Chapter 14
Chapter 14
ya sha garin kwaki da suga shi ma kadan saboda maleji. A yawon neman arzikinshi ne Allah ya hada shi da wani ubangida mai matuqar dukiya a garin Kaduna, Ya tara arziki mai matuqar yawa a dalilin wannan ubangida nashi, shi kan shi ba zai ce ga inda Alhaji Buba (ubangidanshi) yake samun kudi ba, kuma bai san taqamaimai sana’ar ubangidanshi ba, kawai dai kudi yake kashewa bana wasa ba. Sai da mahaifina ya shekara arba’in a duniya ba tare da ya yi aure ba, tsabar son kudi irin nashi yana jin matuqar ciwo ya kashe naira dubu dari biyar ya yi aure, Sai da Alhaji Buba ya yi masa alqawarin ya nemo matar zai bashi kudin auren sannan ya je gidan marayu ya zabo mahaifiyata ya aura, kudaden da Alhajin ya bashi kuma na hidimar auren ya zuba a account dinshi, yaci gaba da tara dukiya. Alhaji Buba ne ya bashi kyautar gida mai kyau a unguwar Rimi, kuma yayi masa kashaidi da tsoratarwar cewa matuqar ya sai da gidan nan to qarshen alaqarsu ta zo, wannan shi ne dalilin da yasa ya haqura suka zauna da amaryarsa Aisha (mahaifiyata) a wannan gida, amma kullum zuciyarshi quna take yi don yana ganin almubazzaranci ne. Duk kyan gidan da suke ciki amma babu abinci mai kyau, sai mahaifiyata ta yi wata uku ba ta ga idon shinkafa ba, kullum girkinta daga tuwon masara miyar kuka ba nama ba kifi, sai jiqon garin kwaki da manejin sukari, ko kuma ta kwadanta shi da kuli-kuli. Kuma abin da zai baku mamaki shi ne, shi kan shi mahaifina haka yake cin wannan abincin ba tare da wani damuwa ba. Watan su biyu da aure mahaifita ta samu ciki mai matuqar wahala da laulayi, sam ba ta iya hassala aikin komai a gidan, kuma ba ta iya cin abincin da mahaifina ya bari a gidan, tana buqatar ababen marmari dana kwadayi, mahaifina yayi tsalle ya dire kan cewa ba ta isa ta sashi asarar kudinshi ba, duk yanda taso ta fahimtar da shi ya qi fahimta, daga qarshe ma cewa yayi saidai cikin nata ya zube matuqar sai ya barnatar da kudinshi a kanta. Wani baqin hali da mahaifina ya ke da shi shi ne na hana mahaifiyata fita ko da maqwabta ne balle gidan marayu inda ya aurota, kuma ba ta da waya balle ta kira hukumar gidan marayun ta sanar da su halin da take ciki, idan zai fita sai ya kulle get din gidan ta waje yanda babu ta yadda za ta iya fita balle har ta sanarwa da wani halin da take ciki. Cikinta yana girma jikinta yana kara bushewa, kallo daya za ka yi mata ka tabbatar tana fama da qarancin jini a jikinta, duk wannan bai sa mahaifina ya tausaya mata ba. Idan yaga tayi kwana da kwanaki ba ta iya barci sai ya sami almajirai ya turasu daji su debo mata sassaqen madaci da ganyayyaki masu illah ga mace mai juna biyu ya dafa ya tilasta mata shan su, kuma tunda mahaifiyata ta samu ciki ba ta taba ziyartar asibiti ba, wannan shi ya kara haifar mata da mummunar matsala ba tare da saninta ba. Cikinta har ya shiga wata na goma sha daya ba haihuwa ba alamarshi, lokacin ta koma tamkar kwarangwal saboda matuqar rama, sai tirtsentsen ciki a gaba wanda har rinjayarta yake wani lokacin. A wannan lokacin da mahaifiyata take buqatar taimako daga mahaifina shi kuma sai ya tsiri tafiye-tafiye, sai yayi kwana biyu bashi a gida, Duk da hakan dai bai fasa kulle gidan ta waje ba idan zai fita. Wata rana da daddare naquda ya tasowa mahaifiyata gadan-gadan, gashi kuma mahaifina baya gida, duk yanda taso zuwa ta bubbuga qofar get din gidan ta ciki ko Allah zai sa wani ya jiyota daga waje ya kawo mata dauki ina….!!! Allah bai bata ikon hakan ba, tayi matuqar galavaita yanda ko dan yatsanta ta kasa dagawa. Abin da ya qara daga mata hankali shi ne yanda jini yake bin qafafuwanta, duk da dai ba ta taba haihuwa ba, kuma ba’a taba haihuwa a gabanta ba ta san akwai gagarumin matsala daga wannan jinin da taga yana biyowa daga qasanta. Ciwo ya yi tsanani gareta, azaba tayi azaba, kuma haihuwar ta tsaya cak sai azabar ciwon mara da baya da duk wani sassa na jikinta, ta sadaqar da ci gaba da rayuwar duniya, don haka ta lumshe ido tana kalmar shahada a zuciyarta. Kamar daga sama taji ana gyara mata zaman dirshan din da tayi a kan tiles ana bubbuda qafafunta. Daqyar ta yi nasarar bude idanunta don ganin mai mata wannan taimakon, tsohuwa ce don a kiyasce ta haura shekaru hamshin da biyar, da taimakon Allah da taimakon wannan tsohuwa mahaifiyata ta haifeni. Tana haihuwa ta waiwaya don ganin abinda Allah ya ba, na fado duniya cikin riga irin wanda ake haifar wasu jariran da ita, idanuna a bude suke qyar ina kallon ummata yayin da ita ma take kallona, ita kuma wannan tsohuwa ta yi qoqarin yage rigar jikina, kallon dakiku talatin ya ratsa tsakanina da ummata sai ta maida idanunta kan wannan tsohuwa da ta taimaka mata tace “Ga amanar ‘yata nan a hannunki, Allah ya yi mata albarka…..” Tana gama fadin haka ta yi kalmar shahada ta ce ga garinku nan! Tsohuwa nan ita ta gyara komai na gurin da Ummata ta 6ata, sannan ta yi min wanka ta nad'e ni cikin wani zani na Ummata, ita ta yiwa mahaifiyata wankan gawa stab! Bayan an idar da sallar asubahi ta sanarwa da maza a masallaci akwai jana’iza a gidan mu. Duk mazan Unguwar ba wanda yake da number wayar mahaifina, domin duk yanda suka so qulla alaqar maqwabtaka da shi ya qi bada fuskar hakan sai suma suka fita daga hanyarshi. Matan maqwabta su suka hada kayan jarirrai masu matuqar yawa aka ba tsohuwar nan ta ringa saka min, tun ina jaririyata ina da farin jinin jama’a, duk wacce ta kalleni sai ta ji qaunata a cikin zuciyarta, hakan yasa na sami kyaututtuka mai yawa daga iyaye mata da maza. Har aka yi kwana uku da rasuwar mahaifina bai dawo ba, don haka maqwabtan mu su ka yi addu’o’insu ga mahaifiyata suka watse, gidan mu ya rage daga tsohuwar nan sai ni ‘yar jaririyar kwana uku a duniya, wannan lokacin har na qware a shan madarar jarirai da maqwabta suka tara min katan-katan, na yi ‘yar qiba tamkar wacce ta yi kwana arba’in a duniya. Kwanan mahaifiyata hudu da rasuwa mahaifina ya dawo daga tafiyar da suka yi shi da ubangidanshi, yayi mamaki tun a qofar get da ya ga qofar gidan shi a bude, ba kamar yanda ya barshi ba, don haka ya fara shirya kwandon bala’in da zai sauke mata idan ya shiga cikin gidan, kamshin hadadden girkin da ya jiyo daga ciki ya sa ya fara mai da masifarshi ciki don dai dama ya qware a son cin banza, ya fitar da kudin shi ya yi cefane ne dai ba zai iya ba. Tsohuwar da ya gani tana tarairayar jaririya tsakar falon gidan yasa jikinshi ya fara sanyi, duk da dai a ranshi bai kawo cewar mahaifiyata Allah ya yi mata rasuwa ba, ko sallama bai yi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27