Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wani abu aka feso min irin wanda mahaifina ya fesa min, sai gani a wani daki na daban, sabanin wanda nake ciki a da. Shima wannan dakin mai duhu ne amma ba kamar wancan ba, akwai dan wadatar haske kadan, sabanin wancan da ko tafin hannuna ba na gani. Yini uku aka sake dauka wannan mutumin yana shigowa don aikata tsafi irin na wancan dakin, amma tarihi ke maimaita kansa. Sai da aka canja min dakuna har guda bakwai abinda ya faru a dakin farko shi yake faruwa a kowane daki, Kuma duk dakin da aka canja min sai na taka qwarangwa din kan mutum da qafata ta dama, bayan ihu da girgiza ya cika dakin komai zai koma daidai, sannan wannan haske yake bacewa. Tun da na take wannan kai na bakwai na tsinci kaina a wani irin yanayi tamkar ba ni ba, ina gurin amma kamar ba ni a gurin, umarni kawai ake ba ni daga zuciyata ni kuma ina aikatawa ba tare da ko zurfafa tunani ba. Ina zaune guri daya zuciyata ta yi min umarnin in tashi in nufi yamma na dakin, cikin duhun nasa kai a inda zuciyata ta tabbatar min nan ne yamma. Bangon da ya tare ni ya tabbatar min na isa jikin bango. Zuciyata ta ba ni umarnin in yi bismillah sau uku, in shafi bangon dakin, Ina aikata hakan qofa ta bude, a wani babban falon mai wadataccen haske na tsinci kaina, Falon ya hadu iya haduwa. Domin kuwa an zuba komai na jin dadin rayuwar duniya. Tun daga kan kujera da labulaye da kafet (capet) din komai koraye ne, amma suna da haske. Tsawon minti biyar ina kalle-kalle amma ban ta6a komai na cikin falon ba ina tsaye a inda nake. Yamma na sake nufa kamar yadda zuciyata ta umarce ni, ina isa na yaye labulen da ya tare jikin bango, kofa ce mai tsananin kyau da daukar ido ta bayyana a gurin, hannun dama na sanya na bude qofar tare da fadin “Bismillahir rahmanir rahim.” A wani daki na bayyana mai cike da abubuwan ban tsoro da firgitarwa, wasu manyan qorai ne guda biyar, girke a jikin bangon kowane kusurwa na dakin, cikin manyan qoren cike suke da wani irin ruwa jajir mai hade da baki-baki (jini)abinda aka fada min kenan da na yi tunanin ruwa ne a cikin qoran. Qwan lantarki qwaya daya ne tal a tsakiyar wannan dakin, kuma haske mai kama da jini yake bayarwa. Motsi da wani irin gurnani daya ringa fita daga tsakiyar dakin shi ne abinda zai fi tsorata duk wanda yake cikin dakin, wani abun mamaki shine zuciyata a tsaye take, babu tsoro ko kadan a cikinta. Yamma na dakin na sake nufa, kamar yadda zuciyata ta umarce ni. Ina isa jikin wannan qore masu dauke da jini na ja na tsaya. “Rufe idanunki.” Aka fadamin haka a kunne na. Ban 6ata lokaci ba na aikata abinda aka umarce ni. Minti uku tsakani aka umarce ni da in bude. Ina budewa na tsinci kaina a wani daki na daban mai dauke da wata qatuwar tukunya a tsakiyar dakin. Babu abinda ke fita a kowace kusurwa na dakin sai turiri mai matuqar zafi. Sakwan goma na hada zufa na yi sharkaf amma duk da haka ban fasa tafiya zuwa yamma na dakin ba. Abin mamaki shine ina tafiya amma tamkar ba na yi, domin ga bangon yamma na dakin ina gani a can nesa da ni amma na kasa isa gare shi. Hakan ya fahimtar da ni a guri daya nake bayan kuma tafiya nake yi. Wata mahaukaciya dariya da ta cika dakin ita tasa na ja na tsaya cak, ba tare da na shiryawa hakan ba. Tukunyar na zurawa ido don kuwa ta cikinta dariyar ke fitowa.... tsawon minti biyar ana 6a66aka dariyar sannan muryar ta dauke tamkar daukewar ruwan dama. “Ci gaba da tafiya.” Zuciyata ta umarce ni, ina daga qafata ta dama don zuwa gaba naja na tsaya cak! Wasu qananan halittu masu kama da kwadi su suka yi ta 6ullowa daga jikin kowane kusurwa na dakin, kuma kai tsaye ni suka nufo suna kukan kwadi suna feso min wani abu mai kama da dafin maciji. “Rufe idanunki.” Aka fadamin haka cikin tsawa a kunne na, da sauri na runtse ido kam, Tsawon mintina talatin aka ba ni umarnin budewa, ina bude ido na tsinki kaina a tsakiyar daji mai yalwar bishiyoyi da ganyayyaki. Inda na tsinki kaina jikin wata qatuwar bishiya ce wacce yawan ganye da rassanta ya sa sai a can nesa nake hango rana. Amma harabar bishiyar inuwa ce da wata iske mai dad'i take kad'awa. Umarnin zama aka ba ni daga cikin kunne na, don haka na zauna ina maida numfashi tare da lumshe idanu. Sai kuma na fara tunain rikitattun al’amuran da suke ta faruwa a rayuwata. Tsayin mintuna talatin ina a haka, wani abinda zai baku mamaki shine, sam bana jin yunwa, ba na jin qishirwa, kuma bana jin barci duk iya tsawon wadnnan kwanaki da na dauka. Da na fahimci na tsira daga sharrin matsafan sai na fara tunanim yadda zanyi in rama sallolin da suke kaina. Abin baqin ciki ma shine, ban san ko iya kwanaki nawa na dauka a gidan wannan matsafi ba, balle in san yawan sallolin da ake bi na bashi. A hankali na bude idanu ina kallon kayan jikina. T.shirt ce da siket din jeans a jikina, sai hula mai dauke da tambarin “AZZAHARA’U” a kaina. Lumshe idanu na sake yi ina tunanin yadda zan yi in samu ruwan alwala da doguwar riga da hijabi da sallaya don sauke faralin dake kaina. Daga can nesa da ni na ringa juyo surutai sama-sama, don haka na kasa kunnena ba tare da na tashi daga inda nake zaune ba, Surutan kamar ni suke nufowa don tun ina juyo su daga dan nesa na fara jin su a kusa da ni. “Kamar muryar su Aunty Hassana?” Na fada a zuciyata hade da bude idanuna da suke lumshe. Yalwataccen murmushi ne ya wadaci fuskata don ganin su Aunty Hassana ne, a hannayensu duk biyu janye suke da wasu manyan jakunkuna masu matuqar kyau da daukar ido, da gudu na karasa gare su na rungume su ina murna. Sai a wannan lokacin wasu zafafan hawaye suka ziyarci idanuna, rauni da tsoro suka cika zuciyata, don haka na 6arke da kuka mai hade da shessheqa. Basu katse ni ba sai kama hannaye na da suka yi muka zauna a harabar wannan bishiya da nake zaune tun kafin isowarsu, ganin ba ni da niyyar tsayawa da kukan nawa ya sa Aunty Hassana fadin “Ko ba ki yi murna da ganin mu ba ne mu koma inda muka fito?” Hannu nasa na rufe mata baki tare da qoqarin rage sautin kukana har daga qarshe na samu nasarar tsaida hawayen gaba daya. Labari na ringa ba su na abubuwan da suka faru da ni a bayan tafiyarsu, abinda ya ba ni mamaki da al’ajabi shi ne yadda sam ba su yi wani mamaki ba da abinda Abbana ya aikata agareni, har daga qarshe na buge da tambayarsu cewa “Naga ko damuwa da abinda ya aikata a gareni ba kuyi ba, shin ku bakuji mamaki bane?” Anty Hussaina

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});