Chapter 17
Chapter 17
ehm lfy qlw wlh. To naga ai duk sanyin nan kana zufa yace maybe fever ne ke son kama ni. Yace to Allah ya kyauta. Tashi yy yace to ni bari na wuce yace to a sauka lfy Allah ya tsare. Har ya kai bakin qofa kuma yace af na manta munyi magana da Abban Abbas mun yanke nan da two months zaayi bikin kawai ya tafi da matan sa. Allah ya sanya alkhairi ya fada Daddy yace Ameen. Yace to na wuce Allah ya baka lfy in kana buqatar hutu to ka dauka. Yace to inshaa Allah. Wata ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon qasan table din Heedah na zaune ta dora kanta a tight dinsa da alama ma bacci take. A hankali ya dauko ta bisa sofa ya kwantar da ita tare da gyara mata kwanciya. Zama yy yana tunanin Heedah da badan Daddy ya zo ba ai da baisan me zai faru ba. Sai wurin daya na rana sannan ya tada ta suka nufi gida. Sai wani irin kallo yake mata. Suna zuwa gida kitchen ta fada tayi musu abinci mai dan sauqi. Sannan ta je tayi wanka tayi sallah. Sai da suka je cin abinci taga har yanzu yana mata wannan kallon. tace wai Yah lfy naga sai kallo na kk yi. Murmushi yy sannan yace kawai ina mamakin ki ne ina kk koya abunda kk mun dazu. Rufe ido tayi tace wlh ba wanda ya koya mun haka nan nayi. Murmushi ya qara yi tare da rungumo ta yana laluben lips dinta dan kaucewa tayi tace Yah kaci abincin tukunna. Yace na ci ko muci dai. Sai bayan sun gama cin abincin sannan suka dawo parlour. Yace wai ke dazu kina ganin Daddy shine kk yi min bacci wato in ya kama ni ke ba ruwan ki ni na sani. Murmushi tayi tace ni wlh ban ma san nayi baccin ba kun dade kuna magana har na gaji. Yace wai kinga yadda nake zufa kuwa. Har Daddy sai da ya gane bana da gaskiya yace wai lfy nake kuwa. Dariya ta dinga yi masa ai kuwa yace au dariya ma na baki kenan zakiyi mai dalili kuwa yanzunnan. Kama ta yy ya birkita ta ya fara blowing mata butterfly kisses a wuya don yasan she's very ticklish a wurin. Bisa carpet din parlour n suka zube. Ai kuwa dariya ta fara yi tana Yah kayi haquri ka bari cikina zai fashe. yace say the magic word. Ta rasa meye magic word din can tace please stop it. Cak ya tsaya da kisses din yace now that's the magic word. Dora ta yy bisa qirjinsa suna ta sauke nunfashi kamar wayanda suka yi gudu. Sai da suka nutsu sannan tace Yah meye magic word din wai, yace the magic word is "please".................................... Written by the π πβ¨DIVASππ Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia. (4 any comments or correction )π 07032266308 [3/28, 1:41 PM] Aysha Mazoji: ππZAHEEDAHππ5β£6β£ Washe gari gida ya biya ya sauke ta sai da aka ba Goggo amanar ta sannan ya kira Deelah ita ma aka mata warning wai ta kula masa da baby girl dinsa da kyau tace to inshaa Allah zaa kula da ita. Bayan ya wuce dakin Heedah suka shige suka zauna. Deelah tace kinji wai bikina nan da two months ko. Wani irin tsalle Heedah tayi tace ke don Allah wannan wane lucky guy ne haka. Deelah tace ke dallah ana gaya miki ni ban ma san ko yana so naba wlh. Qila ma irin naki zaamun auren hadi. Heedah tace ke baki san auren hadi ba yafi dadi wlh ni ina murna don Allah waye. Ke Yah Abbas ne fa Yah bai gaya miki ba. Maybe ya manta ne. Kai amma nayi murna fa, don Yah Abbas yy fa Allah ya sanya alkhairi. Deelah ta tura baki tace ke fa baki da mutunci ina gaya miki matsala ta kina wani Allah ya sanya alkhairi Tace to tsaya yanzu ai dai ba fasawa zaayi ba ko ai dole nace Allah ya sanya alkhairi. Nan dai tai yayi mata nasiha har ta dan sakko suka yi ta fira. Haka suka ci gaba dayi in zai tafi aiki sai ya sauke ta gida ya wuce koda Mamy ta masa magana me yasa yake kawota yayi mata bayanin komai tace to haka ma yy kyau a hankali zata ware inshaa Allah. Haka sukayi kwana takwas yana kaita gida. Ranar Thursday ya sauke ta gida ya wuce wurin aikinsa. Ciwon mara ta fara tun tana daurewa har ta fara fita hayyacin ta. Deelah ce ta shigo dakin ta same ta a haka ai kuwa da gudu ta qarasa wurin ta tana tambayar ta me ya faru. Maranta take nuna mata da hannu. Da sauri ta tashi ta kira Mamy ko kafin su iso ta suma. Kama ta sukayi suka sa mota suka nufi hospital. Kai tsaye ER aka kaita suna bata taimakon gaggawa. Sai da suka gama aka mata allurar bacci sannan aka kaita wani room. Doc ne yace Hajia ina baban ta yake ne tace yana bisa hanya yanzu zai qaraso kafin ma ta rufe baki sai ga Daddy ya shigo yace to ko zaku dan biyo ni zuwa office dina akwai wani dan bayani da zan muku. Dukkan su suka bishi banda Deelah. Sai da Suka zauna sannan yace a gaskiya yarinyar ku ciwon MP ke damunta kuma chronic one ne so, the best solution dai kuyi mata aure kawai. Dukkansu sakin baki sukayi suna kallonsa kafin daga baya Daddy yace ai tana da aure. Kallon sa Doc yy cikin mamaki yace tana da aure? to amma mijin bai da lfy ko? Don ciwon MP n ta gaskiya na virgin ne. Kallonsa Daddy yy yace to mun gode amma ina Doc faruk don shine Doc n mu sai ya diba mana shi yaga in yana da lfy. Doc yace eh to gaskiya an tura shi yin wani course ne a Canada kuma zai dauki tsawon two months kafin ya dawo. Daddy ya masa godiya yace to inshaa Allah zamu kawo sa sai yaga Doc din. Dakin suka koma cike da jimami Daddy yace bari na kira Abbas muyi magana nasan shi komi kenan zai sani. Yana fita ya kira Abbas yace ya same shi a hospital yanzunnan. Baayi minti goma ba sai gashi ya qaraso, sai da ya gaishe da Daddy sannan suka samu wuri suka zauna. Daddy yace magana nake so muyi akan abokinka yace to Allah ya sa dai lfy. Yace eh to da sauqi dai. Daddy yace ka gaya mun tsakanin ka ga Allah abokinka yana da wata matsala ne Abbas yace wlh Daddy a iya sani na Adeel bai da wata matsala amma ban san wace irin matsala kk nufi ba Daddy nan Daddy ya gaya masa duk abinda ke faruwa................................................ Written by the π πβ¨DIVASππ Aysha,Nafeesah Mazoji &Amira Jibia. (4 any comments or correction )π 07032266308 [4/6, 8:39 PM] Aysha Mazoji: [3/26, 12:14 PM] Aysha Mazoji: ππZAHEEDAHππ5β£3β£ Sai bayan magrib suka rabu yace zai je gida amma gobe zai dawo ya ci girkin amarya tunda yau bata lfy. Suka yi bankwana suna ta raha ya tafi. Washe gari da Adeel zai tafi wurin aiki tare da Heedah ya tafi don
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31