Chapter 8
Chapter 8
ne abinda ya faru tsakanina da ita a daren jiya, da kuma rayuwar shan kayan mayen da na daukar wa kaina ina ‘yar qaramar yarinya. Babbar matsalar shi ne, na yi mata kashedi a kan duk abinda za ta gani a tare da ni. “Amma… a juri zuwa rafi…” Tana fadin haka ta janyo bargo ta lulluba min, cikin tausayi da qauna ta da take ji a zuciyarta. Karatun Alqur’ani ta jiyo yana tashi cikin tattausan sautin muryar “Ahmad Sulaiman” a falo, don haka ta nufi can. Duk su shidan da bata san sunayensu ba in banda “Rahma” da taji na kira sunanta jiya, sai kuma “Baba” da na ba ta umarnin ta shirya mata abinci a jiya, suna zazzaune a kan kujeru daban-daban. Har qasa ta tsuguna ta gaida Baba, ta amsa mata da fara’a har tana tsokanar ta; “Ya kuwanan baqunta?” Murmushi kawai ta yi sannan ta yi jam’in gaida su gaba daya. “Akwai abinda kike buqata ne?” Safiyya ta tambaye ta tana kallon ta cikin kulawa. “Alhamdulillahi, ba na buqatar komai, na gode.” Ta mai da mata da amsar hakan bayan ta fadada fuskarta da murmushi. Qarfe ara da rabi Baba ta gama hada kayan karin kumallo a kan dinning table, suna zazzaune akan qananan kujeru zagaye da babban teburin da aka shirya kayan abinci. Kowa a cikinsu qoqarin hada kumallonshi yake yi, sabanin ita da ta zabga tagumi hannu bibbiyu. Abinda ya kara bata mamaki har ya sanya ta tagumi shi ne ganin dukkaninsu babu wanda ya damu ya duba yadda na tashi. Kuma ko ita da muka kwana muka tashi daki daya ba su tambaye ta ya nake ba, qoqarin cika cikinsu kawai suke yi bayan kuma a yadda ta lura nice shigaba a cikinsu. “Ya dai Fatima? Ko kina buqata wani abin karyawar ne daban?” Baba ce ta yi mata wanan tamvayar da damuwa a fuskarta, ganin kowa yana cin abinci amma ban da ita. “A’a, ..yanzu zan hada nawa” Ta amsa tana qoqarin bude gwangwanin madara da cokalin hannunta. *** Sanye nake da singlieti fara wacce ta yi matuqar dacewa da fatar jikina, wando na sanya three-quarter amma yana da fadi bai kama min jiki ba, duk wani lungu da saqo na jikina fidda kalar qamshi daban yake yi don haka zai yi wuya mutum ya iya tantance wane irin turare na fesa. Qarfe sha daya da minti arba’in da biyar agogon falon ya nuna min. tsawon awa hudu ina barci, Minti arba’in da biyar kuma na dauka gurin wanka da shiryawa, Ganin fitowata falon ya sa dukkansu gyara zama suna min barka da fitowa. Gaban Baba na wuce na tsuguna har kasa na gaisheta sannan na nemi gurin zama. Hada baki suka yi gurin gaishe ni, na amsa da murmushin da bai cika yankewa a fuskata ba. “Ya dai Fatima? Ina fatan baki takura ba?” na tambayeta bayan na lura da kallon da take ta bina dashi tun bayan fitowa ta. “Kin tashi lafiya?” abin da ta tambayeni kenan, ta share waccen tambayar da na yi mata. “Alhamdulillah.” Na amsa mata ina dan dariya don in kara kwantar da hankalinta. “Sadiya taimaka ki hada min ruwan lipton. Rahama bani remot din T.V pls.” Da sauri suka miqe don cika umarnin da na basu duk da na yi umarnin ne cikin salon roqo. “Zamu fita yammacin yau don samawa Fatima duk abinda zata buqata, so kowa ya kasance cikin shiri zuwa qarfe biyar na yamma. Fatima ki yi lis din duk abinda kike buqata.” “Toh! Na gode, qwarai.” Ta amsa min. "GA CIKAKKUN LABARAN DUNIYA.. A jiya da daddare ne wasu ‘yan bindiga mata da ba a san ko su waye ba suka kai hari wa gidan yarin da yake hanyar Kaduna zuwa Abuja, Sun yi amfani da bindiga gurin harbin qafafun mutum shida daga cikin jami’an tsaron da suke gidan, sannan suka zarge qafafun mutum tara daga cikin jami’an tsaron, mutum biyu kuma a can bayan gidan aka gansu kwance suna sharar barci sakamakon hoda mai sanya nannauyar barci da ‘yan matan sukayi amfani dashi. Sunbi jami'an tsaron gaba daya sun shaka musu hodar, hakan yasa har yanzu da suke kwance a kan gadon asibiti na SALAMAT ba su san inda kansu yake ba. ‘Yan bindigan dai ko da suka sami nasarar shiga gidan basu dauki kowa ba sai wannan mai laifin Fatima Ibrahim wacce aka kaita gidan a yammacin jiya, sun yi amfani da dan mabudi mai lalata ko wani irin kwado ne gurin bude qofar dakin da fursunan take, kuma sunyi umarni ga duk matan dakin su kama gabansu idan suna buqata. Wata mata mai suna Hajara Musa daga cikin fursunonin da suka fice daga dakin amma ba ta yi nisa ba ta suma a hanya ita ce ta bayyana hakan bayan farfadwarta, ga yanda ta bayyanawa wakilanmu faruwar al’amarin. (Take aka dallaro hoton fursunan a fuskar talabijin) Dan jaridan ne ya fara tambayarta da cewa, “Ya sunan malamar?” “Hajara Musa.” Da alamun galabaita a muryarta, fuskarta da jikinta ma sun nuna gajiyawa. “Ya aka yi wannan al’amarin ya faru tunda kina cikin fursunonin da komai ya faru a gabansu?” “Muna cikin barci muka fara jiyo harbin bindiga daga can bayan gida, daga bisani kuma muka ji shiru, minti goma tsakani muka ci gaba da jin harbe-harben ba qaqqautawa, sai kuma can muka ji ana bude kwadon qofar dakin mu, tsananin tsaro yasa duk muka miqe tsaye, fursunar da aka kawo ta jiya ne kawai ba ta miqe ba, tana zaune tana kuka, wasu ‘yan mata muka gani sanye da riga da wando, sun rufe fuskarsu da manyan tabarau, kai tsaye gurin wacce take kukan suka nufa, sun dan yi maganganu a tsakaninsu daga bisani suka kama hannun junansu suka fice da ita.” “Kun ji maganganun da suka yi da ita?” “A’a, qasa-qasa suke magana.” “Yanzu idan kika ga ‘yan bindigan za ki shaidasu?” “A’a, lokacin a rude muke, ba zan iya gane fuskar ko daya daga cikinsu ba.” “Su nawa ne ‘yan matan?” “Ban yi tunanin qirga yawansu ba, amma a hasashe na za su kai su goma.” “Me yasa duk sauran ‘yan dakinku suka gudu, kema kin yi niyyar guduwa Allah ne bai baki sa’a ba.” Duqar da kanta ta yi na wasu ‘yan sakanni sannan ta dago hawaye na bin fuskarta ta ce, “Su suka ce duk mai buqatar gudu qofa a bude take.” “Kin san hukuncin wanda ya yi yunqurin gudu daga gidan yari kuwa?” Shiru ta yi ba ta amsa ba, bai gaji ba ya qara tambayarta da cewa “Tun tsawon wani lokaci kike zaune a gidan nan?” “Watanni uku da suka wuce…” “Me kika yi har aka yanke miki hukuncin zama a gidan yari?” Shiru ba ta amsa ba (sai kuma suka dauke hoton hirar) Wakilin namu ya sake zantawa da I.G na ‘yan sandan jihar Kaduna, in da ya tabbatarwa da wakilin namu cewa (nan take suka hasko hoton inspector general din tare da 'yan jaridu a cikin gidan yarin. “Ranka ya dad'e me zaka iya cewa akan wannan abin da ya faru?” “Wannan shi ne karo na farko da hakan ya tava faruwa da wannan gidan yarin, kuma abin mamaki ne qwarai da muka ji cewar mata ne ‘yan bingidan ba maza
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27