Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Zaheedah Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ne bakya sallah? Cikin in ina tace yah deel bansan asuba tayi bane yace yanzu ai kin sani yayi wucewarsa daki. Ta dauki tsawon lokaci a tsaye don tana jin fitsari gaya bata san inda zata nufa ba ai kuwa sai gashi ya fito yace au baki tafi sallar ba kenan tace yah bansan toilet din ba . Tsaya wa yai kallonta sannan yace do you know that you are very stupid and I'm not going to tolerate your stupidity. Of all the rooms in this house yet you don't know how to get to a toilet. kwafa yy yace kafin na fito daga kitchen ki bace min daga sight yayi wucewarsa zai hada coffee. Ai kuwa ta nufi wata qofa ta shiga nan take ta sauke ajiyar zuciya da taga bedroom ne, ta shiga toilet tayo alwala tazo ta bude gyalenta tayi sallarta bisa carpet sai data gama addu'o'in ta sannan ta Kwanta bisa bisa carpet din ai kuwa sai bacci soboda ta gaji sosai....... Written by the πŸ’…πŸŒŸβœ¨DIVASβœ¨πŸŒŸπŸ’… Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira jibia [1/31, 9:17 PM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’1⃣6⃣ Bacci tayi sosai don sai wurin 10 ta farka ta tashi ta shiga toilet taga sabon toothbrush tayi sannan tayi wanka ta fito daure da towel ta rasa to ina zata samu kayan da zata sa kawai sai ta maida kayanta tana tsakar zuge zip dinta kawai sai ganin mutun tayi ya shigo tai saurin dauko veil dinta ta rufe jikinta. Kwafa yy sannan ya wurga mata phone πŸ“± kawai yai tafiyarsa yana tunanin she's really a big villager daga shigarsa ta wani rufe jiki kuma wai da kayafa a jikinta. Kwaila kawai da ita. Ita kuwa tayi tsaye da phone a hannu ta rasa me zatayi dashi can taji an kira ta duba taga number n Mamy ai kuwa taji wani sanyi ta daga ta gaisheta Mamy tace ya kadaici tace Mamy nayi missing dinku wlh tace ai zaki saba tace yawwa Mamy kayana fa tace ki duba cikin closet zaki gansu tace wane room tace ko wane room akwai kayanki so ki duba tace na aiko muku da breakfast Don Allah kici nasanki da rashin cin abin ci. Tace zanci Mamy yaushe zaku zo tace zamu inshaa Allah tace Mamy deelah fa tace kufa bakwa rabuwa da shirme daga kwana daya sai kuma ta kama zuwa. Kin dai san halin yayan naku so you have to be extremely careful with him tace to Mamy Nah zan kiyaye. To Allah ya yi muku albarka. Suna gama waya ta bude closet sai kuwa taga kaya daidai ita ta dauka ta saka sannan ta dauko zunbulelen hijabinta ta saka ta fita palourn tayi hanyar da taga kamar dining room ai kuwa taga dainin cike da breakfast ta zauna tadan ci sannan ta tashi ta wuce dakin da ta kwana tayi zauniyarta ta kunna plasma din da ta gani ta gano CN (cartoon network) taci gaba da kallo don tana son cartoon. Shi kuwa ya cika yayi dam kamar zai fashe tsabar fushi don yarinyar ta bata masa rai sosai 😑.Tashi yayi ya nufi room din da take yana tunanin yau sai ta sani kuwa.............. Shin me ta masa? Guess Written by theπŸ’… 🌟✨DIVASβœ¨πŸŒŸπŸ’… Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia. [2/2, 7:24 PM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’1⃣7⃣ Kallon ta take Hankali kwance tun kafin ya Shigo qamshin perfume dinsa yai mata sallama ta dago da sauri cikin bugun zuciya ai kuwa sai gashi kamar wani zaki ya wurga mata harara yace ke wai wace irin wawiya ce ke ne? Cikin rawar murya tace yah me nayi yace kina tambayana me kk yi ba tun dazu na kawo miki phone dina ba me ya hana ki meda mun da kk gama. Tace yayah I'm sorry na manta. Ya kalli idanunta duk sun cuko da hawaye Yace ke kuma baki da aikin yi sai ba mutane haquri komi you are sorry. Nidai kinsan ba wasa nake da keba so kibini a hankali yayi kwafa ya juya yayi ficewarsa daga dakin. Kallon da batai ba kenan ta ci gaba da rera kuka ita batasan me yasa yah Deel ya tsane ta ba ita a tarihin rayuwarta kaf bazata iya cewa ga abin da ta taba yi masa ba hakanan dai ya tsane ta. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨. Kwanci tashi anyi sai da aka yi sati biyu da bikinsu sannan Mamy tace ta fara girki don kullum daga gida ake kawo musu tsakaninta da boss din kuwa ba kome sai hantara ba wata maganar arziqi dake hadasu shiyasa ma take wuni a daki in ta fito to saidai in abinci aka kawo. Wani lokacin haka nan zai shigo har bedroom din yai tai mata fada na ba gaira ba dalili. Shiga kitchen tai ta hada delicious lunch Fried rice with Ham & Hotdog (some may misunderstand Hotdog for a recipe made with dogs 🐢, so to avoid any misunderstanding "Ba da kare ake yi ba "). Ta hada juice dinta na watermelon πŸ‰ mai sanyi duk ta jera bisa dining table. Ta wuce tayi wanka tayi kwanciyar ta. Gogan naku ya shigo gida dama ya kwaso yunwarsa ya zauna bisa dining yana bude abinci yaji wani qamshi ya daki hancin sa tun daga kan yadda akayi garnishing abin cin yasan yau akwai banbanci yace to yau ko a restaurant aka siyo mana abincin . Yai serving din kansa ya kai lomar farko sai da kunnensa yai motsi dan dadi nan yaci gaba da nada shi kansa sai da yayi mamakin abincin da yaci don ba kadan bane. Ya dauko juice din watermelon Wanda yaji pic milk ga sanyi kai shidai alhmdllh in yaje gida sai ya tambayi Mamy ina aka sawo musu wannan abincin dan wannan tabbas ba daga gida aka yi shiba duk da Mamy ba daga baya ba wurin girki amma wannan saura kadan kunnensa πŸ‘‚ ya katse. (so, what do you think?) Written by the πŸ’…πŸŒŸβœ¨DIVASβœ¨πŸŒŸπŸ’… Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia [2/4, 10:52 AM] Aysha Mazoji: πŸ’πŸ’ZAHEEDAHπŸ’πŸ’1⃣8⃣ Sai datayi sallar magriba sannan ta shiga kitchen don tasan wuraren 8 yake dawowa ba abu mai nauyi tayi ba kawai Beef Macaroni soup sai desert din kuma tai Beef Tacos sannan ta hada zobonta wanda yaji citta ta jera bisa dining sannan ta debi nata taci ta je ta watsa ruwa tai sallar isha'i tayi shafa'i da wutiri sannan tai kwanciyarta. Shi kuwa yana can yana nadar girki shidai tunda yake bai taba cin girkin da ya masa dadi irin wannan ya ma mance ya tambayi Mamy ina aka siyo musu don in anbar kawo musu abinci ya ringa zuwa yana ci don bazai iya cin girkin yarinyar nan (dariya muka yi mukace tun yaushe kuma πŸ˜‰) ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Haka suka kasan ce kullun tana masa girki mai rai da lfy ba tare da yasan ita keyi ba kullun yana nadar girki har wani tunbi2 ya fara baida matsalar abinci. Sunyi wurin wata daya da aure ranar wata Friday tayi mai breakfast yaci ya fita tun tana lunch taji marar ta na mata wani iri tai lissafi taga maybe yau period dinta zaizo aiko indai haka ne ta shiga tara bama uku ba don wani irin wahallalen ciwon mara take ga ba Mamy ita yau ya zatai a gaggauce ta gama hada lunch

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});