Chapter 17
Chapter 17
aiwatar da abin da ya yi niyya tunda farko amma babu dayan daya yiwu, hanun na maqale a iska. Wani matsanancin tsoro ne da mamaki ya ziyarceni don haka na ja da baya zuciyata tana bugawa Fat!Fat!Fat! kamar za ta faso waje ta fito. Dana qara kallon fuskan mahaifina kuwa sai abin yaso ya bani dariya, ya matuqar galabaita, a fuska kawai za a gane matuqar tsoratarshi balle kuma a kai ga yanda jikinsa yake mazari, rashin sanin abin yi da kuma ganin lokaci yana kara qurewa har ana kirayen sallar magariba a masallacin unguwar yasa na matsa kusa da shi. Ruwa da yake bin qasan tiles din tsakar dakin ne ya bani mamaki, sai a wannan lokacin na tabbatar fitsari mahaifina yayi, duk yanda naso kar in yi dariya sai da na dara. Hannuna na daga na tankwa6ar da hannun nasa zuwa qasa kamar an yi ruwa an dauke jijiyon da suka sagar masa da hannun suka saki. Da gudu ya fice daga dakin, ni kuma na ci gaba da qyalqyala dariya. Ko don akwai yarinta ne a tattare dani a wancan lokacin sam ban dauki abin da ya faru da wani muhimmanci ba, ina gama dariya na sake dauro alwala na gabatar da sallar magariba. Bayan na idar ne na zauna a nutse na fara bubbbude sabbin jakunkunan dana gani wadanda na san ba nawa bane har guda uku a cikin dakin. Farin ciki mai tsanani ya wadaci fuskata ganin abincin gwangwanin dana leda kala-kala shaqe da babban jakar da saboda girmanta da qyar na iya zage zip din. Jaka ta biyu sabbin kaya ne english wears masu matuqar yawa shaqe da jakar. Jaka ta uku kuma dangin drinks ne shaqe a ciki, irin wadanda na saba sha a gidan tsohuwa Zahara’u. Farin cikin daya cika zuciyata yasa na manta da babin mahaifina da halin da yake ciki, sai da na ci na sha na qoshi sannan na gabatar da sallar isha’i, na kwanta a gado da nufin yin barci. Tunanin tsohuwa Zahara’u dasu Hassana da Usaina, da irin rayuwa mai dad'in dana gabatar a gidanta ne ya dawo a zuciyata. "Yanzu waye zai riga rarrashina yana shafa min kai har in yi barci? Waye zai ringa bani abinci a baki? Waye zan ringa yiwa shagwaba yana rarrashina? Waye zai ringa min kitso da kwalliya? Wa zai ringa koya min karatun boko dana larabci? Wa zai ringa dafa min duk kalar abincin dana buqata da wanda ban buqata ba masu dad'i? Wa zai...... wa zai.... wa zai..? Ganin abubuwan dana rasa a rayuwata suna da matuqar yawa yasa na fashe da kuka ina kiran “Ammi (kamar yanda nake kiran tsohuwa Zahara’u kafin in san sunanta) Ammi don Allah ki dawo gareni.... Anty Hassana... Anty Hussaina... ku dawo gareni don Allah...” abin da nake mamaitawa kenan ina kuka ina birgima a kan gado. Sai da nayi kuka ya isheni wanda ya daukeni tsawon awa uku, amma duk cikin wadanda nake kiran ba wacce ta amsani. Shiru na yi ina ajiyar zuciya, idanuna sai zafi suke min saboda kukan dana dauki tsawon lokaci ina yi, rintse idanu na yi ina jiran barci ya daukeni ko zan sami sauqin baqin cikin da yake cunkushe a zuciyata. Tsawon lokaci ba barci ba alamarsa daga qarshe dana gaji da juye-juye sai na tashi na zauna na sanya kaina a tsakanin cinyoyina na fada duniyar tunani mai zurfi. Abu fa kamar wasa karamar magana na neman zama babba, kwana biyu ana wasan buya tsakanina da Abbana, kuma a wadannan kwana biyun ko barcin minti biyar ban samu ya daukeni ba. Idanuna duk sun tashi saboda barci ba a cin bashinsa, duk iya tsawon awoyin da zan dauka a kwance ina jiran barci ya dauke ni sai dai in gaji in tashi zaune amma barcin ba zai zo ba. Ina matuqar son in yi barci don har layi na ke yi idan ina tafiya a tsakar gida, kuma a wannan ranar tun daga sallar asubahi da mahaifina ya fita gida bai dawo ba, hankalina a tashe yake matuqa, na yi kuka harna gaji ba wani sassaucin dana samu. Misalin qarfe biyu na ranar dana cika kwana uku a wannan hali na yanke wa kaina shawarar fita qofar gida ko zan sami mai taimakamin. Sanye da riga t- shirt da wandon jeans wanda ya fito da dukkan suroin jikina, rigar ta kamani sosai, 'yan kananun kirgan dangin dana fara suna tsaye cas cas a qirjina. Hula ne sanye a kaina amma duk da haka sai da ya tona asirin dogon gashin da nake dashi. Qafata sanye da silifas din wanka na tura qofar get din gidanmu na leqa kaina waje a hankali, da yake layi ne na masu hannu da shuni, kuma ranar litinin ce ranar aiki unguwar tsit babu alamar mutane, ko na masu gadin gidaje. Ina tsaye a qofar gidanmu ina hawaye na rasa ina zan dosa? kamar daga sama naga qofar get din gidan da yake kallon namu ya bude, wani kyakkyawan saurayi matashi ya fito sanye da kayan motsa jiki. Kallon kallo ya gudana a tsakaninmu idona share-share da hawaye. “Qanwata lafiya?” Ya tambaye ni da kulawa a muryarsa. Shiru na yi ban amsa masa ba, kuma ban daina kukan ba. “Ko kina kukan tafiya da abbanki yayi ne?” A bakin sa na ji wai mahaifina ya yi tafiya don haka na yi qarfin halin girgiza masa kai alamar a’a. “To mene ne? Kina jin yunwa ne?” kai na sake daga masa alamar a’a. Bai gaji ya sake tambayata “Ko baki da lafiya ne?” Da hanzari na daga masa kai alamar, “Eh.” Na qara da fadin “Don Allah ka taimaka min da maganin da zan samu in yi barci, yau kwana ina ta so inyi barci amma ko gyangyadi bana iya yi.” Ina gama fadin haka na rushe da kuka mai tsananin qarfi na tsuguna a qasa, hannu biyu na dora akai ina shassheqar kuka. “Oh, sorry qanwata mai kyau, ba dai barci kike son ki yiba?” “Eh.” Na fada bakina har rawa yake yi gurin fadin haka. “Jirani a nan ina zuwa.” Cikin gidan da ya fito ya koma ya tattaro min kwalaban magungunan tari da qwayoyi masu gusar da hankalin mutum leda guda ya kawo min. “Ki yi ta sha har sai kin ji barci mai nauyi yana fizgarki sannan za ki daina sha.” Abin da yace min kenan ya fara tafiya gudu-gudu zuwa inda ya nufa. "Wannan rana ita ce ranar farko ta fara shaye-shaye na" Ina fadin haka na fashe da kuka su Fatima suna tayani, sai da muka yi ya ishe mu, sannan na ci gaba da basu tarihin rayuwata. "Tun daga wannan ranar matsalar rashin barci ya kau daga gareni, sabo mai qarfi ya shiga tsakanina da Mahfuz (kamar yanda ya bayyana min sunansa) ina kiranshi da “Yayana” shi kuma yana kirana da “Qanwarshi mai kyau” Tun daga lokacin ya zama idan zan yi barci sai na sha wadannan kayan mayen nake yin barci, idan sun kusa qarewa zan sanar da shi, shi kuma bai tava gajiyawa gurin kawomin wadansu ba. Idan mahaifina baya nan har gidanmu yake shigowa, kai har cikin dakina, amma ni ban taba kwatanta shiga gidansu ba. Mu’amala tsakanina da Abbana kuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27