Chapter 16
Chapter 16
boko ba. Ina shekaru goma sha biyu a duniya Allah ya dauki ran tsohuwa Zahra’u, duk zaman da na yi da ita sai a ranar na san sunanta, daga bakin wani farin dattijo mai dogon gemu daya biyo su Hassana zuwa gidan mu. Shi ne mutum na biyar dana taba gani a rayuwata, su Hassana suna kuka suke nuna masa ni, ina rungume kan gawar tsohuwar ina shessheqar kuka, ina kiran don Allah ta tashi, kar ta tafi ta barni. Da matuqar tausayi a fuskarsa ya kamo hannuna, sannan ya jani zuwa jikinsa, wata addu’a ya tofa min a tsakiyar kaina, minti biyu tsakani barci mai nauyi yayi awon gaba dani. Ban tashi farkawa ba sai a wani daki na daban da ban taba gani ba a rayuwa ta, mutumin da aka kira mahaifina yana zaune a gefen gadon da nake kwance yana kallona, fuskarshi ba walwala ko kadan, balle in sa ran kallon kauna da tausayi irinna ‘ya da uba. “Me ya kawo ki gidan nan?” Sai a lokacin na gane cewa a gidan mahaifina nake, tuno rasuwa tsohuwar yasa na fara hawaye, da sanyin murya na ce masa. “Allah ya yiwa Ammi rasuwa.” Dan haka muke karanta, ni da su Hassana “Allah ya jikanta.” Ya fada cikin tabe baki, saboda tsabar rashin imani da tausayi irin nasa. “Ta ina kika shigo gidan nan?” Da mamaki nake kallosa, tsabar haushi da baqin ciki yasa na yi masa wani kallon mugun tsana sannan na ce. “Ni da gidan ubana har sai na nemi izinin shigowa?” Ba shi da na fadawa magana kadai zuciyarshi ta buga ba, hatta ni da na yi maganar sai da zuciyata ta buga saboda tsoro, Kallon shi nake qyam da idanuna na kasa bari bugawar zuciyata ta bayyana a fuskata. Matukar mamaki ne ya kama shi, don tsayawa ya yi baki da hanci bude yana kallona, muka yi musayar kallo na wasu ‘yan daqiqu, kowa da irin abin da yake sakawa a zuciyarsa. “Irin tarbiyyar da ta koya miki kenan?” Ya fada yana zare min ido fuskarshi ba walwala, bai bani damar furta komai ba ya ci gaba da cewa, “Ni mahaifinki ne, don haka ba zan dauki iskanci da rashin kunya ba, dole ki saisaita kalaman bakin ki idan za ki yi magana dani, matuqar kina son mu daidaita, idan kuma ba haka ba zan dauki mummunan mataki a kan ki.” Yana gama fadin haka ya sa kai ya fice daga dakin ba tare da ya kara kallon inda nake zaune ba. Tabe baki nayi cikin rashin nuna damuwa da barazanar da ya yi min, a zuciyata na ce, “Wallahi babu wanda ya isa ya takuramin, mu zuba ni da kai.” Sannan na yi qwafa na fara bin dakin da kallo. Abin da ya bani mamaki shine, Komai da yake cikin dakin kamar gado da madubi da jakunkunan kaya duk nawane wadanda nake amfani da shi a gidan tsohuwa Zahra’u, har da karin wasu sabbin jakunkunan manya-manya wadanda ban san ko mene ne a ciki ba. Yunwa nake ji don haka na miqe don in samarwa kaina abinda zan ci, idona ne ya fada kan agogon bango dake maqale a dakin, karfe biyar da kwata na yamma, wannan ya tabbatar min akwai bashin sallar azahar da la’asar a kaina wanda ban yi ba, don haka na fara tunanin yanda zan tambayi mahaifina ina ne ban daki? Ina fitowa daga cikin dakin dana farka barci naga wani qofa a kusa da gurin, don haka na bude da tunanin ko bandakin ne? Ganin shine yasa na yi murmushi domin na tsani hurdar da zai hadani da wancan mutumin (mahaifina). Ina zaune akan sallaya bayan na idar da sallar la’asar, hawaye ne mai zafi yake bin fuskata, ba kowa da komai nake tunawa ba illa tsohuwa Zahara’u, da rayuwar farin cikin da na yi a gidanta. Amma wai yau gani a gidan mutumin da sam bai damu dani ba, kuma a hakan zan ci gaba da rayuwa har Allah ya kawo min mijin aure in bar qarqashin kulawarsa. Addu’a nake ina shassheqar kuka ina nema mata gafara a gurin Allah madaukakin sarki, turo qofar dakin da aka yi ba tare da sallama ba yasa na dago idanuwa ina kallon mai shigowa. Yana tsaye riqe da wani dan qaramin kofi da wasu qulle-qulle a hannunsa, nan take na shafa addu’ar ina goge hawayen fuskata da hijabin sallata. “Ga abincin ki nan! Ban san da dawowarki ba don haka shi kenan ragowar garin da ya ragemin a gidan nan! A niyyata daman shi zan sha yau sai gobe idan na fita in auno wani, don haka tun da kin dawo ni na haqura ki sha kawai, ga quli-quli da ragowar suger nan na san zai isheki zuwa gobe.” Tunda ya fara maganar nake kallon bakinsa bana ko qiftawa, domin ko kadan ban fahimci mai yake nufi ba, na ji yana batun gari da quli-quli da suger, na san dai suger domin muna amfani da shi ko a gidan Ammi, gari kuma qila yana nufin garin tuwo ne na semovita wanda tsohuwa take tuqa mana tuwo dashi lokaci zuwa lokaci, amma abin da ya kira quli-quli ban taba jin sunansa ba tun da aka haifeni. Domin in tantance ko meye yasa na matsa zuwa gabansa na amshi kofin da ledojin don in gani ma idanuna, da cokalin cikin kofin na ringa juya abin da ya kira gari ina ayyana yanda zai dankare min a cikin cikina matuqar na kuskura nasha wannan abin, dunqulallan abinda ya qira quli na ringa kallo da ido ina mamaki, daga bisani na kara a hancina don a zatona kashi ne aka shanya ya bushe, rashin jin wari yasa na gane ba kashi bane wani abin ne daban! “Baba mene ne wannan?” Na tambaye shi ina nuna masa garin da quli-qulin. Ya kai maqura wajen zuciya da fusata, jira yake a ce qyat ya yi bindiga, don haka ya bani amsa da cewar "Ubanki ne.” “Daga tambaya sai zagi? Ni fa wallahi ban san ko me ye wannan ba, don ban taba ci ba, ni ban ma taba ganin irinshi ba" “Shi uwarki taci ta rayu har ta haifeki.” Bai bari na ajiye numfashi ba ya bani amsa da hakan, yana numfarfashi, kamar zai rufeni da duka. Jin ya fara ambato uwata dake cikin kabari yasa raina ya fara baci, ina sonta duk da ban yi rayuwa da ita ba, na kalleshi tsawon daqiqu kafin nace, “Ni kam wallahi ba zan ci abinda na tabbatar ba zai narke min a ciki ba, wadannan irin muggan abincin daka ringa turawa mahaifiyata shi yayi sanadin mutuwarta, bayan Allah ya taimaketa ta haifeni...” “Ni kike fadawa wannan maganar?” Hanunsa ya dago da niyyar wanke fuskata da mari. Ganin hakan yasa na rintse ido ina jiran saukar mari a fuskata, karo na farko da wani hannu zai sauka a jikina da niyyar duka, Minti daya biyu ban ji saukar marin ba don haka na bude ido don ganin abin da ya dakatar da shi. A tsaye yake, sai zufa yake ketowa daga kowace qofar gashi na jikinsa, hannunsa kuma miqe a iska ya tsaya qyam kuma daf dani da niyyar marina, qoqari yake ya maida hannun nasa baya ko kuma ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27