Chapter 12
Chapter 12
hannu.” Tana maganar tana wani yatsina, wanda yake qarawa fuskarta muni. Shiru nayi mata ban tanka ba, a zuciya ta ina mamakin karfin halinta. “Ki sakar min hannu na ce.” Ta qara maimaitawa a fusace kamar za ta rufe ni da duka. Nan ma nayi iskar kare da ita, tamkar da kurma take magana, kuma dukda haka ban sake ta ba. "Ki sakar min hannu don uwarki.” Ta fada cikin karaji, batan ta lailaya ashar ta makawa uwata, abin da ya janyo dugunzuma da tashin hankalina, da a ce mahaifina ta zaga ba zai tava zuciyata ba ko kadan, sam babu wanda zai fahimci mugun riqon da na yi mata amma ita din tana ji a jikinta don har ta fara rintse ido tana cije baki, gumi yana diga daga goshinta. Duk abinda yake faruwa yana daga gefe yana kallo, shi kanshi yayi niyyar roqon alfarmar in sakar mata hannun, zagin da tayi min ne ya dakatar da shi, shi kanshi zagin ya taba zuciyarshi. Cikin kankanin lokaci idanuna suka kada sukai ka, muryata a zafafe na fara tambayarta da cewa “Wa ya turoki ki zagi mahaifiyata?” Na fadi hakan ina qara damqe hannunta iya qarfina. A jikinta take jin jijiyoyin hannunta suna tsittsikewa ba ta san lokacin da hawaye ya fara tsiyayo mata ba saboda tsananin azaba. Kukanta ne ya daga mishi hankali don haka ya matso kusa da mu ya ce, “Ki yi haquri, ki samar mata hannu don Allah.” Ya fadi hakan idonshi yana kaina. Harara na watsa masa da dara-daran idanuna tamkar zasu fado kasa, sannan na yi mishi kallon ‘Kai kuma a su wa?’ go gefe kaban guri' A tsorace yaja da baya, hankalinshi a matukar tashe, a zuciyarsa yake Allah wadai da fitinar Yasmin. “Hajiya don Allah ki yi haquri ki sakar mata hannu.” Masu riqe mana kwanduna suka fadi hakan suna kusanto ni. “Duk wanda ya matso kusa da ni wallahi sai na kumbura mishi fuska.” Na fadi hakan da murya mai sauti, cike da hargagi da tsawatarwa. Hakan shi ya janyo hankalin su Safiyya da Rahma, da gudu suka biyo layin da suka jiyo sautin muryata a lokacin har mutane sun zagaye mu ana magiyar in sakar mata hannu. Ni kuma na kafe kan sai ta fada min wanda ya turo ta ta zagar min uwa. Rahma ce ta kama kafaduna ta jingina jikinta da nawa ita kuma Safiyya ta yi bismilla ta vanvare hannuna daga riqon da nayi wa Yasmin, Lumshe ido na yi na nufi hanyar ficewa daga kantin idanuna suna rufe. Rahma ce ta tura siyayyar tawa zuwa gurin biyan kudi, ita kuma Safiyya ta rufa min baya muka fice daga kantin. Yatsu biyu ta sanya a baki ta hura ya fitar da qara mai tsananin qarfi tamkar an hura usir (hakan da ta yi inkiya ce da take isarwa da sauwan ‘yan’uwanmu cewa su fito daga cikin kantin an samu matsala) minti daya tsakani duk suka fito daga cikin kantin zuwa gurin biyan kudi, Sai da ya gama total din kudin kayan da na muka dauka gaba daya, sannan ya kalle ta ya ce “Hajiya an biya kudin kayan, don haka kuna iya tafiya…” Kafin ya qarasa abinda ya yi niyyar fadi, Rahma ta cakumo wuyan rigarshi tana fadin “An fada maka maula muka zo shagonku?” Kafin ya amsa ta qara juyo qara irin wacce tayi dazu daga waje, hakan shi ya tabbatar mata da cewa tabbas akwai matsala babba daga gare ni. Ba shiri ta sakar mishi wuyan riga ya ja gefe yana maida numfashin wahala, Kallon kwandunan siyayyar namu ta yi gaba daya, a ranta ta qiyasta kudi kayan gaba daya, Dalar amurka ta ciro daga aljihun wandonta ta zaro masu yawa wadanda idan canji za a yi zasu kai dubu dari biyar, ta dora a teburin gabanshi ta ce “Idan ka canja ina da tabbacin zasu kai dubu dari biyar” Tana gama fadin haka ta yi musu inkiyar fita daga kantin, hannayensu janye da kwandunan siyayyar, yaran kantin suna biye da su don amso kwandunan. Kusa da inda na yi parking din motata suka hangi taruwar jama’a maza da mata, Da hanzari suka juye siyayyar a cikin but din motocin da suka hawo zuwa kantin sannan suka nufi kusa da motar tawa don ganin abinda yake faruwa. Safiyya tana zaune dirshan a qasa ni kuma ina kwance magashiyan tamkar matacciya, ta dora kaina a jikinta tana hawaye, Tunda take zaune tare da ni ba ta taba ganin hakan ba duk da dai tana tunanin akwai wani babban al’amari a tattare da ni, Fuskokin mutanen gurin kawai za ka kalla ya tabbatar maka da matsanancin tsoron da suke ciki, abu Kamar almara don dai kawai a gabansu ya faru. Awa daya baya na wuce cikin kantin cike da ban sha'awa, duk Namijin daya ganni ba wanda baiyi sha’awar in kasance matarsa ba, amma kuma ina fitowa ganin idonsu na yanke jiki na fadi kusa da mota ta, abu mafi tsoratar dasu shine, duk wanda ya kusanto garemu da niyyar taimakawa Safiyya ta sanya ni a mota sai turiri mai matuqar zafi da yake fitowa daga jikina ya komar dashi baya, daga bisani kuma sai wani farin haske ya zagayemu ni da Safiyya duk wanda ya matso sai hasken ya komar dashi baya, don haka duk sai suka zubawa sarautar Allah ido, suna kallonmu amma basu da ikon taba mu. “Bisimillahir Rahmanir Rahim.” Abinda Rahma ta furta kenan ta nufomu ba tare da wani tsorata ba a tattare da ita. Ga mamakin mutanen gurin ba abinda ya hanata isowa garemu, hannuna ta riqe sannan ta durkuso da fuskarta zuwa gareni ta ce, “Mu saka ki a mota?” Ina jin abinda duk yake faruwa, maganace dai bani da ikon yi don haka na daga mata kai alamar “Eh.” Nan take suka sanyani cikin motar da nazo da ita suka kwantar da ni a bayan motar, Rahma ta shiga gaba mazaunin direba ta tayar da motar ta fice daga harabar gurin su Safiyya suka ruufa mata baya a tasu motocin a guje. *** Duk irin gunjin kukan da take yi da majina tana ihun hannunta zai tsinke bai tanka mata ba, matuqar haushinta yake ji, tamkar ya shako ta ya tsinka mata mari, duk abinda ya faru itace sila, ita ce hatsabibiya wai a dole mai kishin masoyinta. Shi abinda yafi tsaya mishi a zuciya ma abinda ya faru da yarinyar, duk abinda ya faru da akan idonshi ya faru, kanshi sai caji yake yi, ya rasa waqar farawa, ga kukan Yasmin dake qara qona mishi zuciya, amma acan qasan ranshi yana jin matsanancin ciwo na rashin sanin halin da yarinyar take ciki. “Me yake damun ta da har ta faxi a qasa? A wane hali take ciki a yanzu?” Wadannan duk tambayoyi ne da yake buqatar amsarsu daga gareta amma kuma bai da tabbacin ko zai sake ganinta. Yana ajiye motar bai saurareta ba ya wuce zuwa can bangaren da ake sauke shi idan ya kawo ziyara gidan qanin mahaifinshi, kuma surukanshi mahaifan Yasmin. Tun daga harabar gidan take rusa ihu harta dire a tsakiyar falon gidan, birgima ta fara yi tamkar qaramar yarinya, tana ihun fadin hanunta zai tsinke. Bata taba tsammanin yana gidan ba don lokacin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27