Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

har gaban abada idan akwai. Bayan komai ya lafa riqon ta ya koma hannun qanin mahaifinta ya zama mahaifin ta kuma mahaifin dukiyar ta. Babu wata rayuwa ta jin daxi da Fati za ta karar wanda tayi a gidan qanin mahaifin nata. makarantar gwamnati ya sanya ta savanin ‘ya’yan shi da suke makarantar kuxi, duk waxanda ya kamata su tsawatar mishi ya gama siyesu daman kuma mahaifansu (Kakan nin Fatima na wajen Uba tun ta na ‘yar jaririya suka rasu) Da daxi ba daxi har ta kammala Secondary School inda ta fito da sakamako mai matuqar kyau, babban burinta ta ci gaba da karatu amma sam Alhaji Musa yaqi bata damar hakan, amma ‘ya’yan shi da mazan da matan duk babu wanda yake karatu a qasar nan. Alhaji Muhammad aminin kawunta ne don duk wani qulle qulle na kawun nata Alhaji Muhammad ya sani, tun tana aji uku a Secondary School yake damunta da maganar soyayya, nauyin shi ta ke ji sosai dan ta xauke shiu tamkar qanin mahaifinta, batare da saurarar amincewa ko ra’ayinta ba. Alhaji Musa ya xaura mata aure da Alhaji Muhammad. Hannu bibbyu tasa ta rungume shi duk da ba ta son shi ko kaxan, gidanta da ban da na uwar gidan shi kuma uwar yaranshi, ya na nuna mata kulawa dai – dai gwargwado saboda ya na sonta, kuma tana daga cikin jerin matan Allah ya kyautata surar jikin su, da na fuskar su. qarin armashin kuma shi ne yarinya ce qarama dan ita sa’ar xan autan shi ce, ita da Hajiya Kumatu uwar gidan shi suna zaman amana dan kuwa ba ko da yaushe suke ganin juna ba. Idan bada wani qwaqwqwaran dalili ba sukan dauki tsawon lokaci ba su haxu ba. Ba su fara samun matsala ba sai da Xan Alhajin mai suna Nasir ya dawo gida daga inda ya ke karatu acan qasar Malesia, tunda suka je air port da niyyar xauko shi ita da Alhaji da Hajiya ta lura da irin kallon da yake binta da shi, Nasir bunsuru ne gurin bin mata tun kafin ya tafi karatu qasar Malesia da ya je can kuma sai idonshi ya qara buxewa duk yarinyar da ya qyalla ido a kanta sai ya bi duk hanyar da yasan zai samu biyan buqatar shi. Tun yana can ya ji labarin Dadyn shi ya yi aure amma bai tava tunanin daqwalwa irin wannan ya aura ba, ganin farko da ya yi mata gabanshi ya yanke ya faxi daqyar yayi qarfin halin daidaita nutsuwarshi don karya bada kanshi a gaban iyayan shi. Suna tafe a mota zuciyar shi tana saqa mishi hanyar da zai bi dan cimma mummunan manufarshi a kanta, a zuciyar ta take ta addu’a Allah ya daidaita zaman su dashi dan sam bata fahimci wane irin kallo yake yi mata ba, a zaton ta kallon tsana ne da tunani yana taya mahaifiyar shi kishi ne, a minti biyar ya mantar da ita wannan tunani ta hanyar fara janta da hira yana kiran ta “Aunty Fati” duk iyayan ransu cike yake da farin cikin dawowar xan nasu dan haka sam hankalin su ba shi a kan Fatima, idan ya tsomata a hirar shi a xarare ta ke amsawa muryarta a sanyaye. Hakan ba qaramin burgeshi yake ba, shauqin sha’awarta yayi ta xibar shi, har su ka isa gida, ba ta bar babban gidanshi ba zuwa gidanta sai bayan magariba gab da isha’I da yake Alhajin a gidan yake da kwana sai ya haxa ta da Driver ya kai ta gida da sauri Nasir ya miqe ya na kallon iyayan shi fuska a sake ya ce, “Ba ri in raka aunty Fati gida sai mu dawo ta re da Drivern” jikinta sanyi qalau ta ke kallon shi don rashin ga ne manufar wannan cusa kai da ya ke mata. Izinin tafiyar daya samu daga gurinsu ya hanata tankwavar da shisshigin shi , sai ta qara yi musu sallama ta nufi harabar gidan. Dukkansu suna zaune a bayan motar ba mai cewa wani uffan, amma idon shi ya na kanta tamkar zai cinyeta xanye, ba qaramin takurata yayi da idanun shi ba don haka ta takure acan jikin motar, a zuciyarta ta ke addu’ar Allah yasa su isa gidanta lafiya ko zata samu sa’ida da ga mayataccen kallon da yake bin ta da shi. Suna isa ta dakatar da Driven a qofar gida, ta valle murfin motar ta fita sannan ta leqa kanta ta saqon glashi ta ce, “Nasir Allah ya huta gajiyan tafiya mu kwana lafiya” ta qarasa da sauri ta ciro key a jaka ta na buxe get xin gidan ba taga fitowar shi daga mota ba balle lokacin da ya nufota kawai muryarshi ta ji a kusa da ita ya na faxin “Haba aunty na rowar ruwan gidan ki za ki yimin?” a firgice ta sa ki key xin ya faxi qasa muryar ta na rawa ta ce, “Ba… ba… ba haka ba ne, na… naga su Alhaji suna can suna jiranka ne.” bai ce komai ba ya ya tsuguna ya xauki makullin ya buxe get xin ya shige ciki ya bar ta nan a tsaye. Ganin da ta yi ba sarki sai Allah ga idanun Driver tun xazu ya na kanta ya sa ta yi shahadar bin bayan shi, har ya samu nasarar buxe qofar falonta ya shige ciki don haka ta haxa da sassarfa zuwa cikin falon. Yana kwance akan kujera mazaunin mutum uku idanun shi alumshe, jakarta ta aje akan kushin ta nufi kiching ta jero mishi lemuka da ruwa ma su matuqar sanyi a cikin faranti ta xora Cofi guda biyu ta kawo mishi. A zaune ta tarar da shi hannun shi riqe da remot xin T.V ya na canza tashoshi, a gefe xaya ta aje ta xauko xan qaramin table ta xora sannan ta kalle shi ta saki fuskarta ta ce “Bisimillah.” Maqe ka faxar shi ya yi tamkar wani qaramin yaro sannan ya fara kashe ma ta ido irinna gogaggun ‘yan duniya. Muryar ta da mamaki ta ce “Me ya sa? Bayan ruwa ka buqaci sha” “Ni ba irin wannan ruwan nake so ba” Ya faxa yana tura baki, ya fara kwarkwance mata tunanin ta don kuwa ya girme mata nesa ba ku sa ba, a qalla zai girmeta da shekaru goma sha huxu, wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi. Sam bata fahimci inda ya dosa ba don haka ta ce, “dare yana qara yi fa kar su Hajiya su ji shirun ya yi yawa" “Bikin Magaji ya na hana na Magajiya ne?" ya jefa mata tambayar yana qara qura mata ido. Kallo kawai ta bishi dashi ba tareda ta amsa mishi ba. Tashi ya yi ya matso dab da ita sannan ya ce, “Gaskiya Fatima bazan voye miki ba sam baki dace da irin su Dady ba, da irin mu ki ka dace, kina da kyau matuqa, kina da dirin da duk wata qasaitacciyar mace za ta so ta mallaki irinshi, ganin farko da nai miki sha’awarki ta mamaye zuciya ta “Ina sonki” zanso ace kin rabu da mahaifina ki dawo gareni, idan kuma hakan bazai samu ba to gaskiya sai dai mu raba shi daidai da Daddy, don wallahi tunda na xora

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});