayi ya fad'a mata abinda ya ke da akwa. shine ta shigo ta duba ni. Kamar na fashe da kuka saboda takaici! ban iya cewa komai saboda nauyi da jin kunya baccin 'karya na tsira, ina jin suna ta maganganu nayi luf! sai da ta fita daga dakin sannan na bud'e idona na kalle shi. yana zaune kusa da k'afafuna yana waya! Cikin dubara na tashi zaune na d'an jingina da fuskar gado! ganin na tashi yasa ya katse wayar da ya kalle ni, cikin kulawa ya ce." Sannu kin ga yanzu Hajiya ta fita ta shigo duba ki." Zum'bara baki nayi tare da fad'in" Me yasa ka fad'a mata wani abu ya faru a tsakaninmu?" "Me yasa ba zan fad'a mata ba? bayan ta damu da nayi aure na haihu, sannan kuma yanda ki ke kuka da gurin shi ya bani tsoro na je na sanar da ita ko da wani taimakon da za tayi mana." Yafad'a idonsa a tsaye a kaina. Na ce" Gurin fa zai dusashe in sha Allahu. To "Allah ya yarda, amma na yi waya da likitana duk nayi masa bayani abinda ke da akwai, ya bani tabbacin cewa; idan ana bu'katar gurin ya zama normal sai an 'kara wani abun, shine na ce ko zaki bari nayi wani yanzu ko da sau d'aya ne. "Bangane ba." Na fad'a gabana na duk uku-uku! don gabad'aya hankalina ya tashi jin abinda ya ke fad'a. Sai ya fashe da dariya yana kallona. Ganin haka yasa na juya masa baya domin na fahimci tsokanata yake. Da sauran dariyar a tare da shi ya ri'ke hannuna da fad'in" Da wasa nake miki my love ba zan miki komai ba sai gurin ya warke in sha Allahu." Ba tare da na juyo ba na ce" Ka tabbata?" Shiru yayi be bani amsa ba. Shukura ta shigo da'kin da sallama a bakinta. shi ne ya amsa, ni kam kunya tasa na rufe idona, ina 'kokarin 'kwace hannuna dake cikin nasa, ya ri'ke da kyau! 'Bangaran Shukura kuwa ganin ta, kwance lakadan a gadon mahaifinta, sai wani bakin ciki ya turnu'ke ta, ga shi kuma a zaune ya kusa da ita hannunsa cikin nata, kamar ta kurma ihu! saboda takaici. A sanyaye ta ajiye kwandon abincin dake hannunta, ta ce"Daddy ina kwana?" Ya amsa cikin kulawa yana nazarin fuskarta domin ya hango damuwa a tare da ita. Sai da ta daure zuciyarta sannan ta ce" Antina ina kwana." Ba tare dana kalle ta ba na amsa da "Lafiya lau." daga haka ban ce komai ba, amma cike nake da mamaki ya akayi yarinyar ta sauko har take gaishe ni. Ta ce"Daddy Hajiya ta ce na kawo muku abin karin kummalo idan anti ba za ta iya saukowa 'kasa ba" Hankalinsa gabad'aya yana kaina ya bata amsa da cewar" To babu laifi hakan." Hanyar fita ta nufa jikinta duk a sanyaye. sai kuma ta kasa daurewa ta tsaya tana kallonsa kafin ta ce"Daddy ya maganar da mu kayi da kai kwana biyu da ya wuce?" Ya ce." Wace magana kuma?" domin shi ya manta ma sunyi wata magana. Ta ce" Akan dawowar Mommyna d'akinta da kuma al'kawarin da kayi min." Tsawa! ya buga mata tare da nuna mata hanyar fita. " Wuce ki bani guri shashashar banza." Da saurin gaske ta bud'e k'ofar ta fita tana sgare hawaye. Na kalleshi sai na ga duk babu walwala a tare dashi. Na ce" Ya za ayi ka kore ta har kana yi mata tsawa! kada fa ka janyo min 'bakin jini, Shukura 'yar ka ce bai kamata kayi haka ba." Babu fara'a a tattare dashi ya ce." Ke a ganinki abinda tayi ya da ce?" Ido na tsira masa da fad'in." Magana kayi da ita har kayi mata al'kawari lefi ne don ta sake tuntu'barka da maganar. Ya ce." A'a ni ban yi mata al'kawarin dawo da mamanta ba, ta dame ni da maganar sai na ce mata zan duba na gani." Dama abinda nake so na ji kenan daga bakinsa. Sai kawai nayi shiru raina gabad'aya ya 'baci! ban san me yasa ba haka kawai nake jin kishin matan da yayi tarayya dasu duk da cewa a

Table of Contents

Chapters

28 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});