Chapter 25
Chapter 25
iya yanshi suka zura masa ido domin suna matuqar son shi, tun yana dan qarami suka 6ata shi, don haka har ya girma ba kwa6a ba hantara, idan ya tasasu agaba da masifa sai kayi tsammanin shine uban su kuma ‘ya’yan. Amma hakan bai hana idan ya fita ya dawo iyayan su fara rarrashinshi. Yasmin tana masifar tsoronshi, don sam baya mata da wasa, idan ya fara dukanta tamkar Allah ne ya aikoshi. Da magiya da ban haquri iyayan suke qwatar ta a hannunshi, shi yasa indai tasan yana gida bata ta6a yin abinda za ta kuskure a gareshi. A duniya idan akwai wanda Abba yake masifar jin tsoro to Abdul ne, shi ya sa iyayanshi da Yasmin suke matuqar qaunar zuwan Abdul gidan domin hatta tsawon daren da yake dauka bai dawo gida ba matuqar yasan Abdaul yana gari to yana ragewa, hatta abokan shaidancin shi yana jan baya dasu kuma yana gargadin su ja baya da ziyartar shi har sai Abdul ya bar garin Kaduna, shi yasa a ranar da Abdul ya tabbatar mishi ya dawo garin Kaduna da aiki kusan kwana biyu yayi bai yi barci ba, hankalinshi ya yi matuqar tashi, domin ya san duk inda yasa qafa Abdul yana bin diddiginshi a fili da 6oye, amma daya samu tabbacin ba gidansu Abdul din zai zauna ba sai hankalinshi ya dan kwanta, don yana tunanin komai zai zamo mishi da sauqi tunda ba makwancinsu daya ba. A ranar da Abdul’Ahad ya cika kwana hudu da zuwa garin Kaduna a ranar ya fara shiga sabon Ofishinshi, ya yi addu’o’I da dama akan Allah ya bashi ikon tsayuwa akan gaskiya komai dacinta, kuma yayi addu’ar Allah ya bashi ikon gyara hukumar su ta ‘Yan sanda don ya fahimci akwai gyare gyare masu dama a hukumar ta su, cin haci da rashawa ya zama tamkar ruwan sha da abincin mafi yawa daga cikinsu “Matuqar ka ce ba zaka karbi cin hanci ba to kana tare da fuskantar qalubale mai matuqar girma daga gurin gur6atattun manya na sama damu.” Wannan bayani ne da wani dan sanda da yake qarqashinshi ya yi mishi lokacin da suke tsaye suna duba duk motar da za ta shige layin gidan Gwamna, wani Alhaji ne ya damqo ‘yan dubu dubu har guda biyar ya miqa mishi lokacin da ya umarci motar tasu ta sauka can gefen titi don yayi binciken qwaqwaf a kanta. “Ba ko wane dan sanda zaka gani akan titi ka miqa mishi cin hanci ya kar6a ba…” Ya fadawa Alhajin haka fuskarshi a daure tamau, zuciyarshi a mugun 6ace. “Inspector ba cin hanci na ba ka ba, ganinka nake tamkar dan cikina, don haka na baka wannan ne kasha ruwa.” Alhajin yayi saurin juyar da maganar don ganin tayin nashi bai samu shiga ba. “Ok to na gode, ka bar kudinka, ina buqatar ganin takardun motar ka.” Sai da Alhajin ya bata sama da minti ashirin a gurin, domin duk wani lungu da saqon motar sai da Abdul ya duba sannan ya bashi umarnin wucewa, haka kawai jikinshi ya bashi Alhajin ba shi da gaskiya amma duk iya binciken shi bai gano komai ba. Bayan motar ya bi da kallo a zuciyar shi yayi qwafa tare da fadin “Lokaci na gaba….” Shi ma Alhajin ta jikin madubi yake kallon Abdul yana jinjina qarfin hali irin na yaron, wannan shine karo na farko a tarihin rayuwar shi da wani dan sanda yayi mishi bincike a motar shi, duk Check point din da zai wuce sai dai ‘Yan sanda suyi mishi kirari ya basu na kashewa, don haka hoton fuskar matashin dan sandan ya zauna daram a zuciyar shi. **** Muna zaune a falo muna hira cikin farin ciki da annashuwa, Baba Jummala ce take mana tatsuniyar Yar mowa da ‘Yar bora, hatta Fatima da take baquwa ta saki jikinta dau ta zamo ‘yar gida, yau kwananta takwas kenan amma idan ka ganta sai ai tsammanin ta shekara damu. “Ai Allah ba azzalumin bawa ba ne, kunga da yake ‘Yar mowa sunyi nufin cutarwa ne ga ‘Yar bora sai gashi zuwa nemo ruwan bagaja ya zame mata silar arziqinta.” Baba ce ta yi wannan qarin bayanin bayan mun fahimci ta kammala tatsuniyar. "Qwarai kuwa.” muka amsa gaba daya. “Amma ‘Yar bora tasha wahala, ta bala’in bani tausayi duk da dai tatsuniya ce.” Nice na fadi haka ina dan lumshe idanu. “Wallahi nima na tausaya mata, har qwalla na kusa yi lokacin da akace dole sai ta nemo rafin ruwan bagaja sannan zata wanke kayan fitsarin ‘Yar mowa.” Fatima ce ta fadi haka cikin jimami. “Ai abinda zai fara qarewa a jikin Fatima shine hawaye, duk ranar da kikai sakaci hawayenki ya qare babu wanda zai sammiki na shi.” Rahma ce ta fadi hakan ga Fatima cikin salon tsokana, gaba dayan mu dariya muka tuntsire da ita muna kallon Fatima da ta yi rau-rau da ido tana niyyar kuka. “Wa ya fada miki hawaye yana qarewa? kiyi ta kukan ki idan abin kuka ya samu kinji Fatima? idan hawayen ya qare zan sammiki nawa.” Baba jummala ce ta fadi haka tana bubbuga bayan Fatima cikin salon rarrashi. “Zancan gaskiya ya kamata ki koyi jarumta Fati, ba ko wani qaramin abu ake zubar mishi da hawaye ba, ni kam a rayuwata zan iya qirga miki yawan kukan da nayi" Na fadi haka ina kallonta cikin qara tabbatar mata da abinda na fada har zuciyata. “Ai ke ta daban ce Aysha, ni kaina zama dake yasa na zama jaruma, don haka karku damu da Fati, matuqar tana tare damu zata zama jaruma.” Safiyya ce ta fadi hakan tana kallon kowa daya bayan daya. “Yau dai ya kamata a zaga gari da Fatima, tunda ta shigo gidan nan ko qofar gida bata leqa ba….” “Wa ni…?" Da sauri ta katseni tana zazzare ido. "Eh! ke mana, ko akwai wata Fatima bayan ke a gidan nan?” “Amma dai tsokana ta ki ke yi ko? Kin manta yanda aka baza ‘Yan sandan ciki da waje don gano inda na shiga? Ni kam idan kin ganni a waje to na shekara cur a 6oye" “Lallai ke matsoraciya ce.” Sadiya ta fadi hakan da mamaki a fuska da muryarta. “Eh! din, na yarda da ni matsoraciya ce.” Ta amsa da murmushin karfin hali, sannan ta daga hannunta biyu alamun sallamawa. “Shikenan amma ina tabbatar miki ko kin fita yau babu abinda zai sameki, kin riga kin ku6uta daga hannun ‘Yan sanda da duk wani mai nemanki har abada.” Daga haka ban qara cewa komai ba na janyo wayata don duba saqon daya shigo minti talatin da suka wuce. “Amincin Allah ya tabbata a gareki sarauniyar kyawawan ‘Yan mata. Da farko dai ina hadaki da girman Allah ki amshi tubana akan sa6anin da muka samu a kwanakin baya, sa’annan ina qara hada ki da girman Allah ki amshi gayyata ta zuwa Birth Day din haihuwa ta daya zagayo a gobe, zan gabatar da ‘yar qwarya qwaryar liyafa ne da wasu manyan qawayena suka shirya min a Shehu Usman Katsina House a gobe, don darajar manzon Allah S.A.W kada ki qi zuwa taron, don karki qi daukan wayata yasa na turo miki saqo. Hajiya Danasha ce" Shiru na yi na tsawon mintuna biyar ina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27