Chapter 9
CHAPTER 8
⚖HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSOCIATION📚
Fitowa tayi daga cikin daki, taci karo da Kamal zai wuce ta corridor.
“Kin tashi?” Ya tambaye ta. “Ya kike jin jikin ki?
“Na gode da nesanto da kayi daga wurin nan. Amma ina ga ni zan wuce gida.”
A tsanake yake kallon ta na wasu yan dakiku kafin ya bata amsa da katuwar muryar shi da ta kusan tsorata ta.
“Ba zaki je gida ba, kin min alkawarin zaki min bayanin komai.”
“Dan Allah, ka barni naje gida. Ina tunanin shine mafita a yanzu. Bana son na saka ka a cikin abinda bai shafe ka ba. Kuma ba lallai ba ka yarda da ni idan na fada maka abinda ke faruwa da ni. Nafi son na je gida.”
“Kina tunanin, a maida ki gidan da zan yi, labarin bai shafe ni ba tuni? Ko ba komai na cancanci wannan. Kan na yarda da abinda zaki fada mini kuwa, ba zan iya cewa komai ba tinda baki fada min komai ba. Ba zan miki alkawarin yarda da abinda zaki fada ba, amma nayi miki alkawarin zan martaba duk wata kalma da zata fito bakin ki. Muje falo, zan yi order lunch sai ki min bayanin komai.”
A ranta tunani take : A'a ba zata iya saka shi a wannan labarin ba, domin Amriya zata iya cewa ta cutar da shi. Kuma in tayi hakan bata kyauta ba. Ya kamata ta bar wurin nan da sauri.
“Zan maka bayani wani lokacin, zan je wajen aiki yanzu ne.”
Tayi masa karya dan ya barta ta tafi. Bata da tunanin zuwa wajen aiki bayan abinda Amriya ta fada a kan Salmah. Bata iya ma tunanin irin kunyar da zata ji idan taje gaban ogan ta ba. Tana jin kanta tamkar wata muguwa kan abinda Amriya tayi. Wahalar ta tsaya a ita daya, ba zata so wasu su samu matsala ba ta dalilin ta. Ya kamata tayi nesa da kowa amma bata san me zata yi ba ko ta yaya zata yi ba... Tana tsoron ta cutar da mutane fiye da yanda take yi yanzu.
“Kina da taurin kai amma ni na fiki, please, kije falo kafin nayi odan abincin. Bayan nan sai ki min bayanin komai. Kar ki damu a kaina, kawai ki fada min abinda ke faruwa da ke.”
“Bai shafe ka ba Malam..” Ta fada wannan karon da dan bacin rai. Bata san ta ina ta samu wannan kuzarin ba, amma wannan ce kadai hanyar da zai sa ya fahimci bata son saka shi a matsalar ta.
“Ya shafe ni, saboda ya shafi dangina, ba zan barki ki tafi ba dan haka kina iya ihu iya son ranki. Zaki gajiyar da kanki ne kawai.” Ya fada mata shima sannan ya cigaba da tafiyar shi zuwa kitchen kamar komai bai faru ba.
“Ba..zaka..gane ba..” Ta fada tana kokarin bin bayan shi amma shi kuma ya kara sauri ba tare da ya kula ta ba.
Kofar fita ta nufa tana kokarin budewa amma ta kasa domin a rufe take, kuma babu keys a jiki. Ganin ba sarki sai Allah dole tayi yanda yace. A sanyaye ta koma falo ta zauna a daya daga cikin kujerun falon. Tsabar haushin da ya bata yasa bata lura da manyan hotunan zane. Kusan duka falon an kawata shi da zanukan. Tana tunanin shi ke zana su ganin daga gefe akwai zanen da ba'a karasa ba. Da alamu mai son zane ne shi.
Ta kusan rabin awa zaune tana kallon zanukan. Daga karshe wani ya konkwasa kofa. Kamal ne ya fito da sauri yaje ya bude.
“Yauwa nagode.” Taji ance kafin a rufe kofar. Mikewa tayi da niyyar sake gwada sa'ar ta wannan karon ko ya barta ta tafi gida, sai dai kafin ta karasa sai gashi ya shigo falon ledoji a hannun sa. Komawa tayi ta zauna. Shi kuma ya ajiye ledojin bisa table ya koma ya fita kamar yanda ya shigo. Tana kallon sa ya cika table din da kayan ci da na sha ba tare da ya kula ta ba. Bayan kai komo mai yawa da yayi daga karshe yace mata ta fara cin abincin. Plate ya turo mata gabanta, sannan ya ajiye mata coffee mai madara. Ganin ya tsare ta da ito, ta fara cin abincin. Jinta take duk a takure dan idan ta kai loma sai ta fi minti biyar bata hada ta ba.
“Ni bana cin komai sai coffee, dan haka duk wannan ke na siyowa shi. Ki ci...” Ya umarce ta.
“Ni gida zan je, bana son hankalin iyaye na ya tashi. Basu da labarin inda nake tun jiya. Ban ma san wani hali suke ciki ba yanzu.”
Aje kofin shi yayi ya bata amsa.
“Idan kika yi saurin fada min damuwar ki, zan yi saurin barin ki kije gida. Ni zan kai ki gida.”
Taurin kai gare shi ta yanda bata tsammani. Ta lura ba zai barta ta tafi gida ba har sai ta masa maganar Amriya. Tinda hakan yake so kuwa, zata fada masa.
“A makonnin baya...” Ta fara magana bayan dogon shuru da tayi. “A makonnin baya na hadu da wata mata a bakin kogi.”
Kallon ta yayi da alamar ta cigaba yana saurare.
“Tace min sunan ta Amriya kuma tana son mu zama kawaye. Tace min kusa da gidan mu gidan su yake. Haduwa ce ta bazata da ta dan girgiza ni. A ranar nan, kafin ta tafi ta bar gyalen ta kusa da ni. Nayi tunanin koh mance shi tayi, na yanke shawarar kai mata shi gidan su kamar yanda ta kwatanta mini... Na hadu da Mami, wata kawar Mahaifiya ta da nake tunanin ita ce mahaifiyar Amriya amma matar tace min tanada 'ya kuma ta rasu shekarun baya. Ban fahimci komai ba, duk na rude itama haka. Lokacin da ta nuna mini hoton 'yarta Aisha, naga ita ce wacce na hadu da ita bakin kogi.”
Kamal bai ce komai ba, sauraron ta dai yake a tsakane. Koma dai ya girgiza da jin labarin toh jikin sa bai nuna ba. Fuskar sa babu wani alamu, har Zahara taji tsoron kar ace bai yarda da labarin ta ba. Amma duk da haka ta cigaba da bashi labari.
“Tun daga ranar, na fara gane-gane da jin abubuwa. Na daina bacci, ko nayi sai muggan mafarkai. Ban baiwa kaina wahala ba wajen yarda cewa halin da na shiga yana da nasaba da haduwa ta da wannan matar. Ban yi kuskure ba, domin bayan wasu kwanaki ina bacci, wata mata ta bayyanar min. Nan na gane Aljana ce ke son shiga jiki na. Ta ce min tana son ta taimako na.”
“Kika ce mace ce? Da kamar wuya.”
“Tun daga wannan ranar, na fara canja halaye da shiga ta. Ina jinta a jiki na kuma tana sanya ni abubuwan da bana bukatar yi. Bansan me zan yi ba dan na fita daga wannan ukubar. Har tunani na ma ita ke controlling din sa. Idan ta fita daga jiki na ma, ina ji. Ina tune da duk abinda take yi. Sai dai tun jiya, na kasa tuna komai. Kuma hakan na damuna, bansan me take iya aikatawa ba nan gaba. Yanzun haka, ina tunanin yanda zan yi na nemi afuwa gun Mr. Ammar da budurwar shi.”
“Ke kuma babu abinda kika yi? Kika barta duk tana yin wannan?”
“Toh ai ban san yanda zan yi ba na rabu da ita. Ina tsoron ta cutar da dangi na, lokacin da take min magana na tabbatar ba zata rabu da ni ba ta sauki.”
“Ki dena nuna mata kina jin tsoron ta. Bai dace ta dinga gallazawa rayuwar ki ba. Ki daina bata wannan damar. Wa kika fadawa wannan zancen kuma kina karatun alkur'ani mai girma?”
“Ba wanda na fadawa bayan kai. Duk lokacin da nake so in dauko da niyyar karantawa sai inji na kasa. Ina jin ba zan taba fita da wannan tashin hankalin ba.”
“Da farko abinda ya shafi dan uwana, ina baki shawara da karki fada masa komai yanzu. Ki bari har komai ya laba. Kuma ya kamata ki fadawa iyayen ki. Ba karamin abu bane ke faruwa da ke, ba zaki iya yin komai ba ke kadai. Kina cewa ba zaki fadawa kowa ba, saboda kar ki sa su a matsala amma rashin fadar shi zai haifar da masifu da yawa domin ba wanda zai iya taimakon ki. Kiyi maganar da iyayen ki, ni kuma bangare na zan nemi karin bayani daga gun malamai kuma zan kokarta ganin na taimaka miki.”
“Ka yarda da ni kenan?” Zahara ta tambaye shi.
“Zahara, Aljanu suna rayuwa a cikin mu. Bama ganin su amma suna tare da mu. Akwai na kwarai haka akwai bata gari. Suma suna bautawa Allah kamar mu. Shiga jikin mutane yana daga cikin zunuban da aka hane su yi. Kuma suna yin sabo kamar yanda muke yi.”
Gyada kai Zahara tayi alamar gamsuwa.
“Don haka, ki tashi tsaye. Kar ki bari ta rinjayi rayuwar ki. Bata da wannan 'yancin.”
“Nagode da saurare na kuma da yarda da ni da kayi. Wannan ne karon farko da nayi maganar, kuma naji dadi sosai.”
“Ba komai, yanzu zan iya kai ki gida. Kiyi amfani da wannan damar ki sanar da mahaifan ki. Allah kadai yasan abinda wannan Amriyar take iya yi. Mafi akasari Aljani ne ke shiga mace kuma suna iya yinsu ganin sun boye kansu cikin jikin, dan kar a kora su amma nan bayan Aljana ce mace tana komai ganin ta bayyana kanta. Zan yi bincike mai yawa akan wannan, amma kafin nan kiyi magana da iyayen ki.”
“Ok nagode sosai.”
“Shikenan, muje na kai ki gida.”
“Ban san ya zan yi ba, na mayarwa da kanwar ka ba abayar ta. Kunya nake ji na koma gidan ku bayan abinda Amriya tayi.
“Kina iya rike ta.” Yace mata. “Kar ki damu.”
“A'a..a'a..ba zan..”
Katse ta yayi.
“Kar ki yi wani dogon zance, ki dauka, zan siyo mata wasu.”
(....)
A gidan su Zahara kuwa, hankalin Mama ya tashi sosai ganin Zahara bata dawo gida ba. Jiya da ta ganta cikin jar rigar nan, jikin ta bai bata ba amma ganin kamar 'yar tata tana cikin farin ciki sai bata yi magana ba. Amma yanzu ganin ba labarin ta, ta fara da nasanin barinta da tayi ta fita.
“Ko kiran Yan sanda muke?” Ta cewa Abba da ke ta faman duba takardun sa tun dazu.
“Kina tayar da hankalin ki sosai Asiya. Na tabbatar duk inda take cikin koshin lafiya take.”
“Ban san ta yaya kake ba, har ka iya zaunawa haka. Cewa tayi zata je wajen walima ba wai zata kwana a cen ba.”
“Mu bari har zuwa yamma idan bata dawo ba, sai muje mu sanar da yan sanda.”
Konkwasa kofar gida suka ji ana yi.
“Kin gani, na tabbatar ita ce ta dawo.” Cewar Abba.
Tashi Mama tayi taje duba mai konkwasawa, hankalin ta ne ya kara tashi ganin ba Zahara din bace. Wani mutum ne da bata sanshi ba.
“Assalamu alaikum.” Cewar mutumin.
“Wa alaikum salam.” Mama ta amsa mishi.
“Dan Allah ko Zahara Usman na ciki?” Ya tambaya.
Cikin rashin yarda, Mama ta yanke shawarar kiran mijin ta. Tambayar kanta take me kuma wannan tsohon mutumin ke nema wajen 'yarta. Mijin nata ya karaso bayan wasu yan mintuna, suka cigaba da magana da bakon.
“Zahara bata nan, ko lafiya kake son ganin ta?”
“Ko zan iya shigowa? Ina son muyi magana.”
Bayan dan dogon nazari da Abba yayi, daga karshe ya yiwa bakon iso zuwa cikin falo. Mahaifiyar Zahara ta kawo masa abin sha.
“Sunana Malam Shehu.” Cewar shi. “Nazo ne daga kauyen Na'iya. Nazo nan ne saboda 'yarku Zahara. Kuma nayi iya sauri na ganin nazo na ceci 'yarku.”
“Ka ceceta daga me?” Cewar Mahaifin Zahara. “Kan me kake magana?”
“'Yar ku Zahara tana fama da shafar aljanu.”
Kallon juna Mama da Abba suka yi. Tsawon sati biyu kenan Mama na yiwa Abba maganar amma yaki yarda, gashi yau wani mutum ya tabbatar musu. Duk da haka dai Mama zata so taji ta yaya Zahara ta gamu da aljanu.
“Ni babban Malami ne a kauyen Na'iya. Aljanar da ke jikin 'yarku sunan ta Amriya. Na santa saboda ta zauna da dadewa a kauyen mu, kuma ta haifar da masifu da dama. Na shiga neman ta tsawon watanni, sai yanzu aljanun da ke taimaka min suka kawo ni nan gidan ku. A cewar su, tana cikin jikin 'yar ku. Zahara tana dab da shiga halin da 'yan matan da Amriya ta kashe a kauyen mu suka shiga. Nazo nan ne dan kawo karshen ta da taimakon ku da taimakon 'yarku.”
“Ko zan iya magana da mai daki na, na yan mintuna?” Cewar Abba. Shi kuwa malam Shehu yace ba damuwa.
Bin bayan Abba Mama tayi zuwa cikin kitchen.
“Biyan sa kika yi dan yazo ya fada min wannan shirmen?”
“Kana tunanin zan iya yin hakan?”
“Toh ni musulmi ne, amma ba yanda za'a yi na kama karairayin mutumin nan.”
“Ba karairayi bane, ba a banza ba idan yasan sunan Zahara kuma yazo ya fada mana abinda nafi gudu a yanzun nan.”
“Sauki gare shi yanzu samun sunan mutum.” Cewar Abba.
“Ni na yarda da zancen shi, kuma zan saurare shi da abinda yazo.”
(...)
A bangaren Zahara kuwa. Godiya ta yiwa Kamal ta sauka daga motar bayan ya kawo ta unguwar su.
“Kiyi yanda na fada miki, zamu sake haduwa bayan kwana biyu insha Allahu.”
“Ok, nagode.”
Tsayawa tayi har ya tada motar, kafin ta juya ta tattaka zuwa gidan su. Ta nemi da ya ajiye ta nesa da gida saboda tana tsoron kar iyayen ta suyi zaton wani abu ganin ta sauko daga cikin motar wani. Gashi bata san me zata ce ba, na kin kwananta gida toh ina ga kuma anga wani ya sauke ta a mota. Duk da haka ta tattara kuzarin ta, ta konkwasa kofar gidan.
Mama ce ta bude mata kofa. Da tsananin mamaki Mama ke kallon ta, ganin ta sanye da Abaya.
“Mama kiyi hakuri da rashin dawowa ta gida jiya.” Zahara ta fara kai hari kafin Mama. “Zan miki bayanin komai.”
“Lafiyar ki kawai na son ji.” Cewar Mama.
Gyada kai Zahara tayi, Mama tace
“Zamu yi maganar daga baya. Yanzu akwai wani abu mai muhimmanci da nake son muyi. Zo muje.”
Rufe kofar Zahara tayi, tabi bayan Mama zuwa cikin falo. Gaishe da Abba tayi da kuma bakon shi. Zaunawa tayi kusa da Mama.
“Zahara.” Tsohon ya kira sunan ta.
“Tinda gata, ina tunanin zamu je mu fara aikin.” Tsohon ya sake fada.
Kallon Mama da ta kama mata hannu Zahara tayi.
“Akwai Aljana a tattare da ke 'yata, ya kamata muyi wani abun kafin lokaci ya kure.” Cewar Mama.
Mamaki Zahara take ta yaya suka sani, amma ganin wannan tsohon yasa tace shine zai fada musu.
“Amriya tana da karfi sosai, ta gudu koda taji alamun ina nan. Tasan ina nan shi yasa ta gudu, amma dole na maido ta ta karfi a jikin ki domin na kamata. Ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce. Zan yi iya kokari na ganin bata sake cutar da wani ba. Zan fidda ta daga rayuwar ki, dan ki samu yin rayuwa mai kyau.”
Abba tashi yayi ya bar musu falon. Zahara kuwa ta yiwa Mama kallon tambaya.
“Kar ki damu, Abban ki zai ga sauyi a tattare da ke. Ni na yarda da wannan mutumin, kuma nasan zai taimake ki.”
“Idan kun shirya, muna iya tafiya.”
“Zuwa ina?” Zahara ta tambayi tsohon a karon farko da ta bude bakin ta.
“A makabarta, a nan ne za'a yi aiki.”
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story 📖
By Malik al-Ashtar 🖋
On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35