A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel

A Dalilin Da Namiji A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel

A Dalilin Da Namiji Book 1 description: A yau ne Alqalin babban kotun da yake cikin garin Kaduna ya yanke wa wata mata mai suna Fatima Ibrahim hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari, bisa laifin da ake tuhumarta da shi na halaka babban ɗan mijinta mai suna Nasir ta hanyar watsa mishi ruwan zafi duk jikin sa, wanda hakan ya yi sanadiyyar salwantar duk wata fata da take jikinshi. Bai ɗau awa ɗaya ba a asibitin BIBA HOSPITAL ya ce ga garin ku nan.

Mijin matar mai suna Alhaji Muhammad shi ya danƙa matar ta shi a hannun hukumar ‘yan sanda kuma ya tsaya tsayin daka akan lallai sai da ya ƙwatar wa ɗanshi mai rasuwa haƙƙin shi akan azzalumar matar ta shi, wacce ba ta da tsoron Allah ko kaɗan a zuciyarta inji mijin nata.

Ga dai yadda tattaunawar tamu ta kasance da shi.

Gaba ɗaya ‘yan matan da suke zaune a tafkeken falon suka ƙara shiga nutsuwarsu domin jin yadda tattaunawar za ta kasance.

Fitowa ta kenan daga banɗaki ɗaure da towel a jikina, na rufa wani ƙaramin tawul a kaina, fuska babu walwala na zauna a kan cushion mai zaman mutum uku, sannan na ɗauki remote a gefena na ƙara volume ɗin television sosai tamkar zai fasa mana dodon kunne.

Tattaunawa da Alhaji Muhammad

“Ya sunan Malamin?”

Ɗan jaridar ya jefa wa mutumin da suka kira mijin matar da ake tuhuma tambayar.

“Sunana Muhammad Yusuf.Alhaji

Mutumin ya amsa da cikakkiyar murya da ba ta nuna jimami ko kaɗan.

“A yau ne aka kawo ƙarshen shari’ar nan da aka ɗauki tsawon watanni uku ana yi tsakanin mai ɗakinka Malama Fatima da marigayi ɗanka Nasir. Me za ka iya cewa akan hakan?”

“Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) da ya kawo ƙarshen wannan shari’ar. Tabbas ina cikin farin ciki da godiya ga Allah domin an fitar wa da mai haƙƙi haƙƙinsa.”

“Mata irinsu Fatima waɗanda ba sa tsoron Allah ko kaɗan a zuciyarsu wannan ya ishe su darasi idan har suna da tunani.”

“Tun lokacin da marigayi Nasir Allah ya jiƙan shi ya tabbatar min da Fatima ce ta aikata mishi hakan kawai don ya ziyarci gidan ta a matsayin shi na ɗan mijinta karo na uku tun bayan dawowar shi daga ƙasar Malaysia karatu.”

“Lokacin da ya faɗa min hakan bai fi saura minti ashirin Allah ya ɗauki rayuwarsa ba, kuma na ɗaukar mishi alƙawarin ko da zan yi yawo tsirara sai na ɗaukar mishi fansa.”

“Don haka a yau ina mai farin ciki matuƙa. Su kuma masu irin halinta ina masu fatan Allah ya shirye su idan kuma ba masu shiryuwa ba ne Allah ka tarwatsa su a duk inda suke a faɗin duniya.”

Tambayoyi Akan Aurensu

“To yanzu ya matsayin igiyar auren da yake tsakanin ku?”

Ɗan jaridar ya sake jefa mishi wannan tambayar.

“Tun ranar da abin ya faru na yanke igiyar aurena duka ukun da yake tsakanin mu, kuma na danƙa mata takardar ta tun kafin a kawo ƙarshen wannan shari’ar.”

“Akwai zuriya a tsakanin ku?”

“Babu yaro ko ɗaya a tsakanin mu shekarar mu biyu da aure amma ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba.”

“Ba ka tunanin wani irin kallo da iyayenta za su yi maka?”

Ɗan jaridar ya sake tambayar shi.

Muryarshi a fusace ya amsa da cewa:

“Ita ɗin marainiya ce a hannun ƙanin Babanta na aureta, kuma tun da ya ji abin da ta aikata ya zare hannunshi daga kanta bayan ya yi mata Allah ya isa rainon da ya yi mata.”

“Kuma ko iyayenta suna da rai ba zan damu da duk wani abu da za su ce ba, don kuwa ɗa bai fi ɗa ba.”

“To amma…”

Read Also:

A Wani Masarauta Book 2 Complete Hausa Novel

“Dakata Malam! Tambayoyin naka sun ishe ni haka, ina da abin yi.”

Ya katse ɗan jaridar yana gwama numfashi cike da fusata.

“Ƙarshen tattaunawar da ta gudana tsakanin wakilin mu kenan da mijin mai laifin. Wakilin namu ya nemi tattaunawarsa da uwar marigayi amma hakan bai samu ba.”

“Kuma ya nemi tattaunawa da mai laifin ita ma ta ƙi ba mu haɗin kai. Kalma ɗaya kawai ta iya furtawa ga wakilin namu.”

A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel

1 thought on “A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel”

Leave a Comment