Chapter 26
Chapter 26
kafin ta je ta taimaka ma Yah Adeel ta masa breakfast. Rigarta taga ta taso, ta shafa wani abu taji mai dan tauri, da sauri ta bude rigarta dan ganin menene. Wani razanannen ihu ta saka sanadiyar abunda ta gani .......................................... Written by the π πβ¨DIVASππ Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia. (4 any comments or correction )π 07032266308 [4/24, 11:59 PM] Aysha Mazoji: ππZAHEEDAHππ7β£3β£ Adeel na kitchen yaji Heedah ta saki wani wawan ihu. Da gudu Adeel ya nufi dakin don yasan wannan ihun bana lafiya bane. A hargitse ya shiga dakin ganin Heedah na tsalle tana yarfe hannu tana kakkabe cikinta. Da sauri ya qarasa ya riqe ta yana baby girl me ya faru, what's going on, ya aka yi. Da qarfi ya riqe ta don taqi daina tsallen kuma taqi daina kukan. Da kyar ya samu ya zaunar da ita yana qara tambayar ta. Cikin kuka tace Yah wani abu ya fito man a ciki. Yace baby girl wane abu buda na gani. Rigar ta yaye masa kallon cikinta yy tare da zare ido don ganin yadda ya koma. Innalillah ya fada ai kuwa ta qara rudewa ta kuwa qara saka wani ihun. Da sauri ya tashi ya dauko mata hijab dinta ya saka mata. Daukar ta yy don yaga kamar ba ta tafiya sosai. Cikin mota ya saka ta, wani irin fisgar mota yake yi ita kuwa Heedah sai qwala kuka take kamar an aiko mata da saqon mutuwa. Shi kuwa Adeel sai tsula gudu yake kamar zai tashi sama. Cikin 30 minutes suka isa gida, sunayin parking ta balle murfin mota ta fito shima a sakwane ya fito ko marfin motar bai rufe ba. Gida suka shiga Heedah sai qwala ihu take. Ihun Heedah ne ya fito da Mamy da Goggo wanda suke zaune suna fira don daddy bai dade da fita office ba. Mamy ce da sauri ta kama Heedah tana tambayar ta wa ya rasu, me ya faru. Kukanta kawai take yi. Mamy ta juya wurin Adeel tace kai me ya faru ne, ka sanar damu mana kunzo duk kun tada mana hankali. Cikin in ina Adeel yace Mamy wani abu ne ya fito mata a ciki. Mamy tace Subhanallah me ya fito mata kuma. Adeel ya matso kusa da Heedah wadda ke kuka har da su majina. Hijab din jikinta ya yaye tare da dage rigarta yace Mamy kinga jiya lfy qlw muka kwanta yau muna tashi muka ga ya zama haka. Ajiyar zuciya Mamy da Goggo suka sauke a tare. Murmushi Goggo tayi tace yaro yaro ne dai. Mamy tsoki tayi tace shine duk kuka bi kuka rude haka. Ke Heedah yi ma mutane shiru. Ji yanda kk kuka har da su majina kamar wata qaramar yarinya. Sai da Heedah tayi shiru sannan su Mamy suka zauna, Mamy ta kalli Adeel tace to soldier sai ka samu halin zama ko? Kusa da Heedah ya zauna yana kallon yadda su Mamy basu dauki maganar da mahimmamci ba. Mamy tace Goggo yi musu bayanin ko mi ke faruwa. Goggo ta nisa tace wane bayani zan musu kawai a fadi musu kai tsaye. Kai Adeelu matarka ciki ne da ita. Cikin mamaki Adeel yace amma Wlh Goggo jiya bata da ciki yau fa ne ya fito. Kuma yau dinma da safen nan. Heedah ta ce Wlh Mamy jiya banda ciki yau ne ya fito. Mamy tace har yanzu dai baku girma ba, ba kamar kai Adeel. Yanzu duk symptoms din mai ciki kai baka ganewa girgiza kai yy tace to Heedah dai ciki ne da ita kuma tun ba yau ba muka sani. Abunda dai ke ban mamaki yadda yy girma haka don a lissafin mu yanzu cikin watansa uku amma bamusani ba ko zai kai hudu. Wannan sai anje asibiti sai a auna a gani. Adeel jin Heedah na dauke da babyn sa yasa sai washe baki yake dadi har a amadun kunnen sa. Heedah ce dai tayi shiru don Ita kunya ma taji da aka ce tana da ciki. Sai bayan zuhur prayer sannan suka wuce gida da sharadin zasu je asibiti a duba lafiyarta Zo kuga tattali wurin Adeel bayan sun koma gida kamar zai maida ta ciki haka yake ji baya barinta tayi komai sai in ta matsa sosai sannan yake barinta shima ba mai wahala ba. Sunje hospital kuma an tabbatar musu da twins ne cikinta..... ................................. Written by the π πβ¨DIVASππ Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia. (4 any comments or correction )π 07032266308 [5/6, 7:36 PM] Aysha Mazoji: [4/29, 7:05 PM] Aysha Mazoji: ππZAHEEDAHππ7β£4β£ Authors note :--Don Allah ayi haquri da rashin posting da banyi ba for so long it's because I'm going through some phase of life so wish me luck please and I also need your prayers, and finally I love you all Heedah s lovers ππππππ Bayan two weeks suka koma hospital don suna da appointment da Doc. Da yake asibitin turawa ne wata Doc ce mai mutunci zasu ringa gani har ta haihu. Sunan Doctor n Isabella so, suna kiranta da miss Isabella. Sai da suka gaisa sannan taba ma Heedah hospital gown ta saka zasu yi mata awon jini sannan zaa dauki weight dinta sai da aka gama sannan tace ma Heedah ta kwanta bisa gado zaa mata ultrasound. Wani dan gel kyakkyawar baturiyar ta dauko tare da yaye rigar Heedah, kallon Heedah tayi tare da h Yb Ybh murmushi tace this may be cold sannan ta zuba bisa cikin Heedah sannan ta dauko ta fara scanning din nan take computer n ya fara shuuuuu sannan sai ga faint heart beat har guda biyu. Murmushi Doc tayi sannan ta kalli Adeel dake zaune bisa kujera ya riqe hannun Heedah gam. Tace here are your babies, Adeel ya qara leqa computer yaga wani dishi2 yace I can't see anything here. Miss Isabella tace here let me help you out ta fada tana nuna computer n tace right here is baby A and here is baby B, and they seem very healthy. Wani murmushi Adeel ya saki saki tare da cewa Alhmdllh. Doc tace do you want to know the sex of the babies da sauri Adeel yace no, no we want it to be a surprise. Doc ta musu printing din pics din ultrasound din sannan suka mata godiyya tace next appointment in one month. Kai tsaye gidan su Mamy suka wuce don tace tana son ganin Mamy. Mamy tana ta murnan ganin Heedah sai nan nan take da ita. Adeel yace Mamy daga hospital fa muke, Mamy tace to hope komai normal ko? Yace eh ba wata matsala anyi ultrasound kuma ance yan biyu ne. Mamy tace Kai Alhmdllh Allah abun godiya, tace wata nawa ne yace five months ne. A nan suka yi yini sannan suka koma gidansu. β¨πβ¨πβ¨πβ¨πβ¨πβ¨πβ¨π Bayan two months Heedah ce zaune tsakar parlour n su ta wani baje ga cikinta da yayi wani irin girma wanda in aka ce maka zata iya haihuwa da gudu zaka yadda. Zaune take tana shan rake don tunda cikinta ya shiga wata shida take shan rake, rake baya isarta wani lokacin har bakinta da haqoranta ciwo suke mata amma haka nan take daurewa ta sha don ji take in bata sha ba to zaa samu matsala. Don
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31