Chapter 28
Chapter 28
ma Mamy kira da gudu Mamy ta shigo dakin ganin Heedah a zaune qasa tana ta zufa yasa ta saurin kamo ta suka tashi, suna zuwa parlour wani ciwon ya taso ta riqe Mamy kam tana Addua. Bisa kujera Mamy ta aje ta sannan ta ruga kiran Goggo. A sakwane suka shigo tare suka kamata suka fita already driver is ready kawai mota suka shiga sai asibiti. Da yake asibitin turawa ne daki daya aka ware ma Heedah sannan aka kira Doc Isabella. Tana zuwa tace ina Adeel sai lokacin Mamy ta tuna basu gaya ma kowa ba hakanan suka taho. Waya ta buga ma Adeel tace yazo suna hospital. Ai kuwa cikin fifteen minutes sai gashi ya iso a hargitse ................................... Written by the π πβ¨DIVASππ Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia. (4 any comments or correction )π 07032266308 [5/6, 7:36 PM] Aysha Mazoji: [5/4, 7:21 PM] Aysha Mazoji: [5/4, 7:00 PM] Aysha Mazoji: ππZAHEEDAHππ7β£6β£ Yana isowa kai tsaye dakin ya shiga da sauri ya qarasa wurin Heedah wacce ke kwance an manna mata wata computer sai zufa take yi ga nurse guda biyu ga kuma Doc Isabella. Murmushi Doc tayi ma Adeel tace are you ready to be a Daddy? Yeah yeah I'm, but how is she doing. She is doing great, she is almost six centimeters dilated. Salatin Heedah ya katse musu zancen da suke yi, hannun Adeel ta Kama ta riqe har sai da yy yar qara. Sai da ciwon ya lafa sannan ta ringa meda nunfashi. Qara jawo hannun sa tayi tace Yah bazan iya ba akwai ciwo sosai pls help me. Shi ma hawayen ya fara yana sorry baby girl duk ni na jamaki kiyi haquri Don Allah. Wani ciwon ya qara tasowa tuni ya rungumo ta yana shafa mata baya har ciwon ya lafa. Doc Isabella ta qara duba ta taga har takai eleven centimeter dilated. Murmushi tayi tace Heedah you are doing just great, you will feel an urge to push now don't hold it back, just do what you feel is natural okay? Da sauri Heedah ta kada kai. Doc tace Adeel you have to hold and support her this is the birth part okay? Da sauri ya kada kai ya koma bayan Heedah ya kwantar da bayan ta bisa qirjinsa. Aikuwa sai ga ciwo tare da nishi sun taho tare tunda Heedah take bata taba jin irin wannan balain ba. Da ciwon ya kwanta kuka ta saka ita wlh bazata iya ba, Adeel shi Ke lallashin ta wanda shima in ciwon ya taso kuka yake sakawa har sai ya lafa. Haka suka yi tayi har aka samu kan daya ya fara fitowa amma time din ta riga ta galabaita sosai. Computer n ne ya fara wani dan qara kadan. Doc ta kalli Heedah tace you have to be strong okay Adeel tell her pls, she should not give up. Da sauri Adeel ya kalli Heedah wacce idonta ya fara juye wa cikin kuka yace baby kada ki gaji pls kiyi haquri ki daure you have to do this for me and for our babies Pls. Wani nishi ta qara yi da dukkan qarfinta ta riqe hannun sa kuwa har sai da hannun yayi qara. Doc tace Adeel the baby is coming you have to witness the birth of your first child. Come here, da sauri Adeel yy wurin aikuwa yana leqawa ya sanqare kafin ya zube qasa sumamme.............................. Ruwa aka zuba ma Adeel kafin ya farfado aikuwa da sauri ya koma wurin kan Heedah dake nishi aikuwa kukan jariri ya cika dakin Doc ta kalle sa tace you have to cut the umbilical cord Daddy and it's a boy wani murmushi yy kafin ya ansa scissors yayi cutting umbilical cord din sannan ya karbe yaron daga hannun nurse din ya dawo wurin Heedah dake meda nunfashi. Baby girl kalla boy din mu Masha Allah kallarsa. Nurse ta matso tace ya bata babyn zata masa wanka No ya fada da sauri nurse din tace look the other baby is coming ........... Da sauri ya miqa mata shi ya koma wurin Heedah wacce sabon ciwo ya taso mata. Cikin five minutes baby ya qara fadowa wannan karan ma baby boy ne kuma Adeel ne ya yenke cibiya. Heedah shiru tayi kamar tana bacci don ba qaramin galabaita tayi ba. An wanke jarirai duk ansa musu kayan da hospital din ke providing. Matsala daya har yanzu afterbirth (uwa ) bata fito ba. Doc hankalin ta ya fara tashi, wurin computer n da aka sa ma Heedah ta nufa tana dan dubawa. Oh my goodness ta fada da sauri Adeel ya kalle ta yace what what's wrong. Juyowa tayi tana kallon Heedah tace there is another baby ........................ Written by the π πβ¨DIVASππ Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia. (4 any comments or correction )π 07032266308 [5/4, 9:24 PM] Aysha Mazoji: ππZAHEEDAHππ7β£7β£ Da sauri Adeel ya kalli Heedah wacce idonta ya raina fata. Cikin ten minutes Heedah ta qara sunkuto wani baby n. Ba abunda Adeel ke fada sai ALHAMDULILLAHILLADHI BI NI'IMATIHI TATIMMUSSALIHAT. (All praise is for Allah by whose favour good work are accomplished) Wannan karon baby girl Heedah ta haifa Adeel hada su kuka da yaga triplets Heedah ta haifa. An gyara yaran gwanin ban shaawa an saka ma boys din blue soft cotton unisex baby girl din kuma pink aka saka mata da yan hulunan su kamar ka sace su ka gudu. Sai da aka gama gyara Heedah sannan aka nufi dakin Hutu da ita don ko babies din bata gani ba tunda ta haifa last babyn ta take bacci. Adeel ya ma mance da zancen su Mamy sai da suka fito yana dauke da yara biyu sannan yagan su da sauri suka taso hada su Daddy suna yaya. Adeel yace Daddy ga yaran da sauri Mamy ta amsa guda Goggo ma ta amsa guda. Suna ta sam barka, Adeel yace Daddy Heedah yan uku ta haifa fa. Dukkansu suka juyo kallonsa galala. Gudar ya amso daga hannun Doc ya miqa ma Daddy yace ga Daddy's girl nan. Aikuwa duka sai murna Mamy hada su kuka don farin ciki. Dakin da aka kai Heedah nan aka kai babies din aka sa musu gado uku aka kwantar da su sai baccin su sukeyi. Bacci Heedah keyi hankali kwance bata san hidimar da ake yi ba. Lokacin da Heedah ta tashi dukkansu suna dakin sai qara kallon babies din suke yi. Yah Adeel ne ya lura da ta farka. Da sauri Yah Adeel ya qaraso kusa da ita ya na sannu baby girl kin tashi, kallonshi kawai take yi cikin ranta tana tunanin ai dole a mata sannu wannan uwar wahalar da tasha. Mamy tace bari a hada mata tea, Adeel ne ya kama ta ya tayar da ita sannan ta wanke bakin ta cikin wani kwanon silver. Mamy ta miqo mata tea din nan danan ta shanye kuwa. Goggo tace zaheedah baki tambayi abunda kk haifa ba. Shiru Heedah ta mata, Yah Adeel yaje gadon yaran daya bayan daya ya dauko su ya aje gabanta. Ita kuwa Heedah kunya ta hana ta kallon yaran don duk ga su Daddy a wurin. Adeel yace Heedah kinga arziqin da Allah ya bamu Heedah. Kwantawa tayi taqi kallon su ganin haka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31