Chapter 27
Chapter 27
qoqarin lalubar kwayar idanuna. “Don girman Allah ki bani aron minti biyu daga cikin lokacin ki.” Kamar daga sama na jiyo sassayar muryarshi ya daki dodon kunnena, lokaci na farko a rayuwata dana ji wani abu mai kama da ruwan sanyi ya tsirga tun daga tsakiyar kaina har zuwa kan babbar yatsar qafata. Abu mafi ban mamaki shine na kasa tankwabar da roqonshi, saima sanya hannu danai na kashe motar, na jingina bayana da kujera ina kallonshi, alamun shi nake saurara. Da murmushi a fuskarshi yake kallona, ni kuwa Fuskata a d'inke take, babu walwala ko kadan. “Sunana Abdul-Ahad Muhammad, don Allah ya sunan ki?” Hango tahowar Hajiya Danasha da nayi da saurinta ya sani sakin wata wawiyar ajiyar zuciya, don ji nake tamkar bani ba, duk yanda naso in share lamarin wannan Abdul din zuciyata taqi bani hadin kan haka. “Sunana Aysha…” Na fada da sanyin murya. Sannan na bude kofar motar na zuro kafafuna waje. A daidai lokacin Hajiya Danasha ta karaso gare ni. “Ranki ya dad'e, barka da isowa. da girman kujeranki sarauniyar kyawawan ‘yan mata na duniya…” karad'in Hajiya Danasha kenan daya cikamin dodon kunne, dan kallonta nayi, sannan na saci kallon Abdul, sai na fito daga motar gaba daya. “Tabbas ta cancanci kirari fiye da haka" Ya fada a zuciya yana bin hannuna da na rike makullin mota da kallo. Ina fitowa daga motar Hajiya Danasha ta qaraso kusa dani, jikinta har rawa yake tana qoqarin rungume ni, lura da manufarta yasa na dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu tareda fadin “Haba Hajiya wannan ba girmanki ba ne.” Cak taja ta tsaya tana dariya cikin salon basarwa ta ce, “Yi haquri baby, tsananin farin cikin ganinki ne ya sa haka, don sam banyi tunanin zaki sami halarta ba.” Murmushi kawai nayi na ci gaba da kallon yanda ta cokara daurin gwargwaro tamkar wata qaramar yarinya ‘yar ishirin da biyu. “Zo mu shiga daga ciki koh? Duk an gama halarta tun karfe shida shi yasa na kara fitar da tsammanin zuwanki.” Yana tsaye a inda na bar shi har izuwa wannan lokaci, waya ce a hannun shi amma inda nake tsaye nan yake kallo da wayar tashi, don haka nai saurin juyar da kaina zuwa hanyar da zata sada ni da qofar gurin taron ina mai tsananin jin haushin kaina da har na sake kallon Abdul don ganin yana nan ko ya tafi. Qarar tsinin takalmin Hajiya Danasha da take bina a baya shine abinda yasa fuskata cika da murmushi, don haka har na shiga cikin gurin taron murmushin bai 6ace daga kan fuskata ba. Taro ne na manyan mata wanda ya hada jiga-jigai kuma qasaitattun mata ‘yan siyasa, da masu hannu da shuni wadanda ake kiran sunansu suna amsawa. Tun daga manyan jeap jeap din dana gani a gurin fakin din motoci ya tabbatar min ba qana nan mata ba ne agurin, amma ban qara tabbatarwa ba sai da na shiga cikin gurin. Idanuwa ne a kaina ba adadi tamkar zasu cinyeni danye, ban damu ba illa “La haula wala quwwata illah billah…” da na cigaba da ja a zuciyata, tuni na dauke murmushin fuskata na qara shiga cikin nutsuwa ta. Kamar mai tausayin qasa haka nake tafiya a hankali har zuwa kan high table kusa da kujerar Hajiya Danasha ta hannun dama inda ta nuna min a matsayin gurin zama na. Qus qus naga sun yi da wacce na ganta riqe da loudspeeker wacce da alama ita ce MC, lokaci daya na ji muryar mai gabatarwa ta cikin abin magana tana fadin "muna yi wa Aysha Azzahra’u sarauniyar kyawawan ‘yan mata barka da zuwa gurin wannan taro mai albarka” Idanuna suna qasa, na qi yarda in cigaba da hada idanu dako wace mace dake gurin, domin duk wacce na kalla sai inga tana jifana da murmushi, idan ma ba gizo idanuna sukemin ba sai naga kamar har signa sukemin tamkar saurayi ya ga budurwa. “Ya dai baby? Ina fatan ba ki takura ba?” wata qatuwar mata da take zaune kusa dani ta fadi haka tana qoqarin dafa cinyata. Kafin in yi wani yunquri ko in bude baki in bata amsa tuni hannunta ya sauka akan cinyata ta hagu, yanda ta yi saurin dauke hannunta daga jikina kamar walqiya shine abinda ya fi bani mamaki, don haka na kalleta ina murmushi, amma ita tuni ta hada gumi duk da sanyin A.C daya wadaci dakin taron. “A’a! alhamdulillah.” Amsar dana ba ta kenan a gajarce don ganin tana min kallon tsoro ba kamar dazu ba da take bina da kallon sha’awa. Minti biyu tsakani na nemeta daga kusa da ni na rasa. “Ta fi nono fari.” Abinda nace kenan a zuciyata naci gaba da saurarar M.C da take bada umarnin ko wacce mace ta zauna a inda take za’a kawo mata abinci. Wasu ‘yan mata ne da suka sha kwalliya cikin qananan kaya, suke bin ko wacce kujera suna ajiye abinci, ‘yan matan suna tafiya ne cikin salo da yanga da kwarkwasa tamkar suna gaban samari, duk inda suka je ajiye abincin sai sun duqa qasa qasa yanda nonuwansu zai bayyana bayan riga da wando mai nuna tsiraci da suka sanya. Hajiya Danasha ce ta matso kusa da kunnena ta fara fadin “Duk wadannan matan da kika gani suna tallan kansu ne a gurin qawayena, amma zuwan da kikai kin dusashe hasken ko wacce budurwa a gurin nan! Kin samu kar6uwa qwarai ga ko wacce Hajiya da take gurin nan, a yanzu haka akwai alqawarin miliyan goma da wata Hajiya tayi min akan matuqar na shawo kanki ki ka amince zaki bita gidanta ki kashe mata qishirwarta a wannan dare, bayan ita kuma akwai masu alqawarin miliyan biyar biyar da yawa, me ki ka ce Aysha?” *ALHAMDULILLAH. KARSHEN LITTAFI NA DAYA KENAN, MU HADU A LITTAFI NA BIYU. DOMIN GYARA, K'ORAFI, KO SHAWARWARI, A TUNTUBENI TA WANNAN LAMBAR* 09077591726
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27