Chapter 18
Chapter 18
ba yabo ba fallasa, daga gaisawa babu abin da yake hadani dashi, babu ruwanshi da ni, naci abinci ko banci abinci ba duk bai damu ba. kuma baya kwana biyu a gida, kullum cikin tafiye-tafiye yake, yayin da ni kuma kullum qara shaquwa muke da Mahfuz. Wata rana da daddare misalin qarfe tara da rabi na dare, a wannan lokacin na shekara har da wata biyu a gidan mahaifina, kuma har a wannan lokacin sai na sha kayan maye nake iya barci. Mahaifina baya nan, don haka tun qarfe takwas na dare na rufe gida da qofofin dakunan mu, Kamar a mafarki nake jiyo qwanqwasa get din gidan mu a hankali, lokacin na yi mankas da kayan maye barci kawai nake shirin yi, jin bugun qofar ya qi qarewa yasa na miqe ina tangadi na fita zuwa gurin get din. “Wa...ne...ne..?” Na tambaya da muryar maye. “Qanwata mai kyau ni ne.” Ya amsa muryarshi qasa-qasa. Bude masa qofar nayi ya shigo, ni kuma na lallava na koma ciki don ji nayi ina shirin faduwa qasa warwas, shi ya mai da qofar ya rufe ya biyo bayana zuwa cikin falo. Bani a falon don haka ya bini zuwa cikin dakina. Ina kwance nayi daidai a kan gado ina sharar barci, sanye nake da kayan barci masu matuqar ban sha’awa da nuna surar jiki. A wannan dare Mahfuz ya yi niyyar keta min haddi kota wane hali. Amma ina Allah bai bashi sa’a ba, daga inda yake tsaye a tsakar dakin yana kallon surar jikina sanye da dan pant fari da farar best wacce ta kamani tsantsan. A saman best da pant din ne na dora rigar barci mai nuna tsiraici. Yana tsaye yana kallonta cike da sha'awa, idan ya yunqura da nufin fadawa gadon kusa dani sai wani farin haske ya dakatar dashi. Wannan shi ake kira ga “Qoshi ga kwanan yunwa” ya fadi hakan a zuciyarsa, “Ina... wallahi ba za ta savu ba, tsawon shekara daya da wata biyu ina wahala da yarinya amma lokacin fanshewa kuma ya gagara? Wannan sam ba zai yiwu ba.” Ya fadi hakan a fili yana maganan yana tube kayan jikinsa. Yana tsaye haihuwar uwarsa a tsakar dakin, yana safa da marwa da tunanin ta inda ya dace ya afkamin don samun nasarar aiwatar mummunan manufarsa a kaina. Rintse ido yayi ya yi miqa sannan ya daka tsalle da niyyar fadawa kaina, wanna karon ba haske bane ya tare shi, shoking ne da wani tiriri mai matuqar zafi daga jikina suka watsar dashi a jikin bangon dakin. Take ya zube qasa a sume kansa ya bugu da jikin bango, iska mai matuqar qarfi ya ci gaba da hurgi dashi a jikin bango daga wannan kusurwa zuwa waccan kusurwa. Duk wanna abin da yake faruwa bani da masaniya ina kwance ina sharar barci hankalina kwance da taimakon kayan maye, ban farka ba sai da gari ya waye tangararan, duk jikina ba qarfi tamkar wacce aka yiwa dukan tsiya, da qyar na lallaba na dauro alwala na gabatar da sallar asubahi ina ta “Istigifari” a zuciyata. Motsin da nake jiyowa a falo yasa na fara tunanin ko Abbana ya dawo ne? Ina shirin miqewa don zuwa gaidashi naga an turo qofar dakin an shigo da sallama. Fuskar wacce na gani yasa na miqe da sauri ina nunata da dan yatsa manuniya sannan na ce, “Anty Hassana...” da gudu na rungumeta ina ihun murna daga bisani kuma na fashe da kuka, ita ma kukan take tana shafa kaina alamun rarrashi, sai da na yi mai isata sannan na dago da fuskata ina kallonta na ce, "Ina Anty Hussaina?” Da hannu ta yi min nuni zuwa qofar dakin, tana tsaye ta nade hannuwanta a qirji tana share hawaye da dan qyallen da yake hannunta. Da gudu na qarasa gareta na rungumeta ina hawaye. Saida muka nutsa muna zaune a tsakar dakin, in kwanta a jikin waccen, in koma jikin waccan zuciyata cike da farin ciki. “Kun manta dani tunda Ammi ta rasu baku qara waiwayata ba sai yau.” Na fadi hakan kaina yana cinyan Anty Hassana, qafata kuma yana jikin Anty Hussaina tana jamin ‘yan yatsun qafar a hankali. “Shit...! kar ki sake fadin haka, bamu manta dake ba, wasu al’amura ne suka sha kanmu, amma a kullum kina zuciyarmu, kuma daga yau ba zamu sake nesa dake ba, a kullum zamu kasance tare idan mahaifinki baya nan.” “Wanene Mahfuz?” Anty Hussaina ta jefo min tambayar ido cikin ido take kallona. “Maqwacin mu ne, a kullum shi yake debe min kewarku da ta Ammi, amma baya zuwa sai idan Abba baya nan.” “Kin manta da nasihar da Ammi ta yi miki ko? Kin manta kullum saita fada miki kiyi hankali da maza saboda yawancinsu mugaye ne ko? Ko kin manta tarihin zaluncin mahaifinki ga mahaifiyarki? Kin san babban illar da Mahfuz din nan yaso ya yi miki kuwa?” Nan ta bani labarin duk abinda ya faru a daren jiya da ya shigo. Tuni idona ya fara tsiyayar hawaye, a zuciyata ina tuna Ammi da jan kunnen da take min a kullum a kan maza. Zuciyata tana tuquqi ina yiwa mahaifina da mahfuz da duk wani namiji azzalumi “Allah ya isa.” Anty Hassana ce ta ci gaba da cewa “Wadannan kwalaben magungunan da qwayoyin da yake baki da sunan maganin barci qarya yake yi, magungunan da yake gusar da hankali da tunanin dan adam ne, fitar dake yake daga cikin hankali da tunani irin na dan adam mai cikakken hankali, a taqaice dai kayan “maye” yake baki kina ta durawa cikin ki tsawon shekara da wasu watanni, don haka ya zama dole ki tattarosu gaba daya a zubar dasu, kuma ki dauki alqawarin daina shan komai daga rana mai kamar ta yau.” A lokacin da nake harhada kwalaben magungunan da qwayoyin banji komai na daga dacin rabuwa dasu ba, sai ma wani sabon tsana da tsantseni da yake cikamin zuciya. A ranar na yini cikin matuqar farin ciki da walwala da kuzari, Domin su Anty Hassana suna tare da ni. Sun tsefe min kaina sun wanke tas, sannan Anty Hussaina ta tsantsara min kwalliya cikin qananan kaya sabbi daga cikin kayana, Ni kaina na san na yi kyau balle kuma ga wanda zai dora qwayar idonsa a kaina. Girki mai rai da lafiya Anty Husaina ta fita ta amso mana amma ban san ko daga ina ta amso abincin ba. A wannan ranar kwana muka yi muna hira, duk yanda suka so in yi barci in huta barcin ya qi zuwar min haka nan suka haqura muka ci gaba da hira har aka kira sallar asuba. Mahaifina ya kwana biyu baya gida, hakan ba qaramin dadi ya yi min ba, domin na samu sakewa dasu Anty Hassana, kuma sun fada ranar da mahaifina zai dawo zasu tafi, a sallah har addu’ar kar Allah ya dawo dashi na ke yi abinku da quruciya. Wasu farin girki...tsawon wadannan kwanaki biyun ko gyangyadi ban yi ba, hakan ba qaramin dagawa su Anty Hussaina hakali ya yi ba, ni kaina ina so in yi barci amma barcin ya qi zuwa, tuni idanuna sun fara qanana domin ba a cin bashin barci. A daren rana ta ukun ne na sakawa su Anty Hassana kukan barci
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27