Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

CHAPTER 14

Amriya Hatsabibiyar Aljana Book 1 Complete Hausa Novel 2,669 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚

“Ki daina motsowa haba Zahara, idan baki jin bacci. Zaki iya tashi ki samu wani abun kiyi.” Cewar Sarat cikin muryar bacci.

Tana da gaskiya, Zahara ta kasa daina juyi bisa gado, tun lokacin da suka kwanta. Ta yaya zata iya bacci? Bayan abinda ya fada mata. A lokacin shishigin Sarat ne ya kwace ta. Tazo a daidai lokacin da Kamal yace yana son ya auri Zahara.
Zahara taji kamar ta kurma ihu domin ya fitar da ita daga yanayin da take ciki. A lokacin bata san me zata yi ba, ko amsar da zata bashi. Juyawa tayi, tayi tafiyar ta ba tare da tace dashi komai ba, saidai koda suka koma daki ta fara jin haushin kanta na kin tsayawa. Domin akwai akwai tambayoyi da dama da take son amsoshin su.

A lokacin hanyar daga lambun hotel din zuwa dakin da suka sauka, ba karamin tsayi yayi mata ba. Domin tasan idanun Kamal na kanta ga kuma tarin tambayoyin da Sarat take mata.

“Soyayya kuke? Amma munafuka ce ke Zahara !! Bani labari, ta yaya kuka fara soyayya ??”

“Stop please.” Zahara ta fada da sa ran ko Sarat zata yi shuru amma kamar ta manta wacece Sarat.

“Kin hanani kutsa kaina gurin Boss, ashe ke da yayan shi kike soyayya. Amma kar ki damu na fahimce ki, ba wanda zai iya tsallake charm din su. Abun mamakin, yanda kika yi, kika iya shiga wurin shi, duk da miskilancin sa. Come on Zahara, fada mini meye sirrin?”

Haka Sarat tayi ta maganganun ta, ba tare da Zahara ta tanka ta ba, dolen ta tayi shuru da ta gaji. Zahara na tunanin ma Sarat fushi tayi, amma ita wannan ba shi bane a gaban ta.

“Zahara kina takura min, kin hana ni bacci.” Sarat ta sake maimaitawa alhali ita Zahara juwa kwanciyar ta ne tayi wannan karon ba tare da tayi wani kwakwaran motsi ba.

Tashi Zahara tayi daga kan gadon, ta fito ta kofar bayan hotel din. Sanyin da ake dan rurawa yayi mata dadi. Nadamar kin zuwa da Kur'anin ta take. Domin ta lura lokaci ne mai kyau yanzu na karatu da nazari. Idan da tayi hakan kuwa, da ta samu dan sauki har ta iya yanke shawara mai kyau. Domin a halin yanzu, a cikin confusion take. Ta yaya zai iya zuwa a gaban ta yace yana son ya aure ta, alhali basu wani san juna ba. Wannan hujja ce da ke nuna ya dauke ta sakarya, yana tunanin zata yarda da wannan shirmen? Ita kuma yanzu take kara jin haushin kanta, na da bata jefa masa wayar shi ba.

“Kema kin kasa baccin koh?”
Muryar Mr. Ammar ce ta dawo da ita daga duniyar tunani. Yana zaune bisa daya daga bencinan dake cikin lambun hotel din. Tayi nisa sosai a cikin tunanin har yasa bata lura da shi ba a wurin. Murmushi tayi masa, amma babu tabbacin yaga murmushin da yake akwai dan duhu a wurin.

“Ko zaki taya ni zama ne?” Ya tambaye ta.

Bata yi gardama ba taje ta zauna kusa da shi. Hirar aiki suka fara, hakan kuwa yasa ta dan manta halin da take ciki shima haka domin ya nuna mata bayan wasu mintuna.

“Ban yi tunanin haka ba, amma hirar aiki da muke yi a wannan lokacin ya dan yaye mini damuwar da nake ciki.”

“Nima hakan.” Cewar Zahara.

“Da gaske?” Ya fada. “Wani abu na damun ki ne?”

Ba zata iya fada masa abinda ke faruwa tsakanin ta da dan uwan sa ba.

“Dalilin brother na ne koh?” Ya tambaye ta.

Ta yaya ya sani? Yanda ta waro idanu cike da mamaki ne ya bashi dariya. Sai da yayi dariya mai isar sa kafin yace

“Idan da kinga yanda fuskar ki tayi, da sai cikin ki yayi ciwo dan dariya.”

“Ta yaya.. yaya aka yi kasan da wannan zancen?”

“Shi ya fada min.” Ya fada da dan murmushi.

Zahara ta rasa me zata yi tsabar kunyar sa da ta kama ta.

“Baki da damuwa akan wannan, ba zan takurawa rayuwar ku ba. Kawai dai kin dan tashi hankalin ki ne, shi kuwa brother na wannan ne karon farko da naga ya kula budurwa.”

Sunkuyar da kai kawai ta iya yi, domin bata san amsar da zata bashi ba.

“Yayi min bayanin shakkun da kike da game da gaskiyar abinda ya fada miki. Ba wani kwararre bane shi a wannan fannin amma ina tabbatar miki ba zai bayyana miki hakan ba idan ba gaske yake ba. Ban kuma ce kiyi saurin yarda da shi ba, ba tare da kin samarwa kanki amsoshin tambayoyin ki ba. Dan uwa na ne shi, amma ba hakan zai sa na bari ya cutar da ke ba. Idan akwai matsala, ni ne na farko da zan nesanta ki da shi.”

“Ba fa soyayya muke ba... kuma bani da tabbacin irin hakan zata faru a tsakanin mu.”

Dariya Mr. Ammar yayi.

“Ok, kar dai ki tursasa kanki kan abinda baki da ra'ayin shi. Ki fada masa gaskiyar baki bukatar kasancewa da shi, idan da gaske hakan ne a ranki.”

Matsalar ba wai Zahara bace, saidai shi Kamal din. Ba wai bata son shi bane, kawai bata san ko zata iya yarda da shi bane, ta shiga, kai kasa ko a'a. Tana tsoron shiga fagen da bata da masaniya, ta fara soyayyar da zata da ita. Tana da rauni a wannan fannin, cin amana ko rabuwa ta bazata, suna iya yi mata illar da zata iya rasa ranta. Amma idan da gaske auren ta yake son yi? Shin ya dace ta amince? Tana son amincewa, domin addinin ta yayi mata hani kan duk wata alaka da saurayi kafin aure. Idan da gaske yana son auren ta, kamata yayi su samu lokaci su san juna kafin auren.

“Kar ki takura kanki.” Cewar Ammar. “Har yanzu kina da lokaci a gaban ki. Kiyi abinda kike ganin daidai ne. Kar kiyi abubuwan da kika san zaki zo kina dana sani. Ni gani nan... Ban ma san ko zan iya auren matar da nake so ba. Amma ba zan yi kasa a gwiwa ba, zan yi iya kokari na ganin ban yi nadama ba a rayuwa ta. Kuma koda wata rana, ya tabbata na rasa ta. Toh zan san na fafata da iya jiki da ruhi na a kanta.”

Zahara a ranta tace, mai yiyuwa wannan shine lokacin da zata fada masa abinda ya faru. Amma ko hakan zai canza wani abu? Ko ba komai ta samu salama da zuciyar ta amma bata tunanin zai fahimci zancen. Ko kuma kamata yayi ta karfafa masa gwiwa wajen ganin ya dawo da masoyiyar sa.

“Mahaifiya ta na son na auri yar kawar ta domin wani buri nasu na daban...”

“Ban sani ba ko... ya dace na shiga abinda ba ruwa na. Amma ina ganin rayuwar ka ce, ya kamata kayi fada domin wacce kake so. Kayi duk wani abinda ya dace na ganin ka dawo da ita. Na tabbatar ita ma abinda take so kenan.”

Murmushi yayi, murmushi da bai kai zuciya ba.

“A halin yanzu ba wanda ta tsana kama ta.”

“Ina ganin kawai tana cikin bacin rai ne. Bansan komai ba game da hakan amma ina tunanin ba zai yiwu mu iya tsanar wanda muka ce muna so na tsawon shekaru ba, koda wannan mutumin ya cutar da mu. Tana kokarin ta tilasta kanta ne akan ta tsane ka domin yayewa kanta damuwar da take ciki, amma karya kawai take wa kanta. Kayi fada kuma kar kayi nadamar hakan. Kayi iya kokarin ka na ganin ka shawo kan mahaifiyar ka. Ka fahimtar da ita cewa kaima cikakken mutum ne, mai buri da ganin ya gina rayuwar sa mai kyau. Domin kowace mahaifiya farin cikin danta shine nata, tana tunanin wacce ta zaba maka ita ta dace da kai. Amma kaima ka nuna mata, baka yi zaban banza ba. Dukan mu mutane ne, kuma muna yin kuskure, dan haka ka nuna mata tayi kuskure, kuma auren da zaka yi rusa ka zai yi, ba wai farin ciki ba.”

Ya saurari duk abinda ta fada. Dagowa yayi ya kalle ta bayan ta gama.

“Nayi mamaki... Wannan ne karo na farko da kika yi magana mai tsawo kuma babu gargada. Ina tunanin sai na shirya walima domin wannan.” Ya fada yana dariya. “I knew that on the beyond your fragile and shy appearance hides a very thoughtful and intelligent woman. Nagode sosai da wannan shawarwarin naki Zahara, kina da gaskiya kuma zan yi iya kokari na ganin nayi yanda kika ce. I feel a lot.. better now.”

Sosai bata jin dadin ganin sa a wannan yanayin.

“It's normal...” Ta bashi amsa a takaice.

“Ya kamata mu je mu kwanta, kar tashi da wuri yayi wahala gobe. Ina so da an gama meeting din zamu hau hanyar gida.. dan haka ku zama cikin shiri.”

“Ok, Allah ya kaimu.”

Direct daki ta koma, ta tarar da Sarat sai baccin ta take, ita kuwa sai da ta rage kayan jikin ta, domin taji dadin baccin. Bata jima ba bacci ya dauke ta. Ji tayi kamar kwanan mintuna biyar tayi kafin gari ya waye. Kwaramniyar da Sarat ce ke yi ya tashe ta, tuni ita har ta shirya. Bata yi mata magana ba, kawai kallon ta tayi kafin ta fice daga dakin. Da sauri ta tashi ta shirya kafin tayi latti. Ganin bata zo da kaya masu yawa ba, shirya su bai dau lokaci gare ta ba. Wucewa tayi dakin da suke meeting, cikin sa'a kuwa bata rasa komai ba game da meeting din. Hajiya Hasana da mijin ta Elh Nuhu basu kai da karasowa ba. Saidai Mr. Ammar, Sarat da kuma Ibrahim. Sai da suka jira na kamar mintuna talatin kafin bakin su zo. Wannan karon Kamal yana nan, kuma dashi aka yi meeting din. Zahara iya kokarin ta take ganin basu hada idanu ba.

Shi kuwa akai akai yana satar kallon ta amma ita bata yi gangancin hada ido dashi ba. Bayan bakin sun tafi, Mr. Ammar ya basu mintuna ashirin dan su shirya kayan su. Zahara kuwa daman a shirye take, dan haka sai ta wuce direct cikin mota.

“Baki jima ba.” Mr. Ammar yace mata bayan ta shiga cikin motar.

“Daman ba wasu kaya ba gare ni.” Zahara ta bashi amsa.

“Ai da kin tafi tare da Kamal, har ya tafi mintuna goma da suka wuce, shi da Afnan. Taso ta tsaya amma shi yanada ayyukan da zai yi cen gida.”

“Ah...ok..”

“Kin samu yin magana dashi da safe?”

Tana shirin bashi amsa sai ga Ibrahim yazo da kullum fuskar sa dauke da murmushi.

“Wai me Sarat take yi ne?” Mr. Ammar ya tambaye ta.

“Mai yiyuwa bata karasa shiryawa bane, bari naje na dubota.”

“No kar ki damu, bari naje nayi mata magana. Bata lokacin ya isa haka."

Zahara bata tunanin hakan tunani ne mai kyau amma bata da wani excuse da zata hana shi tafiya.

Bayan Mr. Ammar ya tafi, Ibrahim ya shiga motar, ya zauna mazaunin gaba. Bayan sun gaisa. Yace
“In tambaye ki?” Ya fada tareda juyowa yana fuskantar Zahara.

“Ina jinka.”

“Kawar ki, tana da saurayi?”

“Wa Sarat?”

“Eh.”

“Uhm, gaskiya ban sani ba. Dan bama irin wannan zancen da ita amma zaka iya tambayar ta.”

“No, bana tunanin zan iya yi mata wannan maganar, please kema kar kiyi mata.”

“Ok, kar ka damu.”

A BANGAREN AMMAR

Da hanzari ya shiga cikin hotel din, daya daga cikin ma'aikatan ce ta taso da sauri ta tarbe shi.

“Kayi mantuwa ne Mr. Ammar?”

“No, madam kar ki damu. Just nazo duba abinda ma'aikaciya ta ke yi ne.”

“Ah ok, ko na sa daya daga cikin mutanen mu ya raka ka? idan kana so.”

“A'a ba bukata, ba zan dauki lokaci ba.”

“Ok, a fito lafiya.”
Murmushi yayi mata sannan ya shiga lifter. Dakin da su Sarat din suke yana saman nashi ne. Zuwa yayi ya konkwasa.

“Sarat? Ke kadai fa muke jira.”

Shuru bai ji an amsa ba. Cigaba yayi da konkwasawa har ya fara gajiya, amma bata bude ba. Number ta ya kira, yaji a kashe. Har yana shirin juyawa ya koma wajen ma'aikatan, yaji an bude kofar. Sarat ce gaban sa, daga ita sai rigar bacci wacce da ita da babu duk daya. Kasa motsawa Ammar yayi, haka kuma ya kasa dauke idanun sa a kanta.

Kamar rakumi da akala, ta janyo shi zuwa cikin dakin tare da rufe kofa. Tura shi tayi jikin bango, ta wani shige jikin shi.

Hakan babu kyau, ka kuma ci amanar Salmah. Wani bangare na zuciyar sa ne ke ta yi masa gargadi.

Kar ka damu ai ka wahala Ammar kuma Salmah bata bukatar ka yanzu. Dayan bangare na zuciyar sa marar kyau ya shiga ingiza shi.

Haka bangarorin biyu na zuciyar sa suka shiga dambe, a yayin da ita kuma Sarat bata yi magana ba, ta shiga sumbatar shi...a wuyan sa.. a kirjin sa.. a cikin sa.. a ko'ina na jikin sa. Jin hannayen ta yake na yi masa yawo ko'ina a jiki. Yayi iya kokarin sa ganin ya bar dakin, amma sha'awar ta ta baibaiye shi...

“Stop Sarat.. ya kamata mu tafi..” Ya hada iya kuzarin sa wajen fadar kalmomin nan. Ita kuma kamar ya kara tunzura ta, ta yage rigar da ke jikin ta, sai gata ta koma babu komai jikin ta. Hakan kuwa da tayi yayi tasiri gare shi, bai yi wata-wata ba ya tura ta bisa gado tare da haye ruwan cikin ta... Daga nan mai aukuwa.. ta auku.

A BANGAREN SU ZAHARA KUWA

“Awa daya fa kenan, Mr. Ammar bai dawo ba.. gaskiya akwai abinda ke faruwa.” Cewar Ibrahim yana ta kokarin kiran ogan su, amma tana ta ringing ba'a dauka.

“Oh kin gan shi nan ma.” Ya fada lokacin da ya hango Mr. Ammar din.

Ta window Zahara ta hango shi dauke da akwatunan Sarat. Saka su yayi a boot, kafin ya zagayo ya shigar motar. Tare da ce musu

“Tana gyaren kayan ta ne, shi ne na tsaya taya ta dan tayi sauri. Gata nan zuwa.”

“Ah, mun yi tunanin ko wani abun ne ya faru.”

“Wani abu kamar me?” Mr. Ammar ya fada a dan harzuke.

“Toh nima ban sani ba dai.” Cewar Ibrahim.

“Kana da matsala kai..”

Bayan wasu yan mintuna, Sarat tazo tana ta faman washe hakora.

“Sorry na bata muku lokaci. Kayan ne suna da yawa. Da naji maganar Zahara nazo da yan kadan.”

Zahara bata yi magana ba, bata san dalili ba amma tana ji a jikin ta akwai abinda ya faru tsakanin Sarat da Mr. Ammar. Bata gasgata hakan ba, sai da suna kan hanya, Sarat ke ce mata :

“Kina shanawar ki da yayan boss, nima wannan karon lokacin shanawa ta ne !!”

“Me kike nufi da hakan?”

“A'a komai, zan yi kamar ke. Nima sirri ne.”

No.. bayan duk maganar da suka yi jiya, Mr. Ammar ba zai fara wata alaka da Sarat ba, hakan baida wata ma'ana. Ta tabbatar Sarat, ta fada mata hakan ne domin tayi magana... Tana fata ace hakan ne.

Ta gasgata hakan da kyau.. bayan wasu kwanaki da dawowar su, ta fara lura da wasu abubuwa tsakanin Sarat da ogan su. A duk lokacin da suka hadu, tana ganin yanda suke kallon juna. A ranta tace wannan shi ne yake kira da fada akan masoyiyar sa? Dole tayi wani abu kafin ayi nisa. Duk wannan ta dalilin ta ne, zata taimaka masa ganin ya dawo kan hanyar daidai. Haka Sarat ya kamata ta fahimci Mr. Ammar yana cikin bakin cikin rabuwa da masoyiyar sa ne, shi yasa yake kula ta ba wai dan yana sonta ba.

A yayin da Zahara ke kokarin shawo kan Sarat amma taki ta saurare ta, a ranar bayan ta dawo gida daga aiki wajen shidda na yamma, cike da mamaki wa zata tarar in ba Kamal ba zaune a falon su.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
  2. 2 CHAPTER 1
  3. 3 CHAPTER 2
  4. 4 CHAPTER 3
  5. 5 CHAPTER 4
  6. 6 CHAPTER 5
  7. 7 CHAPTER 6
  8. 8 CHAPTER 7
  9. 9 CHAPTER 8
  10. 10 CHAPTER 9
  11. 11 CHAPTER 10
  12. 12 CHAPTER 11
  13. 13 CHAPTER 12
  14. 14 CHAPTER 13
  15. 15 CHAPTER 14
  16. 16 CHAPTER 16
  17. 17 CHAPTER 15
  18. 18 CHAPTER 17
  19. 19 CHAPTER 18
  20. 20 CHAPTER 19
  21. 21 CHAPTER 20
  22. 22 CHAPTER 21
  23. 23 CHAPTER 22
  24. 24 CHAPTER 24
  25. 25 CHAPTER 23
  26. 26 CHAPTER 25
  27. 27 CHAPTER 26
  28. 28 CHAPTER 27
  29. 29 CHAPTER 28
  30. 30 CHAPTER 29
  31. 31 CHAPTER 30
  32. 32 CHAPTER 31
  33. 33 CHAPTER 32
  34. 34 CHAPTER 33
  35. 35 CHAPTER 34
  36. 36 CHAPTER 35
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});