Chapter 3
Chapter 3
qwayar idanuna a kanki to tabbas sai na biya buqatata. Gobe Daddy zai dawo gidan nan donhaka kwana biyu na baki ki yanke hukunci a ranar da Daddy ya koma gidan Momy zanzo danjin shawarar da kika yanke” ba tare da ya qara kallota ya fice da ga falon. Tofa! In ka ji qi gudu sa gudu ne bai zo ba, tsawon minti arba’in batasan a wace duniyar ta ke ciki ba dawowa hayyacinta ta yi ta ganta zaune dirshan a kan kafet xin da ya malale tsakiyar falon. A ranar idan ta ce tayi barci to tabbas ta yi qarya, duk qwarewar sarkin varayin gurin satar mutane a ranar bai yi nasarar satarta ba, daga qarshe ta xauro Alwala ta fara jera nafilfili tana kai kukanta da Ubangijin talikai. Har Alhaji Muhammad ya bar gidan ta rasa mafitar da tafi dacewa a tsakanin zavin da Nasir ya bata, Alhajin da kanshi ya fahimci bata cikin walwala kuma ya tambaye ta amma ta kasa sanar dashi gaskiyar abinda yake damunta. Tun qarfe shida da yamma ta kulle get xin gidan da qofar falonta, a tsammaninta ta kuvuta daga zuwan Nasir, don ko yazo zai koma tunda gidan yana rufe ne. fitowarta kenan daga wanka misalin qarfe takwas da rabi na dare, taji kamar hayaniyar T.V take jiyowa daga falonta, don haka ta xora hijabi akan towel xin da take xaure dashi ta fito zuwa falon. Yana hakimce akan kujeara yana karkaxa makullin motar mahaifinshi wanda ya ke haxe dana qofar get xin gidanta dana qofar falonta, hakan shi ya ba ta tabbacin inda ya samu makullin cak ta tsaya tana kallonshi ta kasa furta ko kalma xaya. “Babyna…” shiya katse mata tunanin da take yana mata kallon qurilla tamkar zai cinyeta. “Me ya kawo ka gidannan?” Ba tambayeshi fuskarta ba walwala ko kaxan, saida ya xan ja fasali kamar bazai yi magana ba sannnan ya ce, "Amsar buqatata nazo ji” “Ni ba irin ‘yan iskan matan daka saba hulxa da su bane, ka je can ka samu dai dai dakai ni matar mahaifinkace ko mun rabu dashi aure ya haramta a tsakaninmu kuma ba zan tava yin zina da aure na ba, don haka karka qara zuwa min da zancen banza.” Ta fadi hakan muryanta cike da masifa, idanunta a kankance. “Kin manta abinda na faxa miki rannan koh? To wallahi bazan tava haqura dake ba, ko da tsiya ko da arziqi sai na cimma burina a kanki kinsan irin azabtarwar da nayi a kwana biyun nan kuwa? To wallahi sai kin haxa jikinki da nawa a gobe goben nan.” Ya fadi haka cikin nuna rashin damuwa da masifa da take mishi. “Qarya kake Nasir Allah bazai tava barinka ka cimma qazantacciyar manufarka a kaina ba, kuma idan baka janye wannan maganar ba zan kira mahaifinka in sanar da shi duk abinda kace.” “Wannan shine babban kuskuren da zaki tabka a rayuwar ki kin manta irin son da iyayena suke min ne? ko kin faxa musu wallahi bazasu tava yarda ba, a qarshe sai dai ma ki janyowa kanki wani bala’in don zan tabbatar musu da cewar tunda na dawo qasar nan kike bibiyata, don naqi amincewa buqatarki ne kikai niyyar shiga tsakanina dasu.” Ya qara matsawa dab da ita, ita kuwa ta fara ja da baya har sai da ta qure da jikin bango yana kusantar ta. Hannu biyu yasa ya dafa bango ya tare ta a tsakiya, fuskarshi ya matsar dab da ta ta sannan yace, “Kinsan kuma tsab zasu yarda da abinda nace, don ana canza mata amma ba’a canza da, kiyi tunani ki samu nutsuwar yau gobe zan dawo in kashe qishirwata.” Daga haka bai qara furta komai ba ya fice ya barta tsaye a gurin kamar mutum-mutumi. yau kam kasa yin sallar ta yi kawai sai ta rushe da kuka mai tsananin qarfi tsawon awa biyu tana kuka wa wannan mummunan al'amari da ke tunkarar ta, daga qarshe sarkin varayi ya yi awon gaba da ita a tsakar falon. Washe gari ba abinda ta iya hassalawa a gidan jikinta sanyi qalau tana kwance akan kujera tana jan carbi, lokaci zuwa lokaci gabanta yana faxuwa tanajan “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” har Alhaji ya shigo ya dubata kamar yadda ya saba idan ba’a gidan ya kwana ba. “Bana jin daxi ne” amsar da ta bashi kenan lokacin daya matsa da tambayar abinda ke damunta. “Zan turo Nasir ya kaiki asibiti” ya faxi hakan yana ficewa da sassarfa don karya makara zuwa Office. Ganin zaman bazayyi mata ba yasa ta miqe ta nufi banxaki da niyyar watsa ruwa ko zata ji qarfin jikinta. Heater bayinta ya lalace kuma ta manta ba sanar da Alhaji ba don haka ta ciko bokiti da ruwa ta jona a jikin soket abayan kujera a falon, tana zama Nasir ya shigo ba tare da sallama ba, kallonshi tayi sama da qasa yana sanye da qananan kaya jeans da T.shet. “Oh My God! Babyna wai baki da lafiya inji Daddy?” ya faxi hakan yana kusantar ta nufinshi don jin yanayin jikinta. “Dakata Nasir, karka kuskura ka matso kusa dani.” Ta yi mishi gargaxin hakan muryarta tangaran babu alamar rashin lafiya a tare da ita cak ya tsaya tamkar an riqe shi, shi bai qarasa kusa da ita ba kuma bai koma baya ba. “Kina tunanin akwai abinda zai hanani biyan buqata ta dake a yanzu?” “Qwarai kuwa” ta faxa muryarta babu alamun tsoro ko kaxan. “Meye shi?” ya tambaya da tsananin mamaki a fuskarshi. “Allah bazai baka nasara a kaina ba.” Dariya ya qyalqyale da shi tamkar sabon hauka sannan ya qara kusantar ta da niyyar haxa jikinta da nashi ko ta halin qaqa. “Dakata” ta sake bashi umarnin haka a karo na biyu lokacin baifi saura taku biyu ya isa gareta ba, bayyi niyyar tsayawa ba amma ga mamakinshi sai ya tsaya. “Bani minti biyar inyi wanka…” ta faxa sannan ta rava ta gefenshi ta wuce zuwa bayan kujera inda ta jona heater. “Fatima shure shure ba ya hana mutuwa duk abinda zakiyi yau sai na biya buqata ta a kanki, don haka jeki dawo ina jiranki” yana gama faxin haka ya zauna akan kujerar da ta tashi yana qyalqyala dariya. Idanun shi kaxai ta kalla ya tabbatar mata da cewa tabbas yau da gaske yake don haka gara ta nemi mafitar qarshe tun kafin wankin hula ya kaita dare, ruwan yana tafarfasa don ya haura minti talatin da jonawa, tana xaukar ruwan a bayan kujerar da yake zaune ta xaga bokotin ta sheqa mishi tun daga tsakiyar kanshi ba tare da ya ankara ba. Raxaxin da ya ji tun da ga tsakiya kanshi zuwa sassan jikinsa yasa ya qwallah gifitaccen qara saboda azaba, second goma tsakani ya sume akan kujerar sai a lokacin ta ji dana sani mai tsanani ya mamaye zuciyarta jikinta ba inda ba ya rawa saboda tsabar tsoro. Tsawon minti biyar ta rasa waqar farawa sai kuka take tana safa da marwa a tsakiyar falon, daga qarshe ta yanke shawarar kiran number wayar Alhajin, kuka kawai take a wayar tana faxin Alhaji Nasir ne…..” “Me ya faru da Nasir din…..?” Ya tambaye ta hankalinshi a tashe. Ta kasa furta komai bayan sai kuka daga bisani ta jefar da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27