Chapter 9
Chapter 9
ba.” “Ko akwai wani mataki da zaku dauka akan hakan?” “Qwarai kuwa, akwai matakan da zamu dauka sosai kuwa.” “Kamar wadanne irin matakai?” “Farko dai mun qara ninka tsaro a cikin gidan da wajen gidan don ganin hakan bai qara faruwa ba, kuma mun baza ‘yan sandan bincike na fararen kaya da masu kaki don bincike wadanda suka aikata wannan danyen aikin da kuma ita kanta mai laifin, ba don komai ba sai don mu miqasu a yanke musu hukuncin da doka ta tanadarwa masu laifi irin nasu.” Yana gama fadin haka ya wuce ba tare da ya qara sauraron 'yan jaridar ba. wadannan hotunan da zaku gani hotunan jami’an tsaron da harin ya afka kansu ne a kwance a gadajen asibiti, (Take aka dalla hotunansu kwance reras tamkar gawawwaki).." Cire qarar T.V da muke kallon labaran na yi, sannan gaba dayanmu muka qyalqyale da dariya sabanin Fatima da tun dazu take hawaye. Tsit! Muka tsaida dariyar da muke yi, lura da halin da ‘yar uwarmu take ciki, kusa da ita muka koma muka rarrsheta, nice na fara dafa kafadunta na ce, “Haba Fatima, mene ne kuma abin kuka a wannan labari? Ko kina tsoron kar asirin mu ya tonu ne?” Da hanzari ta daga kai wasu sabbin hawayen suna zuba shar.. Gwanin ban tausayi. “Babu abinda zai faru da izinin Allah, ki kwantar da hankaliki, wannan ba shi ne hadari na farko da muka fara shiga ba kuma babu abin da yake faruwa.” Na qarasa fadin haka ina shre mata hawaye, sai da muka tabbatar da ta sami nutsuwa sannan muka koma guraren zaman mu. “Ban san sunayenku ba?” Fatima ta fadi hakan tana kallona ido cikin ido. “Oh my God! Sorry ‘yar uwa.” “Waccen da kike ganinta.” Na fadi hakan ina nuna Rahama, “Sunanta Rahama Muhammad labarinta a taqaice shi ne “Mijinta sun yi aure tun ba shi da komai, shekararsu biyar da aure Allah ya hore mishi arziki fiye da yanda ake zato, lokaci qanqani ya danqara mata takardar saki uku, a fadarshi ba zai zauna da ita mai kashin tsiya ba. bayan kuma suna da yara har biyu mace da namiji a tsakaninsu. Abin takaicin shi ne da ta koma gidan iyayenta sai suka koreta wai lallai ta je ta gyara aurenta, bayan kuma ta sanar dasu saki uku ya yi mata, amma sam sun qi fahimtar ta. Ba komai ya sa suka rufe idonsu a kanta ba illa shi mijin yana musu ihsani ko da ya sake ta ya rigata zuwa gabansu ya fada musu qarya da gaskiya, da ya tashi tafiya kuma ya ajiye musu daurin kudi masu matuqar yawa, baqin cikin haka da rashin samin inda za ta nufa yasa taje jikin wata makaranta Islamiyya tana rusa kuka, a can ne Allah ya hadamu da ita bayan na dawo Islamiyyar, yanzu shekarunta ashirin da uku. “Ita kuma waccen ( na nuna Safiyya) sunanta Safiyya Nuraddeen, saurayinta ne ya yaudareta ya yi mata ciki, iyayenta suka koreta daga gidansu qwata-qwata, saurayin kuma ya gujeta bayan ya qaryata cikin wai ba na shi bane, baqin cikin haka yasa ta yi niyyar shiga duniya akan ko karuwanci ne za ta yi, tana cikin tafiya Allah ya qaddara na bigeta da mota, tun a gurin ta fara zubar jini har muka isa asibiti likita ya tabbatar min da zubewar cikin da take dauke dashi, da ta farfado ne ta bani labarinta, hakan yasa na taimaka mata, yanzu shekarunta ashirin daidai. “Waccen kuma (na nuna Sadiya) ita marainiya ce, mahaifiyarta ta rasu, sunanta Sadiya Ibrahim ta rayu cikin tsananin wahala a hannun kishiyar mahaifiyarta, ba ta san dangin mahaifiyarta ba, don su irin fulanin nan ne masu tashi daga wannan jeji zuwa waccen jeji har Allah ya qaddara aure a tsakanin mahaifinta. Bayan ta girma samari suka fara zuwa neman auranta tana da farin jini sosai, baqin ciki yasa kishiyar mahaifiyar tata ta aura mata wani saurayi, tantiri manemin mata. Shekararsu daya da rabi da aure Allah ya dauki rayuwarshi bayan ya yi jinya mai tsanani harna tsawon wata shida, bayan ta gama takaba sai wasu kuraje masu matuqar qaiqayi suka fara feso mata a jikinta. Bayan binciken da likita yayi ya gano ta kamu da cutar nan mai karya garkuwar jiki, a ranar kishiyar mahaifiyar tata ta kore ta daga gidan, duk dangin mahaifinta kuma sun qi karvarta, hakan yasa ta yanke shawarar neman na kanta dan ta rufawa kanta asiri, wanke-wanke take wa wata mai saida abinci a bakin titi, a nan ne Allah ya hadani da ita har na taimaka mata, tun daga lokacin ta ci gaba da karbar magunguna a asibiti, yanzu shekarunta ashirin da biyu. “Waccen kuma (na nuna Nafisa) sunanta Nafisa Khamis, mahaifinta ne ya yi mata ciki sannan ya koreta a gidanshi don ganin asirin shi yana neman tonuwa…………….” “Mahaifinta fa kika ce?” Fatima ta fadi haka tana zare ido, fuskarta na nuna tsananin mamakin maganar. “Qwarai kuwa" na bata tabbacin haka ina murmushi. " Nafisa ba ta labarin yanda abin ya faru.” Nafisa ta yi gyaran murya ta ce, “Tun wata rana da suka samu sabani shi da mahaifiyata har suka rabu ya fara bibiyata, ina yawan saka kaya mai bayyana surar jikina, ranar da ya fara biyo ni da buqatarsa wuqa ya danna min a wuya wai idan ban yarda ba zai kasheni, ganin da gaske yake yasa na amince a haka har ciki ya shiga jikina, a lokacin ne kuma suka sasanta da mahaifiya ta dawo gidan, kwananta biyu da dawowa ta lura da sauyin da yake jikina, ita ta sanarwa mahaifina, tana ganin kamar ina da juna biyu. Fada ya fara kamar da gaske, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, hankalinshi a tashe ya daukeni a motarsa muka nufi asibiti, likita ya tabbatar da maganar mahaifiyata, tabbas ina da juna biyu. Ni kaina hankalina yayi matukar tashi, tunda muka fito asibitin nake rusa kuka, 'uffan' mahaifina baice min ba, abinda ya daure min kai shine ganin ya nufi bayan gari da motarsa, saida yayi tafiya mai matukar nisa sannan ya tsaida motar, ya fito nima ya umarce ni na fita,bingida ya dauko ya yi arresting dina da ita yana zare min idanu, yace muddin ina buqatar ci gaba da rayuwa kar in kuskura in koma gidanmu da zama balle har in tona mashi asiri, in shiga duk inda naga dama a duniya amma banda dangin mahaifiyata ko danginshi, matukar ya sami labari na a nan kusa to wallahi sayya kashe ni. Daurin 'yan dubu guda daya ya jefo min jikina, sannam yaja motarshi ya tafi bayan ya bade ni da kura, Ina kuka amma bai ko tausaya min ba yayi tafiyarsa, da qyar na fidda kaina zuwa bakin titi, a wannan ranar a hotel na kwana, da safiyar washe gari na nemi wata qawata wacce tun muna makaranta ta taba bani labarin ta zubar da ciki, ta rakani wani voyayyen asibiti na fitar da cikin nan, na sha matuqar wahala kamar ba zan rayu ba, sai daga qarshe Allah ya hadani da Aysa ta taimaka min har kika ganni na zama daya daga cikin yan wannan qungiya.” “Siyama kuma (na nuna ta yatsa manuniya) mahaifinta Ahmad Allah ya yi masa rasuwa tun tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27