Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jinjina saqon a zuciyata, kaina ya kulle don haka na rasa irin tunanin da zan yi, ta riga ta gama daure ni da jijiyoyin jikina, domin ta had'a ni da girman Allah dana manzon Allah S.A.W. “Dole inje wannan taron" Na ayyana hakan a zuciyata. “Me ya faru Aysha?” Muryar Baba Jummala na jiyo tana tambayata da alamun damuwa a muryar ta. kallonsu na yi daya bayan daya ina qoqarin yalwata fuskata da murmushi don in kwantar musu da hankali. gaba dayansu hankalinsu yana kaina, duk da murmushin da nake binsu dashi baisa sun saki fuskokinsu ba. “Ku kwantar da hankalinku, ba wani abin damuwa bane, bikin murnar ranar zagayowar haihuwar Hajiya Danasha za'ayi, shine ta turomin da saqo tana had'ani da girman Allah in daure in halarta" “Hajiya Danasha hatsabibancinta ya wuce duk yanda muke tsammani, tasa a dauki ran wanda baiji ba bai gani ba ba wani matsala ba ne a gurinta, ina ganin bai kamata ki halarci wannan taron ba, domin sam ba ta nufinki da alkhairi.” Baba Jummala ce ta fara fadin hakan fuskarta na bayyana matsananciyar damuwa. “Ni kam idan na ji sunanta gabana har faduwa yake.” In ji Rahma da ta zabga tagumi hannu bibbiyu. “Nima dai ina tare da shawarar Baba, kamata ya yi ki yanke hulda da ita, kamar yanda ki ka fada da farko.” Inji Safiyya kenan da ta dafa kafad'ata don kwantar min da hankali. “Tsohuwar ce dole aji tsoranta, domin da ganin idanunta akwai karancin tsoron Allah a tattare da ita.” In ji Nafisa da take zaune acan gefe guda. “Me ake da mace mai sana’ar neman jinsi?” inji Siyama da take zaune kusa da Fatima. “Kudai yi a hankali da bakunanku, don irin wadannan tsofaffin sun wuce duk inda ku ke tunani.” Sadiya kenan da tunda aka fara maganar ba ta ce komai ba. “Ku saurara muji shawarar da Aysha ta yanke kafin mu samu damar tofa albarkacin bakinmu.” Suhaila ta fadi haka tana kallona don jin abinda zan fada. “Nima dai Duk da bansan Hajiyar da ake magana a kanta ba amma na ji na tsaneta, domin sam bata samu shaidar arziqi ba.” Fatima ta fadi haka tana kallon kowa dai dai. Dariya na yi dana fahimci duk sun gama maganganun su, sai da na dan ja fasali kamar bazanyi magana ba sannan nace, "Tabbas Hajiya Danasha hatsabibiya ce kamar yanda kuka fada, kuma tana iya aikata komai idan ta qyalla idonu taga kin kwanta mata arai, daukar ran mutum ba wani abu ba ne a gurinta kamar yadda Baba Jummala ta fada, amma inaso ku tuna da wani abu guda daya da ku ka manta dashi. Mu mun dogara da Allah ne, don haka duk abinda zai sameni ko kuma ya samu daya daga cikin mu tuni Allah ya riga ya qaddara hakan, don haka Hajiya Danasha bata isa ta sani aikata mummunar sana’a irin tasu ba, kuma bata isa ta aikata mummunar abu aikana ba sai abinda Allah ya qaddara zai faru dani. Don haka a gobe zan shirya da yamma in ziyarci taron data gayyaceni ba tareda rakiyar ko mutum daya daga cikinku ba, da Allah na dogara, kuma shi zai kareni daga sharrinta kamar yanda ya kareni daga sharrin mahaifina da tantirin matsafi Alhaji Buba.” Ina gama fadin haka na nufi dakina ba tareda na sake kallon ko mutum daya daga cikinsu ba, a zuciyata nake tunanin ranar farko na haduwata da Hajiya Danasha. " Tun wani fita da mukai zuwa Mr. Bigs don siyo kayan qwalam da maqulashe muka hadu da Hajiya Danasha, yau kimanin wata daya kenan da haduwarmu da ita. Tun a haduwar farko da mukai tayiwa Aisha tayin sana’arta na ‘yan jinsi tsakanin mace da mace, fahimtar da ta yi bata da arziqin da zata shawo kan Aisha yasa ta cigaba dabi ta hanyoyin hikima domin tasamu mu tsunduma a harka irin tasu. Wayar qarshe da sukayi da Aisha karkiso ki ji irin baqaqen maganganun da Aisha ta fada mata, amma saboda tsabar rashin zuciya kinga yanzu ta sake nemanta.” Suhaila ce take yima Fatima qarin bayani akan Hajiya Danasha. “Subhanallahi, masifar da aka hallaka mutanen Annabi Hudu saboda ita? Ubangiji Allah ya tsaremu ya tsare duk wata ‘Yar musulma da fadawa cikin wannan kazatacciyar harka, su kuma masu yi Allah ya shirye su.” Ta fadi hakan hankalinta a tashe, zuciyarsa cike da k'yama da tsantseni. “Amin summa Amin" Suka amsa gaba dayansu. *** Qarfe bakwai ne na yammacin washegari na shirya na bar gida. Akwai dan cinkoso a hanyar zuwa gurin taron, hakan yasa na dauki tsawon minti talatin ina tuqi kafin in fara hango gurin taron, jami'an tsaron dana gani sama da mutum shida shi ne abinda ya bani mamaki. “Lallai shaidanci ya samu gurin zama a qasar nan.” Abinda na fada a zuciyata kenan ina qoqarin daidai ta fakin din motar dana hawo 406 mai launin ruwan toka, ina sanye da baqar doguwar riga wacce ta yi matuqar dacewa da launin fatar jikina, dan qaramin Baby Hijab baqi na sanya fuskata, powder kawai na shafa a fuskata sai dan man baki dana goga a la66ana, amma ba qaramin kyau na yi ba, sai kai tsammanin na dau tsawon awanni ina wannan kwalliya saboda irin kyan dana yi, shigata da kuma motar dana hawo zuwa gurin sunyi matuqar dacewa tare da qayata kwalliyata, ganin jami’an ‘Yan sanda sun nufo motar yasa na tsaya tare da sauke glass din motar ina jiran qarasowarsu. Tun kafin in daidaita fakin idonshi yana kan motar, sauke glashin da nayi ya hango fuskata yasa ya sauka daga kan motar da yake zaune ya nufi gurin. Farin ciki ne fal a ranshi, domin bayyi tsammanin sake haduwa da ni anan kusa ba. “Hajiya barka da yamma, ina katinki?” Dan sandan ya maimaita tambayar da ya yi min akaro na uku tun bayan isar shi gurin, ban kalleshi ba kamar yadda ban yi niyyar amsa mishi tambayar da yake min ba, isawarshi gurin yasa suka sara mishi, da hannu yayi musu umarnin wuce gurin aikinsu, sannan ya matsa daf da gilashin motar ta inda nake tuqin. “Zahra’u…!” Abinda ya fada kenan da tattausan muryarshi mai daukar hankalin duk wacce ta saurara. Sai da na 6ata tsawon daqiqa talatin ba tareda na kalleshi ba, idanuna suna kan wayata da take riqe a hannuna ina niyyar kiran Hajiya Dansha, saida na kara wayar a kunnena sannan na dago fuskata na kalleshi na watsar. Duk da cewa duhun dare ya fara shiga sosai amma haske tar agurin kamar rana, an qawata ciki da waje da manya manyan qwayayen lantarki yanda ko allura ce ta fadi zaka iya dauka, idanuna cikin nashi mukai musayar kallo na tsawon daqiqa goma sannan na sadda qwayar idanuna qasa ina fadin “Hello….” daga can 6angaren Hajiyar ta dauka tana ta nanata “Hello kina jina?” “Eh, Na iso amma jami’an tsaro sun hanani shiga, so zan juya don haka karki zargeni da rashin ganin girman Ubangiji na” Ina gama fadin haka na katse wayar ina niyyar tada motar, duk iya wannan lokacin ya na tsaye a inda yake ya zurawa qwayar idanuna ido, ashe musayar kallon da mukai dashi ne abinda ya kashe mishi jiki, din haka ya dau tsawon lokaci ya na

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});