Chapter 13
Chapter 13
dawowarsa shine karfe goma sha biyu da rabi zuwa qarfe daya na dare, Shi yasa ta kara sakin jiki don tada hankalin iyayen nata, saboda ta san ita din ‘yar lele ce. “Yasmin me ya faru? Me ya faru da hannun naki? Wa ya tava ki? Ko ke da yayan naki ne?” Wadannan jerangiyar kalaman da Mummy da Daddy suka ringa furta mata kenan hankalinsu a matukar tashe suna qoqarin kamo hannun nata amma sam ta qi ba su damar haka. Duk yadda suka so rarrashin ta don sanin abinda ya faru taqi saurarawa, ihu kawai take ba qaqqautawa. "Ko Kun samu accident ne?” Mummy ta sake furta hakan tana qoqarin rungume ta a jikinta. Tun shigowar ta yana kwance kan tree sitter yana busa sigarinsa hankali kwance, A rayuwarshi ya tsani hayaniya, shiyasa matuqar yana gidan ko TV babu wanda ya isa ya kunna ya qure volume, sai dai idan shi yayi ra’ayin haka. Ba zato ba tsammani taji an fincike ta daga jikin Mummy, kafin ta wartsake ta gano wanda yayi mata haka taji saukar mari mai matuqar zafi a kuncinta na dama, Tsananin azaba ya sa ta kife a tsakar falon ta yanka ihu mai matuqar firgitarwa, idanunta tsab suka fada cikin na Yayanta Abba tsaye kyam a gabanta yana hucin fusata, alamun a kowane lokaci yana iya rufe ta da duka, ba shiri ta sanya hannunta mai lafiya ta toshe bakin ihun tana makyarkyatar sanyi da tsanani tsorata. “Abba wannan wane irin zalunci ne? baka da hankali ne? kana ganin yarinya ta shigo tana kukan hannunta don zalunci shine za ka qara mata da mari? Idan ba za ka rarrashe ta ba a matsayinta na qanwarka ai…” “Shiiiiiii..." Ya sanya yatsarshi a baki ya dakatar da mahaifiyar tashi yana gwalalo mata idanu, tamkar zai cinyeta d'anye “Mummy kar ki min ihu, kina jin yarinyar tana neman haddasa min ciwon kai amma kun biye mata sai wani rarrashinta kuke yi, don ubanta idan ba za ta fadi abinda ya same ta ba me ya sa take mana ihu don ta kashen dodon kunne? Duk ku kuka lalata rayuwar ‘yar iskar yarinyar nan amma duk zan gyara muku zama.” Ya karasa fadin haka yana nuna su da yatsarsa manuniya alamun zazzafar gargadi da Jan kunne. "Abba mu ne za ka gyara wa zama?” Mummy ta tambaye shi idanunta suna niyyar kawo hawaye kamar yadda ta saba idan ya tasa su a gaba da kwando-kwando na rashin mutunci. “Mummy na ce ki yi min shiru ko...?” “Tasss!” Saukar zazzafar marin da ya jiyo a kumatunsa na dama ya hana shi ajiye numfashin maganarshi daidai, da jajayen idanunshi ya juya don ganin wanda yayi mishi wannan danyen wulaqancin, hada idanunsu keda wuya ya sunkuyar da nashi qwayoyin idanun yana qwafa a cikin zuciyarshi. “Ashe har yanzu kana shuka wannan rashin mutuncin?” Abdul’Ahad ya fadi hakan bayan ya cakumo wuyar rigar Abba hannu bibbiyu yana shakeshi. “Iyayen naka kake ikirarin zaka gyara wa zama? Ina alqawarin da ka daukar min na daina wulaqanta su?” tunkudo shi gaban Mummy yayi ya duqar da shi kan gwiwoyinshi sannan cikin daga murya yace “Ba su haquri.” Zazzafar huci ya fesar, zuciyarsa cike da kuna, kamar bazai tanka ba sai can yace “Allah ya huci zuciyarki, don Allah ki yi haquri.” Soyayya irin ta d'a da uwa yasa har tana fadada fuskarta da murmushi gurin amsa yafiyarshi. Shi ma Daddy bai ja da nisa ba yace ya yafe, dama duk tabarbarewar tarbiyar d'an nasu sune sila, Sun nuna mishi matsanancin gata kasancewar sun dad'e ba su samu haihuwa ba, kuma sunan mahaifinshi ke gare shi, shiyasa suke kiran shi da Abba. Qwafa Abdul’Ahad ya yi, sannan ya cakumo wuyar rigarsa ya daga shi tsaye, “Idan baka manta ba zuwana garin nan na qarshe na fada maka zan nemi transfer zuwa garinnan ko don saboda akai, don haka ina yi maka albishiri din dawowa garin nan da aiki, Duk inda ka sa qafa ina sane da kai, Ka san abin da zan iya aikatawa da wanda ba zan iya ba. idan kunne ya ji….” Yana gama fadin haka ya nemi guri ya zauna, ya watsawa Yasmin da take tsiyayar hawaye harara, sannan ya fara mayar musu da bayanin duk abinda ya faru da Yasmin. Kafin qarfe goma na dare sun nemi mai daurin karaya na gargajiya ya duba mata hannun, ya kumbura suntum saboda jinkirin da aka dauka ba tare da an bi ta kanshi ba, Ashe wai karaya ta samu a hannun, Tasha tsananin azaba kuwa kafin a gama gyaran, don saida aka rirrike ta, duk da haushin da take ba shi yayi matuqar tausaya mata, ganin irin wahalar da ta sha gurin daura hannun. Ya dauki tsawon lokaci yana rarrashin ta, daga bisani ya nufi bangarensu, zuciyarshi cike da tunani kala-kala “Me yake faruwa da wannan yarinyar ne? anya kuwa ma mutum ce? Daga riqon hannun Yasmin sai kuma a ce ta karya ta?” Da fari tun a Plaza ya zaci raki ne da shagwava irin na Yasmin, amma tunda mai dorin ya fadi ta sami karaya jikinshi ya yi matuqar sanyi, zuciyarshi ta cika da tunani da tambayoyi iri-iri. *** Muna zauna a tsakar falo, misalin qarfe goma da rabi na dare, hira muke yi cikin wasa da dariya. Idan mutum ya kalle ni tamkar ba ni ce kwance magashiyan a dazu ba, hatta Fatima a wannan lokacin ta saki jikinta da mu, duk da dai ba ta cika tsoma bakinta a hirar da muke yi ba, amma idan mun yi abin ban dariya ta kan dara. “Ya dai Fatima? Fadi abinda yake ranki mana.” Na wurga mata tambayar ba zato don tun dazu na lura akwai abinda take son furtawa. Tsawon daqiqu tana kallon na da motsa bakinta alamun tana jinjina abinda zata fada ne. Don in qara mata qwarin gwiwa yasa na ce “Kar ki damu, fadi maganarki kawai” “Ina neman alfarma a gareki.” Ta yi qarfin halin fadin haka tana matsa yatsun hannayenta. “Alafarmar me?” Na tambayeta da mamaki a fuskata. “Don Allah ki bamu tarihin rayuwarki, don Allah.” Dan murmushi nayi, sannan nace “Kwantar da hankalinki fatima, ba sai kin hadani da Allah ba, da ma a yau na yi niyyar warware muku zare da abawa na tarihin rayuwata. Amma ku bani minti talatin in yi wanka….” WACE CE AYSHA AZZAHARA’U?? Mahaifina Alhaji Sa’ad mutum ne mai matuqar son kudi, a rayuwarshi ba abin da yake so sama da kudi, tsabar son kudi irin na mahaifina yasa ya baro can garin iyaye da kakanninshi ya shiga duniya neman kudi. Yana iya yin komai matuqar yasan zai sami kudi, shigarsa duniya ba inda bai zaga ba a manyan garuruwan arewacin Najeriya. Babban matsalar mahaifina shi ne ya san ya nemi kudi ya tara, amma sam bai san yanda zai kashe su ba, baisan ya biyawa kanshi buqata ba, yana matuqar jin ciwon fitar da kudi ya kashe, idan zai kashe qwandala a cikin dukiyarshi yana jin tamkar naman jikinshi yake yanka. A dole yake kashe naira dari biyu a rana, ko ciwo yake ya gwammace ya shiga daji ya sassaqo ganyayyaki ya dafa har Allah ya bashi lafiya, hatta abinci bai iya cire kudi ya siya mai tsada, sai dai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27