Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Zaheedah Book 1 Complete Hausa Novel 1,228 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ο»Ώ[5/6, 7:36 PM] Aysha Mazoji: [4/6, 8:38 PM] Aysha Mazoji: [1/11, 11:55 AM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’ Alhaji Mansur ne zaune shi da matarsa Hajiya Mariya suna tattauna tattauna maganar dansu da suke so suma aure tunda yaqi fiddo matar da yake so,su zasu zaba masa. Hajiya Mariya wadda aka fi sani da mamy ta nisa tace dady me zai hana a hada shi da Zaheedah, dady yace nima nayi tunanin haka amma kinsan yaran namu mugu ne kada ya je yai ta cutar mareniyar Allah Mamy tace in Allah ya yarda ba zai cuce ta ba ita ce daidai shi kaga gata da haquri ga tarbiya yace to haka zaai, yanzu bari muje wurin Goggon muji ta bakinta. Written by :Aysha,NafeesahMazoji&Ameera jibia [1/11, 1:58 PM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’2⃣ Goggo na zaune Zaheeda na mata tausa sukaji sallamar mamy ta kira tace zaheeda ashe kina nan tace eh mamy nazo wurin Goggo ne tace to maza dadyn ku nanan waje kice ya shigo sai ki wuce cikin gida tace toh tana fita dady ya shigo ya gaida Goggo ta amsa tana Sa masu albarka dan ita abinda suka mata sai Allah biyansu bata da abinda zata biya su dashi. Daddy ya gyara zama yace dama Goggo wata alfarma muka zo nema wajenku tai saurin dakatar dashi haba wace alfarma zaka nema wurina kaqi samu kawai ka fadi koma minene in baifi qarfi naba yace dama Adeel nake so abama Zaheedah don girman Allah domin mun duba munga ba wacce ta dace dashi kamar ta kin dai san halinsa kece ma zaki ba wani labarin halinsa tunda ke kk raine sa tun yana qarami har kawo wa yanzu. Written by:Aysha,Nafeesah Mazoji&Ameera jibia [1/11, 9:10 PM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’3⃣ Goggo ta nisa tace to alhmdllh ba abunda zaku nema wurina na hana ku indai ina da iko akan shi dan haka na bama Adeel Zaheeda har abada amma kun san marainiya ce zan kira dangin mahaifanta in gaya masu. Daddy yayi murmushin jin dadi yace Goggo kin gama mana kome ubangiji Allah ya biya ya saka maki da mafificin alkhairi. Goggo tace ba kome Allah ya basu zaman lfy. Mamy tace ameen amma Goggo ai kamata yayi aje wurin dangin mahaifinta a nemi auran ko? Goggo tace wai da basai an wani jeba dana gaya musu shikenan, daddy ya ce ah ah Goggo ki bari kawai ai mata yadda ake ma ko wace diya Goggo tace to shikenan haka din ma yayi. ************ Written by : Aysha,Nafeesah&Ameera jibia [1/11, 10:19 PM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’4⃣ Anje an nemawa Adeel auran Zaheedah wurin dangin mahaifinta an kuma basa an saka ranar aure wata daya kacal aka saka duk wannan bidirin da ake bada sanin wayanda Ake ma shirin be. Ana ta shirye2n auransu daddy yace kada su damu kansu shi zai mata komi tunda dama yarsa ce shi keda alhakin yi mata komi. Ita kuwa Zaheedah sai dai Goggo tai ta bata kayan mata tana sha azuwan maganin dan kanoma ne haka ma mamy tai tayi mata turarruka da sauran dai tarkacen mata ta dai zuba ma sarautar Allah ido. Zaune suke ita da Deelah suna kallon cartoon mai suna Final Fantasy deelah sai gani tayi Heedah ta zabura tace meye kafin tayi magana taga ya Yayan su shigo tuni suka nutsu rannan hade ya kalli deelah yace ke tashi ki kawo mun lunch dina da sauri ta tashi ta nufi kitchen shi kuma ya juya wurin Heedah wacce duk jikinta ke kyarma saboda tsabar tsoro ya nufe ta gadan2 tako zaro ido dan tasan mugunta zai mata aiko ya take mata yan yatsu bata san lokacin da ta saki wata qara ba aiko sai ga mamy ta fito da sauri tana Heedah lfy? Ganin deel a tsaye yasa tai tsaye turus tace wlh Adeel ka fita daga harkar yarinyar nan shin wai bana hanaka taba yarinyarnan ba yanzu jibi yanda kasa ta kuka kai jamaa wlh kaji tsoran Allah Adeel yace mamy ban fa mata komi ba ki tambayeta ai gata nan mamy tace kamaida ni sakara kenan hakanan za tayi qara wlh kabi sannu kada alhakinta ya Kama ka taja hannun Heedah suka yi dakin ta.yabi bayan heedah da harara. Deelah dake tsaye tace yaya ga abincin bisa daini a fusa ce yace will you shut up and get out of my side ai da gudu ta shige daki ta mai da πŸšͺta rufe. ***************** Written by:Aysha,Nafeesah mazoji&Ameera jibia [1/11, 11:26 PM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’5⃣ 🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟 ASALIN SU Alhaji Mansur shi daya Allah yaba ma iyayansa yayi karatunsa har zuwa degree dinsa akan business ne sannan Allah ya hada shi da matarsa Hajiya Mariya ya aure ta. yara hudu Allah ya basu Adeel ne na farko sai Adeelah sai yan biyu Aaidah da kuma Aaheel. Sun tashi cikin tarbiya sosai dan iyayensu akwai ibada . Aadeel yarone matashi dan kimanin shkaru 28 yarone mai ji da tashen kudi da kuma kyau,yayi karatunsa a Oxford university inda ya karanci mechanical engineering yanzu haka shine manager a company dady dake nan kaduna. Adeel handsome guy ne irin masu kwarjinin nanne, yana da tsawo da kuma fadi mai kyau kamar ingarman zaki πŸ† qirjinsa faffada bla-bla-bla u all know d rest WHILE ZAHEEDA wadda suke kira da heeda diya ce daya tilo mahaifanta suka haifa Goggo kuma grandma πŸ‘΅ dinta ce wadda ta haifi babanta kuma suma mahaifanta cousins ne suka yi aure suka haife mahaifanta Allah ya masu rasuwa tun tana shekara uku sanadiyyar gobarar da suka tafka lokacin Zaheedah na hutu wurin Goggo, tundaga tym din riqonta ya koma wurin Goggo koma ince wurin mamy don daddy ya maido Goggo gidansa a lokacin, Zaheedah yarinya ce kyakkyawar gaske fara ce amma farin mai dan duhu wanda turawa ke cema tan Color bata da qiba sannan kuma ba siririya bace she is just curvy in the right places bata da tsawo kuma ba gajeriya bace matsakaiciya ce de in fact fuskarta heart shape ce tana dauke da matsakaitan idanuwa wanda in ta were su akanka sai ka tsargu tana da poppy πŸ‘„lips πŸ’‹ wanda suke jajir dasu, tana da gashi mai tsawo da kuma kyau tana da natsuwa sosai gata da sanyin Hali. A rayuwarta ba abinda take tsoro irin yayah Aadeel sai kuma kace zaka taba lafiyar jikinta ahalin yanzu tana da 16 years ta gama secondary school 🏫 dinta, kuma deelah ta bata shekara daya da rabi. Wannan kenan. 🌟✨🌟✨🌟✨🌟✨🌟 Written by:Aysha,Nafeesah mazoji&Ameera jibia [1/16, 8:02 AM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’6⃣ Zaune take ita kadai a cikin garden din gidan ta lumshe idonta tana shaqar daddadan iskan dake kadawa fuskanta Tana dauke da murmushi, lokaci daya yanayinta ya canja wani irin tsoro ya shigeta qirjinta ya hau bugawa kaman zuciyan ta zata fito duk sanadin qamshin turaren yaya Adeel data ji a firgice ta bude idonta suka yi 4 eyes kuwa idonta ta fiddo sosai πŸ‘€ tayi wani irin zillo tana yayah don Allah kayi haquri kallonta kawai yake yi fuskar nan ba alamun imani a cikin ta yai murmushin mugunta yace ai ke komi aka miki ki kware baki ba dandai mamy taji tazo taitai mun fada ba to yau gani gaki ba mamy ba kowa sai kuma yaya😑. Yace yau sai yadda

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});