Chapter 24
Chapter 24
mata. Gaba dayansu suka bishi da wani mayen kallo kamar zasu cinye shi danye. “Ba kwa amsa sallama ne?” Ya fadi hakan yana qoqarin daidai ta zaman shi a kan kujera. “Yi haquri ba mu ji ba ne Yaya Abdul. Barka da shigowa.” Yasmin ce ta amsa tana jifanshi da tattausan kallo irin na masoya. “Yau wa, ya jikin na ki?” Ya amsa ba tare da ya sake kallon inda take ba. “Sai a hankali Yaya Abdul, wallahi ina matuqar shan wahala…” Ta fadi haka murya a marairace, don a tunaninta zai nuna mata kulawa irin wadda ya sa ba a gaban mahaifanta, amma ga mamakin da ya shayar da ita shine ko kallonta bai sake yi ba, balle tayi tunanin samun amsa ko kuma kulawa daga gareshi, saima maida hankali da yayi wurin canza tashar talabijin daga wanda suke kallo zuwa wadda yake so. A dan kunyace ta kalli Hidaya tana zungurin ta da hannun ta mai lafiya, tayi mata gyaran murya a hankali tana fadin “Yaya Abdul" Ta gane manufar ta don haka ta yi gyaran murya tana fadin “Yaya Abdul barka da yamma.” Sai a wannan lokacin ya kalle su tare da amsa gaisuwar ta fuskarsa ba yabo ba fallasa. Cike da yanga da kwarkwasa a muryarta ganin ta samu shiga harya kalleta ta ce, “Ashe kuma abinda ya faru kenan?” “Eh” Ganin ba shi da niyyar qara wata maganar daga haka, ya tabbatar mata bata samu kar6uwa ba, itama bata ja da nisa ba ta ce, “Allah ya kyauta gaba.” A lokacin yana gab da ficewa daga cikin falon, bai amsa ba, kuma tana da tabbacin ya ji abinda ta fada. Bayanshi suka sake bi da kallo tamkar zasu janyo shi ita da Yasmin din. Abdul-Ahad Muhammad hadad'd'en saurayi kuma dan qwalisa, wanda duk wata mace da za ta yi arba dashi sai tayi sha’awar ina ma ace ya zamo mallakinta. Kallo daya za ka yi mishi ka gane dan fulani ne asali. Duk girman zuriyarsu shi ne ya biyo kakansu Ardo Amadu tamkar kwabo da kwabo, kuma shi ne babba a cikin jikokin Ardon shi yasa tako wane vangare ake matuqar ji da shi. Familyn Ardo Amadu a garin Adamawa ba boyayyu ba ne , domin sun shahara akan abubuwa da dama musamman ilimin boko, dana addini da dukiya, da tsantsar kyau da kuma kyan dirin jiki. Wata dabi'a da suka shahara a kanta shine sam basa auren kad'o sai jininsu na fulani. Duk yawan Family dinsu suna zaune ne a Adamawa, illah daidai ku da suka bar jihar Adamawa zuwa wasu jihohin. kamar mahaifinsu Yasmin da ya dawo garin Kaduna da zama. Shi kuma mahaifin Abdul-Ahad yana can Yola ya na gudanar da kasuwancin shi. Matan aure har guda uku Ardo Amadu ya mallaka wadanda suka haifa mishi ‘Ya’ya goma sha hudu, maza takwas mata shida, mahaifin Abdul Alhaji Muhammad shi ne babba aduk cikin ‘Ya’yan Arxo Amadu, kuma shi yaron matar Ardo Amadu ta biyu ce mai suna Ladi. gidan suna da matuqar hadin kai, bazaka taba iya banbance dan wannan dakin da dan wancan dakin ba. A bayan Abdul Ahad akwai jikoki da dama a zuriyar Ardo Amadu. Ardo ya haura shekara saba'in da biyar a duniya, amma idan ka gan shi za ka yi tsammanin bai wuce shekara hamsin da biyar ba, domin ya yi tsufa ne na ilimin addini, duk wanda ya yi tsufan ilimin addini kuwa ba ya kwarkwancewa. Abdul -Ahad tun yana dan qaraminshi yaro ne mai matuqar sha’awar aikin dan sanda, idan yana zaune da kakanshi ba shi da wata magana sai ta idan ya girma Police zai zama "Ashe za ka zama abokin kowa kenan.” Amsar da Ardo yake ba shi kenan tare da alqawarin matuqar yana raye sai ya cika mishi burinshi. duk Familynsu ba su san wannan aikin na dan sanda da yake buri , amma da yake gaba da gabanta tunda ya samu goyon baya daga Ardo dole kowa ya tsuke bakinshi tareda yi mishi fatan alkhairi. Kwanci tashi ba wuya a wurin Ubangiji ga shi yau har Abdul ya zama Inspector a gurin aikinshi na 'yan sanda. yana samun qarin girma akai akai saboda jajircewa da qwarewa akan aikin shi, dan sanda ne mai matuqar gaskiya wanda bayajin kunyar gurfanar da duk wani wanda ya yi laifi agaban hukuma, koda kuwa jininshi ne. Addu’ar kakanshi yana bibiyar shi aduk inda ya shiga, yasha fadawa hadari da dama amma cikin hukuncin Ubangiji yakan tsallake. Irin su Abdul su ake buqata a hukumar ‘Yan sanda saboda aduk inda ya tsinci kansa yakan tuna da rantsuwar da ya yi akan zai aikata gaskiya ko mahaifansa ne. Ardo kullum yana qara ba shi qwarin gwiwar tsayawa akan gaskiya. Transfer ya samu daga Abuja zuwa Kaduna, hutun kwana bakwai aka ba shi don ya gama kimtsawa zuwa Kaduna da wannan damar ya yi amfani ya je Yola ya kwana uku. Ardo ya bashi addu’o’i na musamman wadanda zai gudanar ranar da ya fara shiga ofis dinshi na Kaduna. Sannan ya sake mishi tuni akan lokacin aurenshi da ‘yar uwarshi Yasmin da a kullum yake qara kusantowa. (shekarun Abdul-Ahad talatin da biyar a duniya amma sam ba shi da niyyar yin aure, haduwar Familyn Ardo maza da mata gaba daya da babbar sallah yasa aka yanke shawarar hada aure tsakanin Abdul da Yasmin, mahaifan gaba daya sunyi farin ciki, ya yinda sauran ‘yan matan Familyn baqin ciki ya cika zuciyarsu kowacce taso zabin na Ardo ya fada kanta, amma sai ya fada kan Yasmin da take kallon kowa a dage, bayan sunfi ta kyau da komai da komai. Dole suka hadiye baqin cikinsu gurin yi mata fatan alkhairi, a fili Yasmin take nuna tsananin so da kishin Abdul-Ahad. A gurin Abdul kuwa ba yabo ba fallasa, dole yaso duk abinda Ardo ya za6a masa don haka ya fara qoqarin cusa sonta a zuciyarshi. Rashin tarbiyya da rashin sanin ya kamata shine babban abinda yake hada shi da ita. Bayan taron ne Ardo ya kebe da Abdul yayi mishi bayanin dalilin da yasa ya za6a mishi Yasmin a matsayin matar aure. "Baffanku na Kaduna masifar son ‘Ya’yanshi biyu tak da ya mallaka a duniya Ahmad, (Abba kenan mai sunan Ardon) da Yasmin ya rufe mishi ido, shiyasa ya kasa basu kyakykyawar tarbiyya, duk wanda aka hada Yasmin aure da shi ba za suyi zaman dad'i ba, kai ne kawai kake da qwanjin da za ka iya tanqwarata tabi umarninka, bayan haka kuma na fahimci tana son ka” Da wannan qarin bayanin da Ardo yayi mishi yasa ya daina damuwa da duk wani al’amarinta) Abba Yayan Yasmin babu abinda ya tasa a gaba sai shaye shaye da neman mata, qungiya suke da ita mai suna Big Boys a cikin garin Kaduna, hatta irin askin da suke yi a kansu ya fita daban, da an gansu ake ganesu, duk yarinyar da suka dora idanunsu akanta ta shiga uku, ko ta wane hali sai sun biya buqatar su a kanta. Wani abin takaici shine duk iyanyansu manyan masu kudi ne, da an kamasu basa yini a kulle ake sakinsu, duk wani iskanci sunayinshi ne da daurin gindin mahaifansu. Tunda Abba ya gama Secondary School a daddafe ya watsar da karatun, su kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27