Chapter 19
Chapter 19
nake ji, hankalinsu ya yi mummunar tashi, a qarshe dai babu yanda suka iya dole a wannan dare suka kawo min maganin mayen dana saba sha a lokacin Mahfuz. Suka tasani a gaba suna kuka da idanunsu ya yin da ni kuma na bingire a gado ina barci, bayan na kwankwadi kayan maye na bugu. “INA LABARIN MAHFUZ?” A ranar da abin ya faru a qofar gidansu aka tsince shi a sume bayan al’ummar gidan sun fito sallar asubahi, abinda ya sanyayar musu da jiki kuma ya basu tsoro shi ne yanda suka ganshi tsirara haihuwar uwarshi kuma wasu sassa daga jikinsa na fitar da jini. Hankali tashe suka yi asibiti dashi, tsawon kwanaki uku bai dawo hayyacinsa ba a ranar da ya cika kwana hudu a asibitin ya ce ga garin ku nan! A Wannan lokacin mahaifina ya dauki tsawon lokaci bai dawo gida ba, don saida ya yi kwanaki goma sha biyar bai dawo ba, ni kam a gare ni tafi nono fari domin duk tsawon wannan lokacin muna tare dasu Anty Hassana. A wannan tafiyar da mahaifina yayi ne ya gane asalin sana’ar ubangidansa Alh. Buba. Tun a safiyar ranar Anty Hussaina take sanar min yau zasu tafi gida, domin mahaifina yau zai dawo.... Tun kafin ta aje numfashin maganarta na rushe da kuka mai tsananin qarfi ina fadin ni dai zan bisu, duk inda zasu tafi sai na bi su. Anty Hassana ce ta janyoni jikinta tana rarrashi tare da mini alqawarin ko sati daya ba zasu dauka ba zasu dawo gareni, da haka ta yi nasarar shawo kaina na daina kukan da nake yi. Ban san lokacin da suka tafi ba ina shiga bandaki da niyyar dauro alwalar sallar la’asar na fito na tarar basa nan. Abin da ya bani mamaki shi ne ganin komai na dakin sun mai dashi kamar yanda yake a da kafin mahaifina yayi tafiya, babu yanda za a yi ka yi tunanin na zauna da baqi a dakin har tsawon kwanaki goma sha biyar. “Tandijan! A gaida su Anty Hassana, a cikin lokacin da bai wuce minti biyu ba har sun komar da fasalin dakin kamar yanda yake a da...?” Na fadi hakan ina rike da ha6a, alamun mamaki, ban zurfafa tunani ba na tada sallar azahar bayan na dora jallabiya a kan riga da wandon da yake jikina. Ina sallar na ji dawowar mahaifina, abin da ya bani tsoro shine, yanda qirjina ya buga dam! zuciyata ta cika da matsanancin tsoro...addu’ar tsari daga dukkan sharri na yi bayan na idar da sallah na zabga tagumi hannu bibbiyu. Surutun da nake jiyowa ya tabbatar min ba mahaifina kadai bane ya shigo gidan, qara la6ewa nayi a kan dadduma jikina a sanyaye tsoro yana ci gaba da mamaye dukkan sassan jikina. Murda hannun kofar dakin tare da kutso kai ba tare da an yi sallama ba yasa na dago kai a hanzarce don ganin mai shigowa, mahaifina ne, a hannayensa duk biyu riqe da manyan ledoji masu dauke da tambarin “Mr Bigs” mamaki ne fal zuciyata bayan ya ajiye ledojin a gabana yana fadin “Bisimilla, ki ci abinci sai ki fito falo ki gaisa da baqi.” Yana gama fadin haka ya juya da nufin ficewa daga dakin ni kuma na bi bayansa da kallo. “Da alamar wasu mahaukatan kudi ya samu..” Na fadi hakan a fili bayan na daina jiyo qarar sabuwar shaddar da yake sanye da ita, tsoro da mamaki yasa ko bude ledojin na kasa yi, minti biyar tsakanin fitarshi daga dakina na gyara zaman hijabin jikina na nufi falo don gaisawa da baqinsa kamar yanda ya umarce ni. “Ko kai fa Alh. Sa’ad? Yanzu za ka shiga duniya a dama da kai cikin manyan mutane, za ka murza naira duk yanda kaso, mota sai irin wacce kake so za ka hau, mata sai wacce ta kwanta maka a rai zaka biya buqatarka da ita, gida sai irin wanda kake sha’awa zaka zauna a ciki. Kai dai kaiwa ka ci gaba da ba Oga Alh. Buba hadin kai...” Maganaganun da kunnena suka juyo min kenan sannan nayi sallama a qaro na hudu tare da kutsa kaina a cikin falon. Su hudu ne a cikin falon duk da mahaifina, daga suturun da suke sanye a jikin ko wannensu za a gane naira ta zauna da gindinta, dukkansu manyan mutane ne. “Ina yinin ku?” Na fada bayan na dan durqusa a jikin kushin din dake girke a qofar shiga falon. “Tabdijan! Yanzu Alh. Wannan ‘yarka ce?” Duk suka hada baki gurin fadin haka suna kallonshi baki bude, ba tare da sun amsa gaisuwar da na yi musu ba. Dariya mahaifina ya saka ba kakkautawa kamar ba zai daina ba, can ya tsagaita tare da fadin “Qwarai kuwa. Kuna mamaki ne?" “Ai dole muyi mamaki, amma ko kadan ba ta yi kama da kai ba, ko dai mahaifiyarta irin baqaqen larabawan nan ne?” “A’a, ai ta ninka mahaifiyarta magirgayiya kyau da diri sosai ma, kamar aljana Aysha take don kyau tun tana jaririya...” “Alh. Zan iya tafiya?” Na katse maganganun da suke yi ina kallon mahaifina zuciyata cike da tsanarsa shi da abokansa. “Je ki, amma ki shirya kuma ki sanya kayan ki a cikin babban jaka zamu yi tafiya.” Ban qara kallon fuskar daya daga cikinsu ba na fice daga falon, a zuciyata ina fadin babu inda zan je. “Yanzu kana da wannan kadarar kake ajiye da ita a gida? Ai yanzu zamani ya canza, kudi sun zarce komai a wannan rayuwar da muke ciki...” “Na sani Alh. Musa.” Na jiyo muryar mahaifina ya katse mai magana don haka na ja na tsaya in ji mai zai ce? “A duk iya tsawon shekarun dana dauka ina aiki a qarqashin oga bai taba haskamin irin sana’ar da yake yi ba. Wai shi a tunaninsa ba zan iya irin wannan harkar ba. Shi yasa a karon farko na fara da ‘yar gidana. Domin kowa ya san ba da wasa nake yi ba. Ina son kudi a rayuwata, tsawon shekara ashirin da biyar rabona da mahaifata duk saboda son kudi. Don haka babu abin da ba zan iya aikatawa ba matuqar zan sami masoyan raina.” Gaba dayansu suka barke da wata mahaukaciyar dariya wanda yasa falon amsa kuwwar dariyar tasu, da sauri na qarasa dakina ina jujjuya maganganun mahaifina a zuciya ta. “Me yake nufi da ya fara da ‘yar gidansa? An ya ba wani mugun abu yake qullamin ba? Wacce irin unguwa zamu je da har yake fadin in zuba kayana a jaka?” Wadannan kadanne daga irin tambayoyin da suka ringa amsa kuwwa a zuciya ta da kwakwalwa ta... farar takardar dana gani a ajiye a gefen gadona ya katse min duk wani tunani da nake yi. Da mamaki na dauki fallan takardar ina jujjuyata a hannuna, tabbas dazu babu ita a dakin “To wa ya kawo ta?” Na tambayi kaina, bayan dawowa ta daga bandaki daura alwalar sallar azahar na tarar su Anty Hassana sun tafi sai da na kalli dakin gabas da yamma kudu da arewa amma ban ga wannan fallan takarda ba. Gani ya kori ji... don haka na warware takardar don ganin abin da ta qunsa... “Ki bi umarnin mahaifinki, Allah ba zai bashi ikon cutar dake ba, duk
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27