Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

‘yar yayayyiya. Mahaifiyarta sanadin hatsarin mota da suka yi ta samu tavin qwaqwalwa, sai riqonta ya koma hannun wan mahaifinta. Mutum ne mai matuqar son ‘ya’yan shi, sam baya yarda a ce dan shi ya yi wani laifi, yana iya sabawa da kowa akan ‘ya’yansa. Yusuf shi ne babba a cikin yaran wan mahaifin nata, tunda ya qyalla ido ya ga makerin budurci ya fara kera Siyama ya kwallafa ranshi a kanta, da wayau da lallami da alqawarin karya a kan zai aureta ya lalata mata rayuwa har ciki ya shiga jikinta, da kan shi ya kai ta asibiti da niyyar a zubar da cikin, gurin fitarwar ne aikin yazo da gaddama sai jini ya balle mata. Ganin hakan da yayi sayya gigice, hankalinsu a tashe yaje ya samu iyayenshi kan cewa ta yi ciki gurin zubarwa za ta rasa ranta, wai shi ma wani abokin shi ne ya kira shi a waya yake fada masa. Da kyar likitan ya samu nasarar tsaida jinin, wannan lokacin bata san inda kanta yake ba, bayan an samu nasarar farfadowarta sai wan uban nata ya koreta daga gidanshi, daga qarshe sai Allah ya hadamu da ita. “Ita kuma waccen sunanta Suhaila Sulaiman, wani azzalumi ne ya samu mahaifiyarta tana tsaka da hauka akan bola ya sadu da ita sai ciki ya shiga jikinta, bayan ta haihu ne ‘yan unguwan suka kaita gidan marayu ta girma a can. Nima a can din Allah ya haxamu da ita. “Ni kuma sunana Aysha Azzahara’u………………" Ringing din wayata shi ya katse min tarihina da na yi niyyar ba su “Hello…” na furta da sanyin murya ina lumshe ido. “Barka da rana babyna, kin gane mai magana kuwa?’' Aka fadi haka daga can bangaren. “Hajiya Danasha" Na kai tsaye bayan na daure fuskata kamar tana gaba na. “Qwarai kin canka daidai sarauniyar mata, na jiki shiru har yau ba ki qara waiwayata ba shi yasa na bugo don jin shawarar da kika yanke, Kar ki manta duk matsalarmu daya ne, A Dalilin daa Namiji mu ma muka kafa wannan qungiya don taimakawa junanmu, na san kina da dukiya don haka ban kwadaita miki ita ba, amma kar ki manta ko kogi bai qi dad'in ruwa ba. Sannan akwai biyan buqatar juna a wannan harkar, kuma za ki qara tsanar namiji fiye da yanda kike a yanzu, muna da manyan mata, masu riqe da manyan muqamai na gwamnati, a wannan qungiyar akwai mata ‘yan siyasa, akwai mata manyan ‘yan kasuwa…. Ke har daga qasashen qetare irinsu India, China, Malaysia akwai wadanda muke harka dasu. Ki shigo cikin qungiyarmu ke da sauran ‘yan matanki ku ji dad'in rayuwa, ku shana da dukiya, ku yi abin da kuke so zamu tsaya muku. Wallahi tun sati biyun da suka wuce da Allah ya hadamu sam bana iya barci son ki a kullum dad'a ruruwa yake a zuciyata… ki taima…” “Dakata Danasha..!!" Na kira sunanta kai tsaye ba tare da inkiyar hajiyar ba, saboda tsananin bacin rai, a zafafe na ci gaba da fad'a mata duk abinda yazo bakina. “Maganata ta qarshe akan wannan qungiya taku shi ne, wallahi ko da zan yi yawo tsirara saboda tsammanin talauci ba zan tava yin qazantacciyar rayuwa irin ta qungiyarku ba, kuma a cikin ‘yan matan da nake tare dasu ma babu wacce za ku samu hadin kanta. Don haka ki tattara tsufanki ki qara gaba, kuma kar ki qara cewa kina so na idan ba haka ba sai na zubar miki da haqora.” Ina gama fadin haka na katse wayata ina numfarfashin fusata, Rintse ido na yi na kwanta a kan kujeran da nake zaune, minti biyu tsakani duk suka fara sulalewa zuwa dakunansu. “Zo mu tafi dakina Fatima, duk abin da ba ki gane ba sai in qarasa amsa miki.” Rahama ce ta furta hakan, sannan ta janye hannun Fatima suka nufi dakinta, tsawon minti goma sha biyar ina kwance idanuna a runtse daga bisani na miqe na nufi dakina. “Tsawon wani lokaci kenan da kafuwar wannan qungiya taku?” Fatima ta tambayi Rahama bayan ta zauna a kan kujeran dressing mirror. “Wata shida kenan.” Rahama ta amsa mata batan ta zauna a gefen gado. “Bani tarihin Aysha mana” Sai da ta yi murmushi sannan ta amsa mata da cewa “Duk gidan nan ba wacce ta san tarihin Aysha, ko wani lokaci idan ta yi niyyar fada mana sai wani abin ya taso kamar dai yanda ya faru yau, amma duk mun qosa qwarai mu ji tarihinta, bayan sunanta da shekarunta babu wani abu da muka sani a kanta.” “Shekarunta nawa?” Fatima ta sake tambayarta. “Sati biyu ya rage ta shiga shekaru goma sha bakwai.” Shiru ya ratsa tsakaninsu harna tsawon minti biyu, kowacce a cikinsu da irin saqe-saqen da take yi a zuciyarta. “Amma kun san tana shan kayan maye?” Fatima ta sake tambayarta fuskarta na bayyana damuwa da jimami. “Qwarai kuwa, duk gidan nan mun san haka, a taqaice ma ba ta iya barci in dai ba ta sha kayan mayen ba. wannan yana daya daga cikin dalilin da yasa duk gidan nan muka qosa mu ji tarihinta, akwai abubuwa masu matuqar ban mamaki da daure kai a tattare da ita. Karamin misalin da zan baki shi ne dukkanmu babu wacce ta bata tarihinta da kanta, daga haduwarta dani ta karanto min tarihina daga farko har qarshe, kuma duk sauran ‘yan matan hakan ta kasance dasu, kema ranar da aka yanke miki hukunci ita ta karanta mana tarihinki.” Ajiyar zuciya ta sauke tana qara jinijna abin a cikin ranta, can kuma ta yi qarfin halin fadin “Wannan gidan qasan da kuke rayuwa a ina kuka samu kudin ginawa?” Sai da Rahama ta qyalqyale da dariya sannan ta fara tunanin tsarin gidan nasu da Fatima ta radawa gidan qasa. Daga can kofar gidan dai shi kadai ne kwal a tsakiya dajin, sai ka yi tafiya mai nisa kafin ka tadda wani gida a can gaba. Get ne mai matuqar kyau da girma a jikin qofar gidan, katanga ne mai tsananin tsawo wanda duk wayon barawo bai isa ya tsallakaba, idan ka shiga harabar gidan, rumfuna ne aka yi gurin adana motoci a ko wani kusurwa na harabar gidan. Daga can tsakiya aka yi ginin wani daki wanda shi kadai ne qwallin qwal a duk girman harabar gidan, ko wani rumfa motoci ne guda hudu, sai daga gefe aka jera mashinai ‘wayyo kudina' guda goma. Motoci masu matukar kyau da tsada guda goma sha biyu ne a gidan. Idan ka bude wannan dakin da yake tsakiyar gidan babu komai a ciki sai wani hanya a tsakiyar dakin daya gangara yayi kasa an jera matakala tamkar dai gidan sama amma wannan ne qasa ne, idan ka miqe zuwa kasan matakalan ba inda za ka tsinci kanka sai a wani qaton falo mai matuqar girma da qyatuwa, an zuba duk wani kayan more rayuwa da ake bukata, a cikin falon akwai dakuna guda guda goma sha biyu, ako wani daki akwai bayi aciki, daga can gefe aka yi kichin hade da sitor dauke da katan-katan na lemuka da buhu-buhu na abinci, a takaice tsaruwar gidan ya wuce in bayyanashi a wannan dan qanqanin littafin. Ajiyar zuciya ta saki bayan ta gama tunanin tace, “Duk girman gidan nan

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});