Chapter 11
Chapter 11
da duk wani kayan alatu da siturun da muke sakawa mallakin Aysa ne, yanda kika ga gidan nan mu ma haka muka tarar da shi.” “Tabxijan!” abin da Fatima ta iya furtawa kenan sannan ta zabga uban tagumi da hannu biyu. *** Qarfe biyar da minti ashirin da bakwai muka yi parking din motocinmu a qofar ‘MANGAL PLAZA’ Siyama, Rahama, Safiyya mota daya suka hau, Sadiya, Suhaila, Nafisa suka hau mota daya. Farar mota kirar marsandi na hau, kamar yanda duk kayan jikina farare ne, wandon jeans ne wanda ya dan kamani daga sama ta kasan kuma sayya bude, T. shirt din dana saka ita ma fara ce an rubuta ‘Baby’ da golden colour a gaban rigar, ban sanya hula ba illa wani farin qyalle dan siriri dana daura a saman kaina zuwa qeyata na fitar da gashin kaina mai matuqar kyau da tsawo ya bazu har saman kafadata, a saman qyallen dana daura an rubuta ‘Azzahara’u’ da qananan rubutu ruwan golden ta gaban goshi. "kin yi kyau matuqa….. amma a hakan za ki fia?” abin da Fatima ta ce min kenan lokacin da muke gab da fitowa daga gida. Murmushi kawai na yi mata kamar yanda yanzu ma nake murmusawa bayan na tuno abin da ta ce min, ni ce a gaba sauran ‘yan matan suka rufa min baya, muka nufi cikin qaton kantin. Tun kafin ya daidaita fakin din motarshi a harabar gurin yaga fitowarta daga cikin motar, “Tabbas ita ce” ya fadi hakan a zuciyarshi, kwanaki biyar kenan ya taba haduwa da ita da sauran ‘yan uwanta a ‘check point’, a lokacin ba a mota ya gansu ba, a kan mashina ‘wayyo kudi na’ ne sun goya junansu, abin da ya baiwa duk mutanen gurin mamaki shine, a dokar da yayi tsanani a garin Kaduna shi ne matuqar kana kan mashin idan ka je check point sai dai ka sauka ka tura mashin din har ka wuce sojoji, sannan ka hau ka cigaba da tafiya, Sukam kansu tsaye suke ratsa tsakanin motocin, a lokacin yana can tsallaken titi a tashi motar yana jiran layi ya zo kanshi, Har sun sa kai zasu wuce sojojin biyu suka dakatar dasu a fusace. A lokacin bai yi tsammanin mata bane don sun sanya hular kwano duk sun rufe fuskokinsu, dakatar dasu din da aka yi ya sanya wacce take gaba ta sanya hannu ta sabule hular kwanon da yake kanta, sai su ma sauran mahaya mashin din wanda suke biye da ita suka fara sabule hulunan kwanon da suke sanye a kawunansu. Kanannadadden gashin kai mai matuqar kyau da sheqi da tsawo shi ya fara bayyana daga bisani kyakkyawar fuskarta ta biyo baya, idanunta a lumshe tsawon daqiqa goma sannan ta bude su tana kallon sojojin bayan ta qawata fuskarta da murmushi, da hannunta daya ya ga ta yi musu alamar ya aka yi? bakinta yana motsi a hankali, ya ga alamar ta qara furta wata kalmar amma bai fahimci abinda tace ba. Nan take ya ga sojojin sun yi musu umarnin wucewa ba tare da wani daukar mataki ba, harda karin Sara mata, sannan suka bi ta kallo ido da hanci bude. Wannan abinda ya faru yaba duk wani wanda ya ke tsaye a gurin matuqar mamaki, A lokacin ya yi tunanin ita din ‘yar gidan wani babban kusa ne a garin Kaduna, tun ranar fuskarta ya qi bacewa daga idanunsa… “Abdul-Ahad tunanin me kake yi?” Yasmin da take zaune a gefenshi ta tambayeshi fuskarta ba walwala ko kadan, bayan ta lura da kallon da ya bi ‘yan matan da suka shige cikin kantin da shi. Murmushi ya jefeta da shi don kwantar da hankalinta daga bisani ya yi qarfin halin fadin “Babu komai, kaina ne yake dan sara min.” Kallon rashin yarda ta bi shi da shi na tsawon daqiqu sannan ta ce, “Kar dai ka manta watanni shida nan gaba za a daura mana aure, kuma zan iya yin komai ciki kuwa har da kisa ga duk yarinyar da ta nemi rabani da kai, ko da kuwa kai ne ka ce kana sonta.” Tana gama fadin haka ta bude qofar mota ta fita ta jingina da motar tana jiran fitowarshi. Share gumin goshinshi yayi sannan ya gyara zaman tabaran da yake sanye a idanunsa ya fito daga motar jikinsa ya yi matuqar sanyi, kai tsaye kantin da ‘yan matan suka shiga ta ja hannunsa suka nufi ciki. *** Tun daga nesa rigar take daukar hankalina, don haka na qarasa da nufin in dauko ta duk da dai kalar yellow bai cika burgeni ba, dora hannuna akan rigar ke da wuya na ga wani hannu ya riqe rigar, daga faratan kantin masu matuqar tsawo da suke sanye a kunbunan hannun na gane mace ce, sakin rigar nayi na kara gaba ba tare ko fuskarta na kalla ba. Sai da ta yi qwafa saboda takaici, ta so a ce na tanka mata ta yi min wulaqanci a gaban Abdul don ya tabbar ba cika baki take a kanshi ba, za ta iya aikata duk abinda ta ce za ta aikata a kan soyayyarshi. Don haka ba ta haqura ba ta ci gaba da bin duk inda na nufa. Hantar cikinshi sai da ta kada saboda tsabar tsorata, lokacin da ya yi arba da hannun Yasmin damqe da rigar da na fara dauka, a zatonshi zan tanka mata, amma wani abin armashi da birgewa a tattare da ni shine kallon ta ban yi ba na sakar mata rigar na yi wucewa ta. Ganin ta nufi hanyar da na bi ya sa ya fara addu’ar Allah ya sa ba abinda zai faru har sai sun gama abinda ya kawo su su fice, don ya san Yasmin tamkar yunwar cikinshi, fitinanniya ce ta gaban kwatance. Yanayin tsarin kwalin turaren shi ya fara daukar hankalina, na dauka ina karanta sunanshi, kamar da fada aka fisge kwalin turaren a hannuna… da matuqar mamaki na bi hannun da kallo sai na gane hannun dazu ne. Raina ne ya fara baci, amma nayi kokarin hadiye bacin ran, ban kula ba na kada kai da nufin wucewa gaba, tsulum na ga hannun nata a cikin kwandon diban kayan siyayyar da na yi, wanda yaron kantin yake biye da ni yana tura wa ina jefa duk abinda na dauka a ciki, wata doguwar riga puple ta dauko a cikin kwandon siyayyata, ta juya da nufin sakawa a nata kwandon. Da matukar mamaki na bita da kallo, fuskantar abinda take shirin yi yasa na dafa Kafadarta na damqe na juyo da ita muka fuskanci juna, dayan hannuna nasa na damqe hannunta mai riqe da rigar, tun daga qafafuwanta na fara bin ta da kallo har zuwa fuskarta, tasha bilicin, kallo daya na yi mata na gane farinta ba na Allah da Annabi ba ne, a tsaye take single, ba laifi tana da dan kyau a fuska, amma da ta tsaya a baqin da Allah ya yi da ta fi haka kyau, tana sanye da riga da siket na English wears. Fuskata ba walwala nake kallon yadda take kici-kicin qwace hannunta da na damqe, ganin ta kasa qwacewa ya sa ya tsaya cak tana kallo na, tana sauke numfashi sama-sama, daga bisani ta watso min harara, sannan tace “Sakar min
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27