Chapter 21
Chapter 21
hada mun ruwan. Tace to tare da shigewa bathroom din shi kuwa Heedah ya dauka a hankali ya shinfide ta bisa sofa don ya samu ta dan yi bacci. Bedspread din ya yaye ya nufi bathroom din wani daki ya saka a washing machine ya wanke ya kuma sa a dryer sannan ya koma dakin. Koda ya koma har Deelah ta gama hada ruwan yace yawwa to gyara dakin bari na mata wankan da sauri Deelah tace Yah kaine zaka mata wankan. Harara ya wurga mata tare da cewa to in ba ni zan mata ke zaki mata. Dallah kiyi aikin da na saki malama, to tace. A hankali ya dauki Heedah wacce take ta ajiyar zuciya cikin bacci ya nufi bathroom da ita. A hankali ya dan shafa mata fuska tare da dan hura mata iska a kunne bude idonta ta soma yi ,ta bude fuskanta tare da kallonsa nan danan ta kwabe fuska zata fara kk yace shishhh baby girl wanka zan miki kinga har anyi sallar asuba baki yi ba ko? Bata fuska tayi tace to duk ba kai bane.... Dora yatsansa yy a kan lips dinta tare da cewa but I said I'm sorry, I will not repeat it again. I promise you. Cikin ruwan zafin ya saka ta ai kuwa qara ta saki tare da tashi tsaye tana ta yarfe hannu tare da hawaye. Tace nidai Yah banso akwai zafi sosai yace sorry zaki ji dadin jikin ki ne kinji baby girl. A hankali ya sa ta cikin ruwan zafin yana ta rarrashi. Ita kuwa ta wani riqe sa sai kk take masa na shagwaba . Sai da yaji ruwan ya huce before ya yi mata wanka yace to kiyi wankan sai na maida ki. Tace nidai ka tafi bana so. Dan murmushi yy yace are you sure? A shagwabe tace nidai ka tafi. Yace to zan tafi amma in kin gama ki kirani fa, dan hararensa tayi tace ni dai ka tafi. Fita yy zuwa dakin don yaga ko Deelah ta gama aikin. Zaune ya isko ta tana waya, da sauri yace ki tashi ki hada breakfast mana. Aje wayan tayi tare da cewa Yah Mamy tace kada nayi break zata aiko da shi. OK ya fada tare da wucewa parlour ya shiga kitchen ya hado coffee ita kuma Heedah ya hado mata tea ya koma bedroom din lokacin ta fito daga bathroom tana tafiya a hankali tana dan cije baki. Da sauri ya aje kayan dake hannunsa ya qarasa ya ruqo ta yana sannu baby girl sannu kinji. Zaunar da ita yy bisa bed sannan ya shimfida mata sallaya ya saka mata hijab yace baby girl tashi kiyi sallan sai kisha tea kinji. Deelah ce ta qaraso Inda suke tare da cewa Yah wai me ya same ta ne naga bata iya tfy sosai. Harara ya sakar mata kafin yace wai ke me yasa kk cika tambayar tsiya ne iye. Tace to Yah naga bata iya tafiya ne da kyau. Oh God ya fada tare da cewa ke ki wuce ki tafi parlour ki zauna kafin na mangareki a wurin. Tura baki tayi kafin ta wuce tana gunguni. .............................................. Written by the π πβ¨DIVASππ Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia. (4 any comments or correction )π 07032266308 [4/6, 4:21 PM] Aysha Mazoji: ππZAHEEDAHππ6β£2β£ Da kyar Heedah tayi sallah sannan ya bata tea din tasha yace Mamy tace zata aiko da breakfast yanzu. Da sauri ta kalle sa tare da cewa Mamy tasan banda lfy ne? Yace eh mana menene? Tace to wane irin rashin lfy kace mata Ina yi? Yace nidai kawai nace baki lfy tace amma dai bata gane ba ko yace nidai ban sani ba amma da kyar inta gane. Yah mu tafi parlour n mana yace ok but I thought ko zakiyi bacci ne tace ni bana jin bacci yanzu inason magana da Deelah ne. Okay? Yace but me zaki fada mata ne. Kallonsa tayi tace labari fa kawai zamuyi fa. yace ok let's go. A hankali suke tfy don ruqota yy Deelah na ganin su tayi saurin tashi ta qaraso kusa da Heedah ta riqe ta tace sannu sister nah wannan ciwo haka ya jikin tace da sauqi Alhmdllh. Tace to Allah ya baki lfy sister nah. Zama sukayi suka dan fara fira har aka kawo musu breakfast shima da kyar ya samu taci da yawa sannan ya qyale ta shima ya ci. Yinin ranar haka suka yini jinyar Heedah sai dare Mamy tayo waya wai Deelah bazata dawo bane yace Mamy wai da abarta ta Kwana, Mamy tace kai ni bana son shirme yanzu na kira Abbas yazo zai kawo muku dinner to sai ya taho min da ita. Tohm yace tare da godiya. Baayi minti ashirin ba sai ga Abbas da basket a hannu. Deelah ta amsa ta ajiye a coffee table. Zama yy tare da cewa wash. Heedah ta gaishe sa ya amsa tare da cewa amarya amarya bakya laifi ko? yake tambayar ta ita dai murmushi kawai ta ke masa yace yau kun wahalar mun da mata ko? Tun asuba sai yanzu. Adeel yace eh din anje an wahalar da ita din kai abinda zakayi. Abbas yy dariya yace ni yau bazan yi dakai ba tunda nasan duk yau kana cikin shauqi ne so, I don't have your time bari in ka ware zamu gauraya. Tsoki Adeel yy yace naji nima likewise I don't have any time of yours. Miqewa yy yace malamai sai anjima ko Abbas ya fashe da dariya tare da cewa friend yau harda korar mu lallal zamu gauraya ne zaka sani. Adeel yace eh din nidai ku tafi Sai Allah ya kaimu. Dan kwafa yy tare da cewa wlh nima zan rama ne very soon. Yace ai sai dai ka rame kuwa. Don baza kaga qafarmu gidan ka ba. Abbas ya qara dariya yace duk ba laifin ka bane nasan matsalarka wlh. Dan tura sa Adeel yy tare da cewa a gayas. Deelah ta ma Heedah sai safe tare da fatan samun lfy. Suka rabu cikin kewar juna. Shi kuwa Adeel har bakin motar ya raka su sannan ya dawo cikin gida. Sai da ya tabbatar ta ci abinci kafin ya kaita bathroom tayi wanka saboda yasan dole tayi kafin ta kwanta. Fita yy domin ya hada coffee ita kuwa da ta gama wankan ta ta saka rigar bacci ta haye gado tuni bacci yy gaba da ita don tana da buqatar baccin dama. Shi kuwa Adeel yana gama wa ya nufi bathroom yy wanka shima, ya saka pyjamas dinsa ya haye gadon tare da jawo ta. Cikin bacci taji ana lalubenta da sauri ta bude idonta tare da fara yarfar da hannu ga hawaye har sun wanke mata fuska. Tace but Yah you promise me, katse ta yy ta hanyar cewa hey hey hey baby girl ba wani abu zan miki ba fa kwantar da hankalinki I won't break my promise zan haqura har sai randa kk yarda kinji baby girl yi kwanciyar ki.bisa qirjinsa ya kwantar da ita. A hankali yake dan jijjigata har ta koma baccin before masu addua shima ya kwanta ................................... Authors note :- I'm very sorry for the inconvenience caused by me for not posting in like three
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31