Chapter 7
Chapter 7
fad'a tana dariya. Shiru na yi mata ina motsa baki. Ganin haka yasa sum-sum-sum ta wuce zuwa dakinta. Sauran ‘yanmatan ma duk sallama suka yi min. ina amsa musu da kai suka wuce dakinansu. Tsawon minti talatin da biyar ta dauka kafin ta fito zuwa falon tana sanye da jallabiya baqa wacce ta yi matuqar dacewa da farar fatarta. “Kin fito? Barka da fitowa…” na fadi hakan idanuna a rufe. Ban bari tace komai ba na ci gaba da cewa, “Ga abinci can a kan dinning, idan akwai abinda kike buqata ki yi magana.” Na fadi ina mata ishara da inda dinning table din yake. Tun fitowarta ta lura da idanuna a rufe suke, a zatonta barci na ke yi, jin na yi magana ya bata tabbacin idanuna biyu. Isharar da na yi mata ina daga kwance ya daure mata kai, sai ta ja ta tsaya ba tare da ta yi gaba ko baya ba. Tsawon minti biyu tana kallo na, ba tare da ta furta komai ba. “Ki je ki ci abinci mana, dare yana qara yi fa. Idan kuma kin qoshi mu je mu kwanta.” Na fadi duk da haka idanuna suna rufe. Qafafunta har hardewa suke gurin zuwa dining din, don al’amarin ya fara ba ta tsoro. Tsattsakar abincin ta yi ta sha lemo kadan, daga inda take zaune ta furta a ciki. “Na qoshi.” Wanda tana da tabbacin ban ji abinda ta ce ba. “Toh, mu je dakin da kika yi wanka mu kwanta.” Na fada ba tare da na tashi ko na bude idanuna ba. “Na shiga uku ni Fatima!” ta fada a zuciyarta, kuma a tsorace, Allah yasa dai ba gidan Aljanu na Kawo kaina ba" Murmushi nayi, don ganin tana neman sa wa zuciyarta kokwanto a kanmu, yasa nace, "Ba gidan aljanu bane, mutane ne 'yan uwanki" Tsananin tsoro ne ya sake cika mata ciki, hannu biyu tasa ta dafe kirjinta, “Taya aka yi kika san abinda na fada a zuciyata?” Wannan karon sai da na qyalqyale da dariya mai isa ta, sannan na ce “Sanin abinda yake zciyar wani sai Ubangijin da ya halicce mu Fatima, kar ki gurbata imaninki mana.” Na fada mata hakan, amma har lokacin ban bude idona ba. Kallo na take ta rasa abinda za ta furta saboda rudanin da na jefa ta a ciki. Ta buxe baki kenan za ta sake magana na dora dan yatsa manuniya a baki na ce “Shiiii….!!! Kar ki tsananta magana Fatima, ina miki rantsuwa da Alllah mu ba masu cutarwa ba ne gareki, saboda haka ki kwantar da hankalinki karki tsananta magana kan duk wani abinda zaki gani a tare dani. Ki tashi ki shiga ciki ki kwanta nima yanzu zan shigo.” Ina gama fadin haka na juya mata baya idanuna a rufe. Tana son ta qara magana amma bakinta ya kasa furta komai, tamkar an daure mata bakin don haka ta lallaba ta miqe zuwa dakin da ta yi wanka wanda tun farko ta ji na fadi mallakina ne. Minti goma tsakani na bi bayanta, jikina ya bani idonta biyu don haka ban kalli inda ta ke kwance ba, bandaki na shiga na dauro alwala, ina fitowa na dauki doguwar riga ta akan daddumar sallah na koma ban dakin na sanya. duk abinda nake idanunta na kaina har na ta da sallar nafila lokacin agogo ya buga qarfe hudu da rabi na dare, Ina zaune ina lazimi da casbaha a hannuna har aka kira sallar asubah, tashin Fatima na yi a lokacin har barci mai nauyi ya dauke ta. Ban tashi daga kan daddumar ba sai qarfe bakwai na safe, “Kin ta shi lafiya?” Na fadi hakan ina kallon ta bayan na fara gajiya da kallon da take bi na da shi tunda ta idar da sallar asubahi. A zatona barci za ta koma amma sia na ga ta ci gaba da zama a gefen gado. Gyada kai kawai nayi, sannan na janyo wata ‘yar qaramar akwati a qarqashin gadon, budewa na yi cikin nutsuwa na fara ciro wasu qananan kwalabe a ciki. “Idan kwai abinda kike buqata kina iya tambayar duk wanda kika gani cikin gidan nan. Zan yi barci… idan za ki yi kallo ki fita falo.” Na fadi haka ina kallon Fatima ido cikin ido. Kai kawai ta daga a maimakon buda baki, ta ba ni amsa. Ban damu ba na bude kwalba daya daga cikin kwalaban na shanye ruwan ciki, Sai da nasha kwalabe uku, sannan na dauko wata qwaya na sanya a bakina na taune na hadiye ba tare da na kora ruwa ba. Kadan kadan idanuna suka lumshewa suna budewa nan da nan na fara ganin komai hurhudu, Don haka na gyara kwanciya a kan gadon na juya wa kwalaben da na gama amfani da su baya. “Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un!” abinda farima ta furta kenan hankalinta a tashe, tana kallon na yi daidai ina barci a kan gadon. Sadaf-sadaf ta tashi daga inda take zaune har zuwa gurin kwalaben. Benelyn, Totalyn, sunayen da aka rubuta a jikin kwalaben kenan. A hankali ta janyo akwation ta bude, Abubuwan da suke ciki suka yi matuqar tayar mata da hankali. Kayan maye ne wadanda ba ta san iyakarsu ba a ciki, Qwayar da ta ga na tauna ba tare da ruwa ba, qwayar roci ne. jikinta a sanyaye ta rufe akwatin ta mayar inda ta dauko. Kallo na take tsawon daqiqun da ba ta san iyakarsu ba, Fatima ta raya a ranta, kyakkyawa ce ni ta gaban kwatance, ta lura ba na jerin baqaqen mata, amma kuma ni ba fara ba ce. Kuma na fi kalar chakulet haske. Wani irin haske fatata take dauke da shi mai matuqar daukar hankali. Ba ni a cikin jerin mata masu qiba, amma ni ba siririya ba ce, dukiyar fulanin da suke tsaye kyam kuma cikakku a qirjina shi ne abinda yake kara fisgar hankalin maza da mata a fuk lokacin da na fita sanye da qanana kaya (English wears). Cikina a dame yake tamkar ba na cin abinci. Ina da yalwataccen qugu mai firgita hankalin duk wani lafiyayyen namiji. Gaba daya a jikina babu wani abu na kushe, sai dai ga hasidin iza hasadin. Dara-daran idanuna wadanda har ‘yan uwana mata daukar hankalinsu suke, ga wani irin lumshewa da suke a duk bayan second hudu, wanda wasu suke tsammanin gayu ne irin nawa, amma haka Allah ya halicce ni. A fuskata za ka gane ni din qaramar yarinya ce, a tunanin Fatima idan na yi wuta in kai shekaru sha bakwai. Ba ta tunanin zan dara haka ko kadan. A dan fahimtar da ta yi mana duk sauran ‘yan matan gidan sun girme ni. "Idan akwai kuskure a hasashena ai zan tabbatar tunda ina gidan.” Ta fadi hakan a zuciyarta. A dan fahimtar da a yi min daga daren jiya zuwa safiyar yau ni yarinya ce mai tsananin ibada, don ta lura tun daren jiya ban bar kan darduma ba saida na je jikin gadon na tashe ta ta yi sallar asubahi. Ina tashin ta kan dardumar na koma. Sannan na dauki tsawon awa daya da rabi ina karatun Alqur’ani mai girma bayan na idar da sallar asubahi. Abinda ya daure mata kai a game da ni shi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27