Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na ajr tocilan hannuna a jikin wani dan itaciya yana haska gidan yarin yanda duk wanda ya biyo ta bayan gidan zai iya hango hasken. Daya ne ya fara qarasowa kafin ya ankara na lallaba ta bayan shi na buga masa kan bindiga a kunnenshi, shu…. Ya tafi zuwa qasa idanunshi suna rufewa suna budewa saboda azaba. Kafin ya dawo hayyacinshi na shaqa mishi wata farar hoda wanda na karba a hannun Sadiya, daga can nesa na ji alamar tahowar daya mai gadin don haka na sulale na kwanta a cikin ganyayyaki. Idanunshi da tocilan hannunshi can nesa suke haskawa don bayyi tsammanin wani zai kwanta a gurin ba, qafata na sanya na tade shi ya hantsila can gefe bindigar hannunshi ma tayi can gefe daya, kafin yayi yunqurin tashi na sanya qafata na buga mishi naushi a ciki, runtse ido yayi saboda tsananin zafi kafin ya bude na shaqa mishi hodar hannuna. Tocilan na dauka na haska fuskar mai gadin da ya fara isowa gurin barci yake hankali kwance, amma wanda bai sani ba sai ya yi tsammanin mutuwa ya yi, ban saurari dayan ba don nasan shima yanzu barcin zai dauke shi, na qara matsawa jikin gidan yarin kadan, harbi na fara sakewa ina bada tazarar minti biyu tsakani sai da nai harbi hudu, qarar harbe-harben shi ya gigita hankalin jami’an tsaron da suke cikin gidan don sun tabbatar ba lafiya ba, duk tsammaninsu ya tafi kan cewa ‘yan fashi ne suka biyo wani da yake neman tserewa har kusa da gidan yarin, don hakan ya sha faruwa basau daya ba ba sau biyu ba. Jin da sukayi harbin yakika qarewa ya sa suka fito da gudu dukkansu don ganin me yake faruwa. Su Rahma suma suna kwance a cikin ganyayyaki kamar yadda muka tsara, kafin jami’an tsaron su ankara aka ringa zarge qafafunsu da igiya ba tare da suna ganin masu musu wannan daurin talalar ba. Sun samu nasarar zarge qafafun mutum tara, yayin da mutum shidda suka ankara da abinda yake faruwa. Kin qarasawa gurin suka yi don gudun afkawa tarkon da sauran ‘yan’uwansu suka afka, Daga nesa suke haska gurin da tocilan hannunsu amma ba su ga komai ba sai ‘yan uwansu a kwance. Ga makamansu duk sun faxa gefe guda, a tsorace suka cigaba da haskawa suna harbe-harbe a iska. Ta jikin katangar nake leqan abinda yake faruwa, ganin suna bata mana lokaci yasa na yi bismillah na saita qafafun mutum biyu daga cikinsu na harbe su a qafa da bindigogin da sike riqe a hannuna dama da hagu. Nayi nasarar samun su, hakan ne ya ankarar da sauran mutum hudun daga inda harbin ya fito, wani ragon azanci da suka yi sai dukkansu suka biyo bangaren katangar da nake cikin sanda suna haska tocila, su Rahma ne suka miqe da hanzari suka dauki bindigogin ‘yansandan da suke kwance suna kici-kicin kwance qafafunsu suka harbi ‘yan sandan a qafafunsu ba tare da sun ankara ba. Da sauri duk muka bi su muka shaqa musu hodar da take hannun Sadiya minti biyu tsakani nannauyan barci ya yi awon gaba da su. Mu kuma muka shiga cikin gidan hankali kwance. Don muna da tabbacin ba za su farka ba sai sun xauki tsawon awa goma sha biyu suna barci. Mabudi ne da yake bude kowane irin kwado mukayi amfani dashi gurin bude dakin da take ciki, don haka ba mu sha wahalar bude dakin ba, suna tsaye cirko-cirko tamkar kajin da suke fada Sun tsaya maida numfashi. Ganin shigowarmu ya sa suka nufo mu suna zazzaro ido. Kallon sakan biyar ya ratsa tsakaninmu, da alamun mamakin yadda muka shigo cikin gidan har muka bude dakin da suke ciki, ba tare da mun fuskanci matsala daga masu gadin gidan ba suke yi,mu kuma kallonsu muke don tanrance wace ce Fatima a cikinsu? Can kusurwar dakin na hangi wata ta takura kanta a tsakanin cinyoyinta. Da hanzari na nufi gurinta don jikina na ba ni tabbacin ita ce Fatima. Hannu na sa na dafa kafadarta bayan na durqusa kusa da ita. Da sauri ta dago kanta a dan firgice take kallo na sannan ta maida dubanta zuwa ga su Safiyya. “Wace ce ke? Ku su waye?" Ta tambayi hakan bakinta na rasa, idanunta a warwaje, wadanda suka kumbura kuma suka rine zuwa jajaye, saboda tsabar kuka. “Mu ‘yan’uwanki ne, kuma mun zo mu tafi da ke ne.” Na fada mata hakan da tattausar murya don in kwantar mata da hankali. Kallo ta bi ni da shi na rashin yarda da abinda na fada. Dagabisani kuma ta ce “Ban san ku ba, don haka ba zan taba bin ku ba. ku bar ni kawai. Haka Allah ya qaddara zan qarasa rayuwata a gidan yari…” tana gama fadinn haka ta fashe da kuka, sannan ta qara maida kanta tsakanin cinyoyinta, kamar yadda muka tarar da ita da farko. Muna da tabbacin za mu fuskanci tirjiya daga gare ta, don haka ranmu bai vaci ba ko kadan. Da yatsu biyu na kira su Rahma zuwa gare mu, sannan na qara dafa kafadarta a karo na biyu. Hawaye ne wasu na korar wasu tamkar ruwa suke bin kyakkyawar fuskarta. Ban ba ta damar fadin komai ba nace, “Ga wannan tocilan ki haska bayan rigarmu ki ga me aka rubuta.” Na miqa mata tocilan hannuna, sannan duk muka jujjuya bayan rigarmu zuwa gare ta. Tsawon minti uku kafin na jiyo muryarta na faxin, “na amince zan bi ku.” Da matuqar murna na rungume ta, sannan na kama hannunta duk muka nufi hanyar ficewa daga dakin. “Ku taimaka don Allah ku fitar da mu gaba daya.” Muka jiyo muryar wasu daga cikin fursunonin suna fadin haka. “Kofa a bude take ga duk wanda ya yi niyyar fita, amma mu dai ga wacce muka zo dauka nan.” Ina gama fadin haka muka fice da sauri don ganin lokaci yana dad'a qurewa. Karfe uku da minti biyu muka isa gida, Sadiya ce ta dauki dan muqullin qofar get din a cikin mota ta bude mana aka shiga da motar. Baba tana zaune a falo kamar yadda ta saba idan muka fita komai tsawon dare bata kwanciya barci sai ta ga dawowarmu, Yau ma hakan ce ta kasance. Tana zaune da casbaha a hannunta tana lazumi muka shiga cikin falon. Fatima ta nufa kai tsaye bayan ta amsa sallamarmu, da fara’arta ta tarbe ta sannan ta yi mana barka da zuwa. “Abinci kike buqata, ko wanka za ki fara yi ko sallah?” Duk na jera mata wadannan tambayoyin ina kallon ta cikin kulawa. “Wanka da sallah.” Ta amsa muryarta a sanyaye. “Rahma a kai ta dakina a ba ta duk abin da za ta buqata.” Na fadi haka bayan na zube a kujera ina lumshe idanu. Suna wucewa na kalli Baba, “Baba a jera mata abinci a dinning in ya so kowa sai ya je ya kwanta.” “An gama Ranki ya dade.” Ta fad'a da tsokana don ta san na tsani wannan sunan. Murmushi na yi ina kara gyara kwanciya a kan kujera mazaunin mutum uku. “Sannu da aiki ranki ya dad'e, mu kwana lafiya.” Na fad'a wa Baba hakan bayan na lura ta gama jera ma Fati duk abinda za ta buqata. “Kin rama kenan?” ta

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});