Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

A Dalilin Da Namiji Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

A Dalilin 'DA NAMIJI 1 NA FAREEDA ABDALLAH “A yau ne Alqalin babban kotun da yake cikin garin Kaduna ya yanke wa wata mata mai suna Fatima Ibrahim hukuncin xaurin rai da rai a gidan yari, abisa laifin da ake tuhumarta da shi na halaka babban xan mijinta mai suna Nasir ta hanyar watsa mishi ruwan zafi duk jikin sa, wanda hakan ya yi sanadiyyar salvewar duk wata fata da take jikinshi. bai xau awa xaya ba a asibitin “BIBA HOSPITAL” ya ce, ga garin ku nan. Mijin matar mai suna Alhaji Muhammad shi ya danqa matar ta shi a hannun hukumar ‘yan sanda kuma ya tsaya tsayin daka akan lallai sai da ya qatarwa xanshi mai rasuwa haqqin shi akan azzalumar matar ta shi, wacce ba ta da tsoron Allah ko kaxan azuciyarta inji mijin na ta. Ga dai yanda tattaunawar tamu ta kasance da shi.” Gaba xaya ‘yan matan da suke zaune a tafkeken falon suka qara shiga nutsuwar su don jin yanda tattaunawar za ta kasan ce. Fitowa ta kenan daga ban xaki xaure da towel a jikina, na rufa wani qaramin tawul xin akaina, fuska ba walwala na zauna a kan kushin mai zaman mutum uku, sannan na xauki “Remote” a gefena na qure Radion sosai tamkar zai fasa mana dodon kunne. “Ya sunan Malamin?” Xan jaridar ya jefa wa mutumin da suka kira mijin matar da ake tuhuma tambayar. “Sunana Alhaji Muhammad Yusuf.” Mutumin ya amsa da cikakkiyar muryar da ba ta nuna jimami ko kaxan. “A yau ne aka kawo qarshen shari’ar nan da aka xauki tsawon watanni uku anayi tsakanin mai xakinka Malama Fatima da Marigayi xanka Nasir , mai zaka iya cewa akan hakan.” “Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) da ya kawo qarshen wannan shari’ar, tabbas ina cikin farin ciki da godiya ga Allah domin an fitar wa da mai haqqi haqqinsa, mata irinsu Fatima waxanda basa tsoron Allah ko kaxan azuciyar su wannan ya ishe su darasi amma idan har sunada tunani, tun lokacin da marigayi Nasir Allah ya jiqan shi ya tabbatar min da Fatima ce ta aika ta mishi hakan kawai don ya ziyar ci gidan ta a matsayin shi na xan mijinta karo na uku tun bayan dawowar shi daga qasar Malesia karatu. lokacin da ya faxa min hakan bai fi saura minti ashirin Allah ya xauki rayuwarsa ba, kuma na xaukar mishi alqawarin ko da zanyi yawo tsirara sai na xaukar mishi fansa, don haka ayau ina mai farin ciki matuqa su kuma ma su irin halinta ina ma su fatan Allah ya shirye su idan kuma ba ma su shiryuwa ba ne Allah ka tarwatsa su aduk inda su ke a faxin duniya" “To yanzu ya matsayin igiyar auran da yake tsakanin ku?” Xan jarida ya sa ke jefa mishi wannan tambayar. “Tun ranar da abin ya faru na yanke igiyar aurena duka ukun da yake tsakanin mu, kuma na danqa mata takardar ta tun kafin a kawo qarshen wannan shari’ar.” “Akwai zuri’a a tsakanin ku?” “Babu yaro ko xaya a tsakanin mu shekarar mu biyu da aure amma ko vatan wata bata tava yi ba.” “Ba ka tunanin wani irin kallo da iyayanta zasuyi maka?” Dan jaridar ya sake tambayar shi. Muryar shi a fusace ya amsa da cewa, “Ita xin marainiya ce a hannun qanin Babanta na aureta, kuma tunda ya ji abin da ta aikata ya zare hannunshi daga kanta bayan ya yi mata Allah ya isa rainon da ya yi mata, kuma ko iyayanta su na da rai bazan damu da duk wani abu da ya za su ce ba, don kuwa Xa bai fi Xa ba.” “To amma….." “Dakata Malam!! tambayo yinnaka sun ishe ni haka, ina da abinyi” ya katse dan jaridar ya na gwama numfashi ci ke da fusata. “Qarshen tattaunawar da ta gudana tsakanin wakilin mu kenan da mijin mai laifin, wakili namu ya nemi tattaunawarsa da uwar marigayi amma hakan bai samu ba, kuma ya nemi tattaunawa da mai laifin itama ta qi ba mu haxin kai, kalma xaya kawai ta iya furtawa ga wakilin namu. Cikin hawaye ta ke nanata kalmar. “ADALILIN DA NAMIJI” Daga nan ta varke da matsanancin kuka ya yin da ‘yan sanda sukai awon gaba da ita cikin motar shiga ba biya fi ta da Allah ya isa, nan muka kawo qarshen shirin na JAKAR MAGORI…." “Xif na sanya hannu na kashe Redion hankali na atashe kyawawan idanuna sun rine zuwa jajaye saboda tsananin tashin hankali, Safa da Marwa na ke a tsakiyar falon ina doka hannu na dama cikin na hagu, tsawon minti goma na xauka ina hakan da ga bisani na zube akan kujerar da na fara zama tun bayan fitowa ta da ga wanka. Hankalina ‘yan matan da su ke zaune tunda farko a falon yana kaina da alamun jira su ke in furta wani abu sannan su ma su samu bakin magana. “Me maza su ke so su mai da mu a duniyar nan?” Na furta hakan murya ta a kausashe ina kallon ‘yan matan cikin falon xaya bayan xaya. qarar shigowar Messages ba tare da qaqqautawa ba aduk wayoyi na guda uku da suke cikin xaki shiya katsemin maganganun da na fara yi "Safiyya kwasomin wayoyina a xaki" Na faxi haka ina kallon xaya da ga cikin ‘yan matan. Daqiqa talatin tsakani ta fito riqe da wayoyina a hannunta, sai da ta xan rusuna sannan ta miqamin, duk saqonnin sun fito da ga guri xaya ne. number ce kuma babu suna, 7777 shi ne number da ya turo min saqon. Gyara zama na yi don kuwa saqon mai muhimmanci ne a gare mu, saqon daya daga cikin wayoyin na fara karantawa a fili don sauran ‘yan matan su ji meya qunsa. “TARIHIN FATIMA IBRAHIM WACCE TA KASHE XAN MIJINTA NASIR” hakan aka rubuta da manyan baqi a farkon saqon, na xan tsagaita ina kallon fuskokinsu cikin nazari xaya bayan xaya, kowacce a zaqe take da son jin cigaban saqon, don haka na xora daga inda na tsaya. “Marainiya ce gaba da baya, iyayanta Allah ya xauki rayuwar su tun tana ‘yar shekaru uku a duniya, hatsarin mota sukai a hanyar su ta dawowa da ga Abuja zuwa Kaduna marigayi Alhaji Ibrahim mahaifin Fatima shahararren mai arziqi ne. Fatima ita kaxai ce xiyar shi a duniya, mahaifiyar Fatima ‘yar Zindar ce a jamhuriyar Nijar, yawon kasuwanci ya kai mahaifinta can qasar har Allah ya haxa fuskokin su sannan ya sanya soyayya mai tsanani a tsakanin su har sukai aure, bayan kai ruwa ranar da akai da mahaifin Aisha (Kakannin Fatima na wajen Uwa) kan cewa ‘yarsu baza ta yi aure a wata qasa ba. Lokacin da kakannin Fatima na wajen Uwa su ka samu labarin rasuwar ‘Yar su da mijinta sunyi kuka sosai, kuma sunzo har akai bakwai sun buqaci tafiya da Fatima amma Alhaji Musa qanin mahaifinta yace, sam! Hakan bazai tava yuwuwa ba. Sunyi rabuwar dutse da hannun riga wanda hakan ya yi matuqar tunzura su har suka sha alwashin yanda su ka rasa ‘yarsu Aisha mahaifiyar Fatima suka haqura itama Fatima sun haqura da ita har abada, indai ita jinin su ce zata neme su amma su kam baza su tava nemanta ba

Table of Contents

Chapters

27 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});