Chapter 22
CHAPTER 21
⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚
Komawa Khadija tayi ciki tana murmushi tare da tambayar Kamal ko zata kara tsayawa domin taya shi hira.
“Waye yazo?” Kamal ya tambaye ta.
“Zahara ce.”
Da mamaki Kamal ya kalle ta jin Zahara tazo har gida neman shi. Gashi daman ya jima rabon shi da ita sakamakon halin da gidan su yake ciki ga kuma zanen da wani kamfani na kasar Malaysia suka bashi da zai gama shi da gaggawa. Ga kuma rashin lafiyar da yake fama da ita kwana biyu. Yayi kewar ta sosai, yana da tunanin da ya samu sauki yaje gidan su. Sai gashi cikin sa'a tazo, ba karamin dadi yaji ba.
“Tana ina? Ce mata ta shigo."
“A'a tayi tafiyar ta."
“Kamar ya ta tafi?”
“Na fada mata kana nan kuma tana iya shigowa amma tace min wucewa zata yi. Nasan ko sauri take.”
“A'a, ba gaskiya bane abinda kike fada. Idan da tana sauri ne ba zata zo nan ba. Kuma koda tazo nan ba zata ki shigowa ba. Me kika ce mata?”
“A'a komai kawai nace mata baka da lafiya ne kuma ni ke kula da kai.”
“Me kake yi haka? Me yasa ka tashi?” Ta tambaye shi tana mai nufo shi da sauri shi kuwa yana kokarin sauka daga bisa gadon da kyar.
“Tambayar ka nake, ina zaka je?”
“Zan je na ganta ne, na tabbatar tayi wani tunani ne a kanmu.”.
“Kamar ya tayi wani tunani, bata yarda da kai bane ko me? Baka da karfin jikin da zaka fita yanzu, ka kira ta wani lokacin sai ka yi mata bayanin babu wani abu tsakanin mu. Ni zan iya zuwa na ganta saboda kai.”
“No, kar ki damu nafi son naje da kaina.”
Cikin wardrobe din sa ya bincika ya dauko bakin jeans da t-shirt ita ma baka. Duk da yana jin babu kwari jikin sa amma dole sai yaje domin baya son Zahara tayi wani tunani. Haka Zahara take, dandanan karamin abu ya juya mata tunani. Ya fada a ransa. Baya son tayi tunanin yana wasa da hankalin ta ne idan ba haka ba zai sha wuya kafin ya sake samun yardar ta. Sai da aka dauki lokaci sosai kafin ta fara sakewa da shi. Ba zai so ya rasa komai ba saboda yar karamar rashin fahimta.
“Toh ni zan tuka ka, please kar ka tafi a haka. Zan damu.”
“Da gaske kina son taimaka min?" Ya tambaye ta.
“Yes of course, ni fa na tambaye ka."
“Ki kula min gidan, ba zan jima ba zan dawo. Nayi miki alkawari.”
“Amma.."
“Please kar ki ce komai, ba jimawa ba zan yi.”
Ya fada kafin ya saka takalmin sa. Duk da abinda yace mata sai da ta taimaka masa ya shiga mota. Tayar da motar yayi da tabbacin Zahara gida ta wuce. Wajen karfe tara ne na dare, baya tunanin tana wajen aiki. Duk da haka yayi kokarin kiran ta a waya amma tana ta ringing ba'a daga ba. Kuma ya tabbatar da gangan taki daga kiran.
Yasan hakan zata faru. Ba zai ga laifin ta ba. Har yanzu akwai kuruciya a tattare da ita, idan tasa abu a kanta yana wahala a iya canza mata ra'ayi. Hakan yana dan bata masa rai amma yana iya kokarin sa ganin ya fahimce ta.
Yarinya ce kyakyawa da hankali amma tana da karancin yarda. Tana tsoron kar ace yana tare da ita ne kawai dan yayi wasa da hankalin ta domin tana ganin bata kai ajin da zai yi soyayya da ita ba kuma zai iya samun wata fiye da ita. Ba wai ita ce ta fada masa ba, shi da kan sa ne ya karance ta.
Yana kusan kaiwa gidan su, ya sake kiranta domin ta fito amma bata daga ba. Gashi kuma ba zai iya shiga gidan su ba a wannan lokacin, domin zai iya kara hassala ta. Daga karshe yanke shawarar yi mata text yayi.
“Slm Zahara, ina kofar gidan ku. Ina son ganin ki dan muyi magana. Bani da lafiya amma zan jira kofar gidan ku har lokacin da kika ji kina son fitowa ki ganni.”
Tura mata msg din yayi, bayan wasu yan mintuna aka nuna masa ta buda amma babu alamar fitowar ta. Ya fahimci lallai tayi fushi sosai, ya yanke shawarar sake tura mata wani text.
“Nasan abubuwa da dama na yi miki yawo a kai, ki zo ni zan miki bayanin komai. Bana son barin ki a duhu.”
“Idan baki zo ba, ni zan shigo cikin gidan naku."
Bayan kamar mintuna biyu sai gata ta maido masa.
“Gani nan zuwa."
Bai ji dadin barazanar shigowa gidan su da yayi mata ba amma ita ta ja, kuma hakan yayi aiki domin bayan wasu mintuna ta sake yi masa Text tana tambayar sa inda yake. Fada mata yayi wurin da yayi parking. Bayan wasu mintuna sai gata tazo.
Bude kofar motar tayi, bayan ta shigo ta maida murfin motar ta rufe da karfi. Bata taba yin irin haka ba.
“Ina wuni?” Tace masa.
“Me yasa kika tafi?" Ya tambaye ta kai tsaye.
“Babu wani dalilin zuwa na cen."
“Toh kenan kin je ne dan ki ga kofar gidan ki dawo?”
“Bakuwa na tarar gare ka, bana son takura maka ne.” Ta fada da kaushin muryar da ya fara tunanin anya kuwa Zahara ce
“Wa ya fada miki ina son bakuntar ta? Nafi son taki sau dubu."
“Amma ai kai ka kirata. Ina nan tsawon weeks babu labari kuma ace bakada lafiya amma shi ne ita ka kira.”
“Da farko, da farko dai ba ni na kira ta ba. Sannan abinda yasa kika ji ni shuru ayyuka ne suka min yawa, ta yanda baki tsammani. Sannan wata matsala da ta taso a family na ga kuma kaina kamar zaya fashe. Amma na rantse miki kullum cikin tunanin ki nake. Sannan kinsan adadin yanda kike da muhimmanci gare ni, har abada ba zaki taba takura min ba...Naso ace kin zo kin ganni na tabbatar hakan zai mini dadi.”
“Toh amma wannan matar tace min...”
Katse ta yayi.
“We don't care about what she said. Ki daina sauraron abinda mutane ke cewa Zahara, ba zai kawo miki komai ba na alkhairi. Wannan matar friend ce kawai, a koda yaushe tana nan domin ni amma babu komai bayan wannan.”
“Kalle ni nan Zahara." Yace da ita.
A hankali ta juyo ta kalle shi.
“Yaushe zaki fahimci adadin yanda nake jin ki a zuciya ta? Idan da wani ne ba zan zo nan ba, bani da lafiya sosai Zahara Kuma bana tunanin zan iya mayar da kaina gida yanzu.”
“Na cika son kaina da yawa. Mugun kishi ya rufe ni har yasa ban damu da halin da kake ciki ba. I'm really sorry, ban yi tunani bane.”
“That's my Zahara ! "
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kai.
“Ya jikin naka? Me yake damun ka yanzu?”
“Ni ban ma sani ba. Ina da zazzabi kuma ga matsananciyar gajiya amma duk wannan bashi ne gabana ba, abinda nake so shine ki yarda da ni, ko me zai faru ina so ki kira ni ko ki zo ki ganni muyi magana domin ba yara bane mu.”
“Ina son nima ka dinga fada min matsalolin ka, ka dinga neman shawara ta. Yayin da kuma ba zan iya nemar maka mafita ba, zan kasance ko dan na saurare ka.” Ta fada mishi ba tareda ta sauke idanunta ba.
Murmushi Kamal yayi ganin sun daidaita wannan matsalar, kuma yana ganin takun farko ne na alakar su. Yana son yarda ta shiga tsakanin su mai karfi kafin ta amince ta aure shi. Daman ya riga da ya fada mata ranar da taji ta amince da shi, zai zo ya nemi auren ta.
“I'm really happy Zahara..idan da kin sani. Nayi tsoron ki nade kanki kuma ki daina yarda da ni.” Ya fada yana mai kara matsowa inda take.
“Nima nayi farin ciki da muka daidaita hakan, da ba zan iya bacci ba yau." Ta fada a takure ganin yanda yake kusa da ita sosai.
Da murmushi a fuskar sa, ya shiga matso da kanshi zuwa nata, hankalin sa na kan kyawawan lips din ta. Ya daina sauraron duk wata murya da ke gargadan sa da kar ya sumbace ta. Tuni yayi nisa, burin shi yaji yanayin da kiss din su zai bayar.
Kara matsawa yayi har ya kai ga hancin sa ya taba nata. Koda lips din sa suka taba nata, da sauri ta ja da jikin ta baya.
Shima firgigit yayi, yana mamakin abinda tayi da danasanin kasa rike kansa da yayi.
“I'm very sorry, ba da wani nufi nayi hakan ba. Na aikata ba tare da izinin ki ba. Kiyi hakuri da rashin da'ar da nayi miki.”
Zahara duk ta daburce ta kasa magana. Tana magana amma shi bai jin abinda take cewa.
“Sorry amma bana jin me kike cewa.”
“Ba rashin da'a bane, na tsora ta ne domin ban taba yin irin haka ba. I'm sorry."
Murmushi yayi mata.
“Ni zan baki hakuri, kuma Allah ma baya son hakan. Nayi murna ma da kika tsayar da ni. You are so special Zahara.”
Murmushi tayi cike da jin nauyin sa ta sunkuyar da kai kasa.
“Mu je na raka ki gida, dare yayi.” Ya fada yana fitowa daga cikin motar.
Yanayin da suka shiga gaba daya yasa ya manta da ba wani karfi gare shi ba. Faduwa yayi lokacin da ya fito daga cikin motar.
A tsorace Zahara ta yo kanshi, ta taimaka masa ya tashi.
“Zafi jikin ka.” Ta fada hankalin ta a tashe.
“Oh kar ki damu. Zan iya raka ki." Ya fada yana dafa ta.
“Ko fa tsayuwa baka iya yi, bari na kira taxi mu je asibiti."
“No, na fada miki ba komai. Kafin gobe na warware."
“A'a mu je na raka ka."
“Kusan karfe goma ne fa yanzu, me zaki cewa Mama?”
“Na kira ta na yi mata bayani daga baya, nasan zata fahimta.”
Daga karshe ya yarda. Domin da gaske karfin jikin sa kara ragewa yake yi sosai. Bai san me yasa ba.
(....)
A BANGAREN AFNAN
Yau psycologist ke zuwa, juya masa baya tayi domin nuna masa babu abinda zata fada masa. Tun tsawon makonni kenan take fada musu bata bukatar wani gwajin kwalwa amma Ammar yasa likitan ya dinga zuwa yana duba ta har sai ya tabbatar lafiyar ta kalau.
Tun ranar da aka kaita asibiti sakamakon yanke jijiyar hannun ta da tayi, duk hankalin familyn ya dawo kanta ba kamar Hajiya Karima. Da yanzu Afnan ke kiran ta da sunanta, tun ranar da tazo tayi mata barazana.
“Kin dauka saboda kin yi kokarin kashe kanki zai sa inji tausayin ki? Ki mutu yau ko gobe ni bai dame ni ba. Ko ba komai kin tabbatar min da gaske kike son bata sunan gida na. Idan kika kuskura kika fadawa Ammar ko Kamal ko kuma wani wannan shirmen da kika fada min, wallahi sai na lahira ya fiki jin dadi. Kin fi kowa sanin wacece ni da kuma abinda nake iya aikatawa."
Hajiya Karima ta fada mata Kafin tayi tafiyar ta, ta bar Afnan cikin tashin hankali. Abinda yasa tayi kokarin kashe kanta, saboda tasan babu wanda zai yarda da abinda zata fada. Ba zata so ayi ta zargin ta ba bayan abinda wannan mutumin ya aikata mata. Ba zata iya cigaba da rayuwa ba domin idan Hajiya Karima bata yarda da ita ba, bata ga waye zai yarda ba. Waye zai yarda da hakan? Mutum kamar Alhaji Yusuf da ake ganin mutunci da karamcin sa. Gashi kuma da kyawawar mata. Mutane zasu ce hauka take. It kuwa ba zata iya jure hakan ba.
Lokacin da Kamal da Ammar suka zo ganin ta, Hajiya Karima ce masu tayi. Ciki ne Afnan take da, shine tayi kokarin kashe kanta domin bata san waye yayi mata shi ba. Afnan bata yi gangancin musa mata ba, kuma yayyun nata basu ce komai ba. Amma taga a idanun Ammar yayi bakin cikin abinda ta aikata. Kuma ya kira psycologist ya duba ta domin gano ta ina ne ta samu matsalar son kashe kanta.
Saidai ita Afnan bata bukatar wani psycologist, tafi son a barta ita kadai. Abinda ya baiwa yayyun nata mamaki shine, zubewar cikin nata bai wani dame ta ba. Suna ganin ko har yanzu bata dawo daidai bane, amma ita tana ganin wannan shine kadai abu mai kyau da ya same ta kwanan nan.
Idan da likitan nan zai kyale ta na kamar sati guda. Toh zata tattara kayan ta ne ta bar garin. Ta yi nesa da Hajiya Karima, da wannan dan akuyan da ma kowa.
“Ya jikin naki?” Cewar Doctor Abdallah amma bata bashi amsa.
Tasha fada masa ba zata yi masa magana ba, amma ya nace yaki ya shafa mata lafiya.
“Idan baki yi magana ba, ba zan barki ki tafi ba kin sani ko? Yayanki yanada gaskiya, ki bada hadin kai domin shawo kan lamarin. Zaki samu riba biyu, bayan sallamarki ki koma gida da zan yi, za kuma ki samu sauki akan duk wata damuwa taki.”
“BABU WANI DA YAKE IYA TAIMAKA MIN.
Ta fada cikin tsawa da iya karfin ta. Abinda yayi ne ya kara bata mata rai. Bude littafin sa yayi, yayi wani rubutu a ciki.
“Mun samu reaction, yayi kyau mu cigaba."
“Kenan ba zaka shafa min lafiya ba?” Ta tambaye shi.
“Ba zan iya ba, ba dai a halin da kike ciki ba.”
“Ni lafiya ta kalau ! Ka rabu da ni shine zai sa in warware.”
“Kina tunanin lafiyar ki kalau amma kawai kwalwar ki ce ta hada miki katangar garkuwa tsakanin ki da trauma ko fiye da hakan wato hauka.”
“Ok, a dauka bani da lafiya. Idan na fada maka komai zaka rabu da ni?”
“Mu gwada.. mu ga abinda zai faru.”
“A'a.. kar kayi kokarin rikita min kwalwa. Ina son da na fada maka komai ka dena damuna.”
“Ok, za'a yi yanda kika bukata.”
“Shikenan ka dawo gobe zuwa karfe tara zan yi maka bayanin komai.”
“Ok, Allah ya kaimu.”
To be continued...
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story 📖
By Malik al-Ashtar 🖋
For more novels https://bit.ly/3Egdy1m
On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35