Chapter 20
Chapter 20
inda kike zamu biyoki. Hassana da Hussana.” Wani sanyi da ni’ima ne suka mamaye zuciyata dana gama karanta wannan wasiqa. Hankali kwance na fara hada kayana a cikin babban jaka. Muna tafe a cikin qatuwar jeep qirar sienna wacce na ga mahafina ya dawo gida da ita, ina zaune a kujerar gefen driver yayin da mahaifina yake tuqa motar, su kuma abokan nasa suna zaune a kujerar tsakiya na motar, mun danyi tafiya mai nisa amma bamu fita daga cikin gari ba, mahaifina yasa hannu daya ya bude aljihun motar ya dauko wata kwalba mai kama dana turare ya fesa min a hannu yana fadin “Shin-shina wannan turaren ki ji yana da dadin qamshi?” Ba tare da wani tunani ba na kai hannun zuwa ga hancina don shinshinawa. Daga wannan lokacin ban sake sanin inda kaina yake ba, sai bude ido na yi na ganni kwance a wani waje mai tsananin duhu. Alh. Buba qwararre kuma shahararre wajen safarar duk wani nama da ya shafi sassan jikin Bil’adama. Babu wanda ya san asalin garin Alh. Buba. shahararren mai arziki ne na qarshe, ya tara dukiyar da shi kanshi baisan iyakarta ba. Yayi aure-aure kala-kala, duk manyan jihohin arewacin Najeria babu jihar da bai auri mace ba, duk matar da ya aura kwanaki talatin take yi a gidanshi sai ta rasu. Wannan yasa mutane suka kafa mishi kahon zuka, karshe da ya ga asirinsa yana neman tonuwa sai ya haqura da aure gaba daya. Duk matar da ya aura idan ta mutu baya tava kawo gawar ga iyaye da danginta, Sai dai ya je ya sanar musu Allah ya yiwa xiyarsu rasuwa. Idan ya auri mata a Kaduna sai ya kaita gidansa na Abuja bayan kuma yana da gida a Kadunan. Ko kuma idan ya auro daga Kano ya kaita gidansa na Katsina, babu matar da ta tava haihuwa dashi a duk cikin matan da ya ta6a aura har su ashirin da daya. Yana da mutane da yawa wadanda suke aiki a qarqashinshi, akwai shi da hannun kyauta, ya gina gida daban – daban wadanda shi kanshi bai san iyakarsu ba. Matuqar kana aiki a qarqashinshi zaka huta Amma da dukiyar haram, haka kawai Allah ya saka mishi qaunar mahaifina da yake cikin ma’aikatanshi, qaunar da yake mishi ita ta sa ya kasa sanar mishi da sana’ar ainihin sana’arshi. Mafi yawancin tafiye tafiyenshi da mahaifina yakeyi yanada manyan masu arziqi da yake harkar har amtaccen kasuwanci tun daga qasarmu Nijeria har zuwa qasashen qetare, duk abinda kake nema na sassan jikin bil’adama zaka samu a gurinshi, idan ma babu alokacin zai baka lokacin da zaka dawo ka samu. Yana da kebantattun gidaje a garuruwa daban – daban inda ake gudanar da yanka mutane tamkar kaji. Yanada ke6antaccen gida da yake sato mahaukata mata don biyan buqatar wasu masu neman duniya. Ko ciki yaga anyiwa mahaukaciya yakansa a saceta yaci gaba da ciyar da ita har sai ta haife abinda yake cikinta, babban burinshi ya samu jaririn ko jaririyar da take dauke dashi don sai da shi ga wasu masu neman duniya. Yana tura mutanenshi asibitoci don su sato mishi jarirai, a gefe guda kuma Alh. Buba shahararren matsafi ne, duk wanda ya nemi kawo mishi tangarda ko kuma tona mishi asiri sai dai a wayi gari an kashe shi, duk wanda yake shirya mishi mugun abu yana sani. Al’umma da yawa sun zuba ido don ganin qarshen Alh. Buba, amma a kullum tamkar ana qara mishi lafiya da qarfi akan harkokinshi. Wani babban Costomern shi ne ya bugo mishi waya akan yana son ko wani sassa daga jikin budurwa ‘yar shekara goma sha biyar, a lokacin sai Ubangiji ya gwada mishi ikonshi duk yarinyar da aka sato daga wacce bata kai shabiyar ba sai wacce ta haura shabiyar, hankalin Alh. Buba ya yi matuqar tashi, domin anyi mishi alqawarin miliyoyin kudi akan wannan harka, tsafinshi ne ya gwada mishi bazai ta6a samun wannan yarinya ba sai ta hanyar Sa’ad (mahaifina) da yake ya dade da sanin masifaffen san kudi na mahaifina, baishi wata wahala wajen shawo kan mahafina ya sai da mishi da ni a kan Naira miliyan dari ba. Sannan bai 6oye mishi komai ba kan cewa tsafi zai yi da ni, sa’annan ya qara da nunawa mahaifina Alh. Musa wanda ya sai da mahaifiyarshi, don ya samu abin duniya. ***** Wannan daki da na bude idanu na ganni a ciki daya ne daga cikin dakunan tsafin Alh. Buba. Ina zaune a cikin matsanancin duhun da ko tafin hannuna bana iya gani, naji an bude qofa an shigo cikin dakin, koda aka bude qofar ban gane mai shigowa ba don idona ya fara sabo da duhun dakin kuma kafin idanuna su washe aka maida qofar dakin aka kulle. Tsayin mintina biyar naji wata qatuwar murya ta cika dakin tana wasu irin surutai wanda sam bana fahimtar abinda ake cewa, tsayin minti talatin naji muryar ta fara rawa tamkar yana shirin fashewa da kuka, second goma tsakani muryar ta fara kusanto inda nake zaune a qasa don haka na cigaba da takure jikina guri guda ina karanto duk addu’ar da tazo bakina a zuciyata, kamar walqiya naga wani haske ya zagaye ni, a hankali tsoro ke ficewa daga zuciyata don haka na sami damar daga ido don ganin mai wannan qatuwar muryar. Yana tsaye a dan nesa dani tsakanina dashi bai wuce taku biyar zuwa bakwai ba, gajere ne na qarshe kuma baqinqirin, hannunshi riqe da qwarangwal din kan mutum, Tsirara haihuwar uwarshi yake tsaye don haka na sadda kaina qasa inajin qyamar ganinshi, minti biyu tsakani yana tsaye inda yake tamkar an dasa shi amma ya yi shiru sa6anin dazu da yake sambatu, da baya ya ringa tafiya har ya fice daga dakin, yana fita hasken daya zagayeni ya 6ace bat na ci gaba da zama a cikin duhu. Sai da wannan gajeren mutumin ya jera tsawon yini uku yana shigowa yana irin wannan sambatu, idan ya fara kusanto ni sai wannan hasken ya lulluve ni, a karo na uku ne daya nemi qarasowa gareni ta qarfi wannan hasken ya yi jifa dashi can jikin bango. Da alamun yaji jiki matuqa domin ya fi minti talatin bai tashi daga inda aka watsar dashi ba, ya tashi kuma da dingishi ya fice, kuma anan ya bar wannan kan qwarangwal din da yake shigowa dashi. Bayan fitarshi wannan hasken daya zagaye ni bai bace ba, kamar a kunnena naji wata murya tana umarta ta da in isa gurin wannan kai in take shi da qafata na dama. Ban jira komai ba na aikata hakan, ina takewa kan ya dagargaje, take naji dakin da nake ciki ya dauki wani qara mara dadin sauraro, qasar gurin ta fara girgiza tamkar dakin zai rushe in rufta ciki, minti daya tsakani hasken ya bace sai komai na dakin ya koma tamkar yanda yake ada, wannan ihun ma ya tsaya cak tamkar anyi ruwa an dauke. Duk iya wadannan lokacin ban san ko kwanaki nawa na yi a wannan dakin ba, ko kiran Sallah ba na ji, Ina cikin matsanancin duhu, don haka na zubawa sarautar Allah ido ina Istigfari a zuciyata ta. Lokaci mai tsawo naji an budo qofar dakin a karo na hudu, wannan karon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27