Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ce ta amsa da cewa "Zai aikata fiye da haka indai mahaifinki ne, amma da sannu zasu riski qarshensu dashi da duk wasu masu hannu acikin wannan al’amari, domin Allah ba azzalumin kowa bane.” “Qwarai kuwa” Na fada ina gyada kai cike da gamsuwa da abinda ta fada har zuciyata. “Zo muyi tattaki can baya ko zamu samu ruwa kiyi alwala” Anty Hassana ta fadu haka tareda miqewa tsaye ta fara tafiya, muna hanya nake tambayarta ko tasan yawan kwanakin dana dauka a hannun wannan matsafin? "yau kwananki goma sha biyu.” Ta bani amsa ba tare da ta kalli fuskata ba. Kafata babu takalmi haka nake tafiya ina taka danyar ciyayi da yake lokaci ne na damina har muka isa wani dan kogi mai dauke da ruwa shar – shar gwanin ban sha’awa. Alwala kawai na yi kamar yanda ta umarceni amma a zuciyata nake ayyana idan na rama salloli sai na dawo kududdufin na yi wanka. Muna komawa gurin wannan bishiya da muka bar Anty Hussaina naga wani abin mamaki da al’ajabi. Dan qaramin daki ne mai kama da tanti aka kafa agurin, duk wadannan manyan jakunkuna da su Anty Hassana suka taho da su anshigar dasu cikin dakin, dana ta6i abinda akai dakin dashi a zuciyata nake fadin indai ba qudira ta Ubangiji ba zayyi wuya iska ko ruwa ya iya ture wannan dan qaramin rumfa mai kama da daki, ‘yar qaramar katifa aka aje a ciki an shinfida zanin gado akai da filo guda daya. “Ga doguwar riga da hijabi da sallaya ki rama sallolin da suke kanki.” Anty Hussaina ce ta katse min tunani da mamakin da nake yi tana fadin haka. “Ta6dijam! Anty Hussaina duk a cikin wannan dan qanqanin lokacin da muka dauka gurin neman ruwan alwala ne har ki ka iya gina wannan dakin?” Dariya sukai itada Anty Hassana sannan tace, “Waya fada miki ginawa nayi? Kafawa kawai na yi don dama yana nannade a cikin wancan babbar jakar. Ki yi sallah kici abinci lokaci yana dad'a tafiya” Aunty Hassana ce ta katse maganar dana farayi don haka naja bakina nai gum na canza kayan jikina sa’annan na tambayi gabas suka nuna min na tada kabbarar sallah. Ban san iya adadin awoyin da na dauka ina rama sallolin dake kaina ba, amma tabbas na yi matuqar dadewa, domin har rana ta fadi, duhun dare ya fara shigowa sannan na idar “Alhamdulillah.” Na furta bayan na shafa addu’ar da na dad'e ina yi. Flaks mai dauke da ruwan zafi Aunty Hassana ta dauko daga cikin wata jaka nan take ta had'a min tea mai kauri ta miqo min da zafinshi na shanye, sanna ta miqo min robar takeaway mai dauke da dafadukan taliya mai hadin hanta da qoda. Na ci abinci mai matuqar yawa sannan na kora da ruwan swan. “Duk abinda za ki buqata yana cikin jakunkunan nan. Yanzu mu zamu tafi, ki saki zuciyarki, kar kiji tsoron komai, domin Allah yana tare da ke. A nan za ki ci gaba da zama zuwa wani lokaci. Za ki iya zagaya duk inda kike so a cikin dajin nan. Amma kar ki kuskura ki shiga harkar da ba ruwanki, duk wanda zaki gani a cikin dajin nan ki sa mishi ido. Lokaci zuwa lokaci za mu ringa kawo miki ziyara.” Bayanin da suka yi min kenan muka yi sallama, suka fice daga cikin dakin. Ban kwanta barci ba sai da na bude duk jakankunan na ga abinda suke dauke da shi. Tabbas ba su yi qarya ba, komai da zan buqara akwai a ciki, Ba na tunanin akwai abinda zan nema a yanzu sai zuwa gaba. Har da dan qaramin agogo wanda ya nuna min lokaci qarfe tara da rabi na dare. Abinda ya bani mamaki kuma ya sanya ni murmushi shine, har da kayan mayen da suke taimaka min gurin samun barci, har pad din da zan nema idan period dina ya zo akwai a ciki. Sai da na gama kintsa komai a gurin da ya dace sannan na yi alwala da daya daga cikin goran ruwan swan din da suka kawo min, na yi sallar isha’i da shafa’i da wutiri. Izuwa wannan lokacin agogo ya nuna min qarfe goma sha daya da kwata. Waje na leqa don ganin yanayin da garin yake ciki ba tare da jin tsoron komai ba a zuciyata, duhun dare ya fara tsalawa, ko hasken farin wata babu. Sai kukan tsuntsaye da yake tashi nesa kadan da inda dakina yake. Da ‘yar qaramar tocilan da suka kawo min nake haskawa har na isa jikin wannan babbar bishiyar da na fara yada zango tun bayan isowata dajin. Iska mai hade da sanyi amma ba mai cutarwa ba yake kadawa a gurin. Ban jima ba na koma daki na kwanta na yi addu’o’in kwanciyar barci bayan na kora kayan maye. A taqaice sai da na dauki tsawon shekara guda ina rayuwa a cikin wannan dajin mai yawan bishiyoyi da ganyayyaki. Babu wata halitta da take ba ni tsoro a dajin, abin al’ajabi ma shine duk dabbar da na hadu da ita ba ta kulawa da al’amarina. Sai dai in yi nawa gurin ta yi nata gurin. Babu wata dabba da ta ta6a qoqarin cutar da ni, har qananan qwari irin su macizai da kunama ko kul6a ko wahainiya, kuma a kullum ina haduwa da su. Wani lokacin ma suna qofar tantina amma harkarsu daban tawa daban. Ganin haka ni ma ba na shiga harkarsu. Don yana daga cikin kashedin da su Aunty Hassana suka yi min. Duk bayan sati daya suke kawo min ziyara, duk abinda nake buqata kafin ya qare suke kawo min wani. Kuma duk iya tsawon wannan lokacin da na dauka ina rayuwa a wannan daji ban fasa shan kayan maye ba idan zan yi barci. Akwai lokacin da na tambayi Aunty Hussaina cewa, “Aunty na lura sam ba kwa son wannan maganin barcin da nake sha, amma a yanzu da zaran ya kusa qarewa kuke kawo min wani. Kun goyi bayan in ci gaba da sha kenan?” “A’a, har yanzu muna baqin ciki da shan da kike yi, za ki daina idan lokaci ya yi.” Amsar da ta ba ni kenan, muka rufe wannan caftar. Abinda yake kara daure min kai da sanya ni tunani shi ne, rashin ganin bil’adama ko guda ya ratso ta inda nake a wannan daji. Idan na yi kamar zan tambayi su Aunty sai kuma wani abu ya dauke min hankali na bar tambayar a cikin zuuciyata. A ranar da na cika shekara goma sha shidda a duniya suka shaida min zan bar wannan daji izuwa wannan gida da muke rayuwa a yanzu. Duk kayan da na yi amfani da su a cikin wannan daji sun umarci in bar su a can za su sa a kwashe, a yi sadaka da su. Sanin za su sai min wasu kayan masu kyau da tsada ya sa ko musu ban yi musu ba. Tafiya mai tsananin nisa muka yi muka iso gurin mota Sienna irin kirarta daya da wacce mahaifina ya dauke ni ranar da zai saida ni ga Ubangidanshi matsafi Alhaji Buba. Wani kyakkyawan saurayi mai kama da Larabawa shi ne a mazaunin direba, har qasa ya durqusa ya gaishe mu, sannan

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});