Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Zaheedah Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

taje tayi wanka ta kwanta don zuciyarta ke tashi duk cikin symptoms din MP dinta kenan ta samu bacci yadan dauke ta bata farka ba sai bayan magrib shima wani gigitaccen ciyo ne ya tada ta. Ta kama kuka 😭ita Kadai tasan abinda ke damunta ji take qasanta kamar ya fado saboda azaba. Shi kuwa boss din sai wurin 9 ya shigo gidan ya watsa ruwa ya nufi dining yaga wayam ba komai. Yace to yau ya akayi kuma Mamy bata aiko da abinci ba har wurin 10 yace bari na kirata don na riga na saba da delicious food dinnan. Mamy ya kira sai da suka gama gaisawa sannan yake ce mata Mamy Nah yau ya aka yi baa aiko mana da abinci ba. Mamy cikin rashin fahimta tace wane abinci kuma. Yace abincin da ake aiko mana dashi tace to mu yaushe rabon da mu aiko maku da abinci tun two weeks da bikin ku. Yace Mamy wake mana girki kenan tace yana wuce Heedah kuwa tace ya akayi ne yace ba komi naga ba dinner ne bisa dining. Mamy tace to kuwa tabbas Heedah ba lfy ba tunda har batayi girki ba. Tace kaje ka ganin mun ita yace tohm ya kashe wayar sa yana mamakin dama yarinyar nan ke mani wannan delicious girkin lallai a gaisheta. Tashi yy don tuna aiken Mamy data ce ya dubo mata ....... Tun kafin ya shiga dakin yakejin nishinta kamar wacce ake fidda ma rai da sauri ya fada dakin............... πŸ˜‰ Written by the πŸ’…πŸŒŸβœ¨DIVASπŸŒŸβœ¨πŸ’… Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Junia. [2/4, 9:19 PM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’1⃣9⃣ Da sauri ya qarasa bakin bed din don hangota da yayi tana murqususu a bisa bed din sai nishi take. Yace ke lfy bata iya ce mishi komi ba sai nishin da takeyi. Ganin yarinyar mutane zata mutu yai saurin qarasawa ya dago ta. Ke wai me yasameki ne hankalin shi ya fara tashi ganin tana mimmiqewa. Ke kada fa ki mutun man ganin kamar bata nunfashi yasashi rudewa ya ciccibeta ya sata mota sai hospital πŸ₯. Emergency room aka shiga da ita doctors uku ne kanta sai da suka gama mata komai suka mata allurar bacci aka kaita dakin hutu. Wani doctor ne yace ma Yah Deel ya biyoshi. Sai da suka xauna sannan doctor n ya fara bayani. Wato yarinyarnan ba komi ke damunta ba illah MP. is not on common for women to have major problem during their period but her case is worst than we expected. Don haka zan baku shawarar a gaggauta yi mata aure saboda wasu matan da sunyi aure suke dainawa in ma basu daina ba da sun haihu inshaa Allah suke bari. That's all what I advise you to do. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Dakin da aka kwantar da ita ya nufa sai lokacin ya tuna ya kira Mamy ya sanar da ita suna hospital. Mamy duk ta rude tace kuna wane hospital ne. Yace Mamy yanzu ai dare yy kiyi haquri sai in Allah ya kaimu sai kizo tace wa zai kwana wurinta sai da yy dan jim sannan yace zan kwana kada ki damu. Mamy cikin mamakin dan nata tace to Allah ya bata lfy................... Written by the πŸ’…πŸŒŸβœ¨DIVASπŸ’…πŸŒŸβœ¨ Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia. [2/7, 3:48 PM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’2⃣0⃣ Tun da sassafe su Mamy suka iso duk hankalinsu a tashe sai tambayar meya sameta. Mamy da taje bakin gadon ta riqe hannun Heedah sai Daddy dake zaune bisa kujera su Goggo kuwa suna zaune bisa carpet. Daddy ya kalli Deel ya ce wai me ke damunta ne. Gogan naku ba abinda ya fito bakinsa sai "Doctor yace a mata aure". Dukkansu kallonsa suka yi cikin mamaki. Mamy tai mai daquwa tace ungo nan. Daddy yace baccin auran da take dashi wani zaa qara mata. Goggo dai dariya tayi tace ku qalesa. Mamy tace ka fada mana meke damun ta. Yah Deel yace doctor yace wai MP ke damunta. Mamy tace oh ni yasu dama wai har yanzu bata bar wannan ciwon ba. Tace wai Goggo daman ba da anyi aure ake bari ba, Goggo tace ya danganta kuma bakya ganin baa dade dayin auren ba. Duk wannan abin da ake boss din ya tashi yy tafiyarsa gida domin yin wanka. Nan su Mamy suka wuni koda ta tashi da ciwon cikin ta tashi tasha kuka dakyar aka bata abinci taci ai kuwa sai amai nan doctor ya shigo dubata yace kada su damu ba sai an bata komi ba zasu samata ruwa. Sannan a samu ruwa masu dan zafi a sasu cikin bottle a ringa danna mata a mara. Godiya su Mamy suka masa sannan suka yi yadda yace. Sai da dare sannan ya koma ya qara yi musu ya jiki yayi tafiyarsa gida yy kwanciyarsa. Sai data kwana hudu a hospital πŸ₯ sannan aka sallame su. Kai tsaye gida aka wuce da ita. Shi kuwa ba abinda ke damunsa sai harkarsa yake. Abu daya yake damunsa rashin girkin ta har wata yar rama yy. Sai da ta kwana biyu sannan aka maida ta gidanta. Suka qara yi mata nasiha sannan suka wuce.................... ✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟 Written by the πŸ’…πŸŒŸβœ¨DIVASπŸ’…πŸŒŸβœ¨ Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia. [2/7, 3:49 PM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’2⃣1⃣ Bayan tayi wanka, ta shiga kitchen dayake time din dinner ne kawai sai ta dafa chicken and peppers spaghetti ♨. Sannan ta hada ginger drink mai sanyi. Ta shiga bedroom tayi wanka sannan tayi sallah. Shi kuwa yana dawowa ya nufi bedroom dinsa yayi wanka ya gama shiryawa cikin pyjamas yafito ya shiga kitchen zai hada coffee kawai kamar ance yakalli dining aikuwa bai san lokacin da wani farin ciki ya cika shiba Wani qayataccen murmushi πŸ˜ƒπŸ˜€ya saki yy hanyar dining din ya zauna ya fara buda food flacks wani qamshi ne ya masa sallama. Nan take yai hamdala ya fara nadar abincin son ransa, saida ya gama sannan ya qara gode ma Allah. Yy missing din delicious food dinnan. Ranar ya kwana cikin farin ciki. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Safiya nayi ta tashi ta shiga kitchen ta hada Egg Caldereta sannan ta kunna coffee maker sai da yy sannan ta sa a flacks ta jera mishi don ta lura yana son coffee. Tana tsakar gara dining din ya fito tai saurin duqawa ta gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa ya wuce ya hau dining table ya fara niyar cin abinci. Ita kuwa daki ta wuce tana tunanin oh koma yace mata ya jiki... 🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨ Watan su biyu da aure zamansu kadaran kadahan yanzu bai mata wannan fadan sosai sai dai abinda baa rasa ba. Wata ranar Tuesday ya tafi wurin aiki ita kuma ta fito ta shiga kitchen saboda tana son ta gama da wuri. Ta daura girkin ta fito ta zauna parlour kafin ruwan ya tafasa. Dogon riga(english wears) ne a jikinta irin mai shape dinnan duk tabi jikinta ta lafe bust dinta dake cike yy gwanin ban shaawa sai hips dinta sun yi das cikin rigar. Shi kuma boss din dai2 time din ya dawo domin daukar wasu document din da ya manta. Kai tsaye ya shigo gidan zai nufi bedroom dinsa turus yy don ganin wata tsaleliyar yarinya zaune bisa kujera ta jingina jikinta alamar hutawa take ga kanta ba dan kwali gashinta har bisa cinyar ta

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});