Chapter 15
Chapter 15
ba, ya afka cikin falon yana dan muzurai na rashin gaskiya yana zare idanu. Kallon kallo suka yi harna tsawon minti uku, ita bata ce mishi ba shi baice mata ba, wanda hakan yayi matuqar sanyayar masa da jiki, kwarjinin tsohuwar ya cika masa fuska don haka ya zame zuwa qasa yana gaisheta ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba. “Matarka Allah yayi mata rasuwa! kwanaki hudu da suka wuce, dawowarka na tsaya jira don in sanar da kai, da ba ka zo ka tarar dani a gidan nan ba, ga yarinyar da ta haifa maka, na rada mata suna Aysha. Kana iya qare mata kallo harna tsawon awa guda, don da ita zamu wuce zuwa gidana, kamar yanda mahaifiyarta tayi min umarni. Tana gama fadin haka ta miqa masa ni bayan ta kwantoni daga bayanta. Zuciyarshi ta girgiza matuqa da rasuwar mahaifiyata, amma da yake namijin duniya ne ko qwalla bai yi ba, kuma sam bai alqanta rasuwar tata da laifinshi bane. A zuciyarshi yake hasaso kalaman rainin wayon da ikon da tsohuwar nan take neman gwada masa akan ‘yarshi, don haka a ranshi yake fadin “Ma ji ma gani….” Zirga zirgarta kawai take daga kichin zuwa daki ba tare da ta qara kallonshi ba, tana gama girkin abincin da take yi ta sake a kula ta zura hijabinta ta nufo gareshi ta ce, “Ba ni ita nan, zamu wuce.” A fusace ya dago kanshi da niyyar yi mata korar kare duk da dai idan ta tafi bai san yanda zai yi da ni ba, amma ya gwammace ko gidan marayu ne ya kaini. suna hada ido da ita wani mugun tsoronta da kwarjininta ya bugi zuciyarshi, ba shiri ya miqa mata ni hannunsa har rawa yake yi gurin miqanin. Tana gab da ficewa daga falon ta juyo ta ce, “Gidana shi ne na qarshe a wannan layin daga bangaren dama, idan ka yi niyya duk abin da ka siya mata kana iya kawowa a matsayinta na diyarka.” Tana gama fadin haka ta fice, daman tun safiyar ranar ta nemo almajirai suka kwashe duk wasu kaya da yake mallakina da nata zuwa can gidanta da yake qarshen layi. *** Kwanan mahaifina uku a gida yana zaman makokin mahaifiyata shi kadai, ba abinda yake fitar da shi sai sallah, a can masallacine maqwabta suka yi mishi gaisuwar Ummata, a kwana na hudu ne da dawowar shi ya shiga kasuwar barci (Kasuwar saida gwanjo a garin Kaduna) ya ciko jakar gana must go guda da kayan jarirai ‘yan naira ashirin zuwa talatin, sai da ya kashe dubu biyu da dari biyar, yana siyan kayan yana cije baki shi a ganinshi ya yi mugun qoqarin azo a gani. Rabon da ya kashe dubu daya a cikin kudinshi har ya manta, amma yau ya kashe dubu biyu har da dari biyar, sannan yaje ya sai geron kunu mudu uku da sukari rabin mudu, a nan ma dai sai da ya kashe dari biyar, ya hada lissafi gaba daya dubu uku. Yana tuka ‘yar mota starlet din da Alh. Buba ya sai masa ya ke tunanin lallai wannan rana tana daga cikin ranakun tarihi a rayuwarsa, tun da har ya iya kashe dubu uku, cikin kudinshi. Yana zaune a kan luntsuma-luntsuman kujerun da suka zagaye tafkeken falon tsohuwar da ko sunanta bai sani ba, da kwarin gwiwa yake wasa da hannuna, don yana ganin ya yi abin a zo a gani. Tana zaune a can gefe guda akan kujera, a gabanta ta zazzage duk kayan daya kawo tana daddagawa daya bayan daya, tana yamutsa fuska. Daga qarshe ta tattara duk kayan ta maida cikin gana must go din ta zuge zif din ta rufe kamar yanda ya shigo da jakar, tana kallon ledar ta gane abin da yake ciki saboda irin mai zane zanen nan ce. Kallon shi take na tsawon mintuna uku shi kuma idanunsa yana kaina, a ran shi ya ke ta mamakin irin blawus masu tsadar da ake sanya min. “Yanzu Sa’ad ka rasa abinda zaka siyowa Aysha a matsayinta na ‘yar jaririyar diyarka kuma ita kadai da ka mallaka a duniya sai wadannan gwanjunan?” Shiru ya yi bai amsa ba illah qara durqusar da kanshi qasa da ya yi, a ranshi ya na jin qunar kalamanta amma ko idanu ya kasa hadawa da ita balle har ya iya mayar mata da martani. “Allah ya wadaran wannan dukiya da kake tarawa tunda kai kan ka ba ka iya amfanawa kan ka balle har ka amfanarwa wani naka, kar ka manta mutuwa za ka yi ka bar dukiyar kuma duk sonka da su a nan duniya zaka bar su.” Tana gama fadin haka ta je har gaban shi ta karbe ni ta juya da nufin shigewa bedroom dinta, har ta kai bakin qofa ta juyo ta kalleshi tace, “Ka tattara tunmokaranka ka tafi dasu, kuma daga yau matuqar irin wannan tsummar zaka kawowa Aysha to mun yafe maka.” Ya dauki tsawon minti talatin a zaune yana tufka da warwara shi kadai, daga qarshe ne ya yi qarfin halin miqewa ya dauki jakar kayan da geron ya fice. *** Tun daga wannan ranar mahaifina ya yanke shawarar daina ziyarta ta, duk wani ragamar hidimata ya barwa wannan tsohuwa, ita kuma hakan bai taba damunta ba, sai da na yi wata shida sannan ya sake kawo mana ziyara a tsaitsaye, a lokacin ganina da yayi ina tsayuwa gwanin ban sha’awa yaji matuqar mamaki, babu wani alamun da zai nuna cewa ina shan wahala, riga da wando ‘yan kanti masu matuqar tsada da kyau a jikina, anyi min kalba a gashina mai tsawon da Allah ya bani. Tun daga lokacin ya koma baya kawo min ziyara sai bayan wata shida duk da cewa gidaje biyar ne a tsakaninmu, ita kuma tsohuwar nan bata qara taka gidan mahaifina ba tun da ta daukoni ina jaririya. A haka har na shekara goma a duniya, a lokacin duk wani siga ta kyau ya fara bayyana a jikina, ina da matuqar wayau da hangen nesa da qwaqwalwa tamkar ‘yar shekara goma sha hudu. Kuma Duk tarihin rayuwata na sani ne ta bakin wannan tsohuwa, kuma ta yi min ishara da mutumin da yake zuwa gidanta duk bayan wata shida shi ne mahaifina. Na taso cikin wata iriyar rayuwa ce mai rikita tunanin mai tunani, Abin da zai baku mamaki shine tun da na fara wayo ban san wasu mutane ba, daga wannan tsohuwar dana girma a gurinta, sai kuma yaranta ‘yan biyu duk mata da suke kawo mana ziyara duk bayan kwana biyu, Sai kuma mutumin da aka kira mahaifina da yake kawo mana ziyara duk bayan wata shida. Babu abinda muka nema muka rasa, amma kuma ban taba ganin lokacin da wani yake kawo mana kayan abinci ba, duk abin da naso ci shi nake ci, sutura kuwa ni kaina ban san iya yawan kayan sawan da nake da su ba, kuma duk kananan kaya ne masu tsada. Hassana da Usaina (yaran tsohuwar nan) suna da matuqar sona, su suke min komai na daga kitso, wanka, wanke kai, yanke farce, koya karatun boko dana arabic. Suna da ilimi sosai, duk ilimin da nake dashi daga garesu na samu ban taba taka makarantar Islamiya ko
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27