Chapter 30
CHAPTER 29
I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 29 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”
http://www.ashblogg.com.ng/2022/03/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-29.html
Karo na farko bayan lokaci mai tsawo, yau taji tana son tafiya makaranta. Kwanakin nan da tayi cikin gida yasa tayi tunani sosai akan halin da take ciki, kuma hakan ya bata damar kula da kanta da kuma na ƙwaƙwalwarta amma rufe kai kullum a gida ya fara isar ta.
Kwance take bisa gado, tana tuna lokutan baya masu daɗi tare da ƙawayenta. Tun bayan abinda ya faru, tayi nesa da kusan duka mutanen da ta sani. A lokacin tana jinta cikin ƙazanta da ba zata bari ta shiga mutane ba. Kwanan nan kuwa da ta gane bai dace ta tsani kanta ba, son komawa school yazo mata...
Tana tsaka da tuna rayuwarta ta baya lokacin da bata da wata damuwa.. sautin tafiyar ɗan uwanta Ammar ya dawo da ita duniyar zahiri. Knocking ƙofar yayi tazo ta buɗe masa, bayan ya shigo ɗakin sun gaisa ya samu guri ya zauna. Sosai ɗan uwan nata ke kula da ita. Bata da fargabar komai idan yana kusa da ita. Bayan sun taɓa hira, Afnan ke faɗa masa tana son komawa school.
“Kina son komawa school?" Ammar ya tambaye ta yana fiddo ido tsabar mamaki.
Afnan ganin yanayin ɗan uwan nata yasa ta ƙyalƙyace da dariya sannan tace
“Akwai ka da abun dariya, fita fa kawai nace zan yi, amma duk ka tashi hankalinka haka."
“Dole in tashi hankalina, ai wannan labari ne mai daɗi ! Ina nufin.. idan kin ce kina son zuwa school, saboda kin samu lafiya kuma kin shirya ! Ko ba haka bane?"
Gyaɗa masa kai Afnan tayi.
“Naji daɗi sosai da sosai." Cewar Ammar. “Zan iya samar miki malami nan gida idan kika ji ba zaki iya ba."
“A'a ! Ina son jarabawa, zan sanar da kai, idan na ga ba zan iya ba. Nayi alƙawari !”
“Kin tabbatar?" Ya tambaye ta.
“Eh, na tabbatar."
“Cool, toh yaushe zaki fara zuwa?"
“Daga gobe." Ta bashi amsa. “Friends ɗina zasu yi min bayanin abinda nayi missing. Na tabbatar ba zan sha wahala ba."
Washe gari Afnan, tayi sammakon tashi, domin shirin zuwa school. Farin ciki da fargaba take ji lokaci guda. Ta kasa daina yiwa kanta tambayar ta yaya zata yi idan taje gaban ajinsu. Ƙoƙarin ƙin yin tunanin tayi a halin yanzu.
Wannan karon cikakkiyar shigar hausawa tayi akan da da take cin gayunta. Tayi tunanin yin wannan shigar ba zai janyo hankalin mutane ba kanta, saidai koda Ammar ya sauke ta bakin ƙofar school ɗinsu, idanu suka yo kanta.
« Me yasa tayi irin wannan shigar? »
« Me yasa ta ɓace aka daina ganinta? »
« Ya naga tayi rama? »
« Wata ƙila ciki tayi »
« Wata ƙila wani makusancinta ta rasa. »
Wannan kallon ƙurallar da ake yi mata ya biyo da irin waɗannan tambayoyin. Afnan ta ji ta a takure, ƙafafuwanta suka fara rawa. Cikin ikon Allah, wata ƙawar Afnan mai suna Azima da take zuwa kullum a makare sai gata ta ɓullo. Afnan ma tayi tunanin zuwa da wuri zai sa abinda yake faruwa yanzu kar ya faru.
“ƘAWATAAAAAA." Azima ta ƙwalla ƙara tare da rungume Afnan da ta kusan kada ta.
“Mahaukaciya, me yasa kika ɓace tsawon wannan lokacin ba labari? Hankalina ya tashi sosai wlh. Har nace sai na hukunta ki idan kin dawo, amma yanzu murna ba zata barni ba.”
“Ai kin bari nayi magana ko.” Afnan ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace kanta daga jikin ƙawarta.
“Toh ina sauraron ki. Bani labari." Cewar Azima.
“Yanzu muje wani guri inda babu hayaniya, na gaji da idanun mutanen nan."
“Shikenan muje."
“Kowa tambayar inda kike ake, har Anwar ma." Cewar Azima.
“Har shi?" Afnan ta tambaye ta da mamaki.
“Eh har shi.” Azima ta bata amsa. “Kowa a makarantar nan yayi missing ɗinki."
Har da haka Afnan mamaki take Anwar ya tambayi ina take. Haɗuwarsu ta ƙarshe basu kwashe da daɗi ba. Har yau tana tuna cacar bakinta da shi. Ita da Anwar ba soyayya suke ba, a gaskiya tsakanin su biyun ba wanda zai iya ba alaƙar dake tsakanin su suna koda duka makarantar ana kallonsu a matsayin masoya. A koda yaushe suna tare cikin makaranta, idan abu na daɗi ya samu ɗaya daga cikinsu su taru suyi murna haka ma na baƙin ciki. Alaƙarsu tafi ta abokai, haka kuma bata kai ga soyayya ba.
Saidai, abinda ya faru da Afnan yasa ta fara nesa da Anwar da sauran mutane. Jin haushin wannan sauyin na Afnan da kuma ƙin gaya masa abinda ke damunta Anwar ya ɗau da zafi da har hakan ya kai su ga faɗa sosai. Suka faɗawa junansu maganganu marasa daɗi da bai dace su faɗa ba....
“Hello, kina jina kuwa? Cewar Azima ganin hankalin ƙawar tata na wani waje.
“Eh, sorry na harba wata duniyar ne."
“Naga alama, amma ya kamata ki faɗa min abinda yasa kika ɓace. Please ina so in sani."
“Rashin lafiya nayi Azima."
“Rashin lafiya?” Azima ta tambaye ta da alamu maganar ƙawarta bata gamsar da ita ba.
Daidai tana ƙoƙarin balbale ƙawar tata da masifa, sauran ɗalibai suka fara cika ajin.
“Ba zan rabu da ke ba, sai kin bani labarin abinda ya faru."
Kaɗa kai Afnan tayi, ta cigaba da gaisawa da sauran abokananta. Bayan wasu mintuna da fara darasi, sai ga Anwar ya shigo aji.
Afnan ta ga Anwar bai sauya daga yanda yake ba. Yana nan siririnshi, kyakkyawa ga ɗaukar wanka. Koda ya shigo ya haɗa ido da Afnan, yayi sauri ya kauda kanshi tare da samun guri cen karshen aji ya zauna.
Anwar ya share ta. Hakan kuwa ba ƙaramin taɓa mata zuciya yayi ba. Tana tunanin ko har yanzu yana cikin fushin abinda ya faru ne tsakaninsu.
Azima da ke gefe tana kallonsu ta girgiza kai, ta sa ran ko zasu dawo kamar da domin tasan Anwar yayi kewar Afnan sosai. Kusan kullum sai ya tare ta ya tambaye ta ina Afnan. Jin kanshi yasa bai ɗauki waya ya kira Afnan ko ya tura mata text ba amma Azima tasan irin damuwar da ya shiga na rashin jin labarin Afnan.
Dan haka tayi alƙawarin daidaita tsakaninsu su koma kamar baya.
(.....)
A ɓangaren Ammar koda ya ajiye ƙanwarsa gidansa kuma ya tabbatar tana cikin tsaro, yayi saurin kaɗa motarsa zuwa gidan ɗan uwansa Kamal. Ya ƙagu ya sanar da ɗan uwansa labari mai daɗi game da Afnan. Yana jin kamar ya kai shekaru aru-aru rabon da ya yi magana da Kamal. Ba wani abu mamaki bane, domin wannan lokacin babu wanda yake da time ɗin wani. Dan haka wannan ranar ta zama kamar wata babbar rana da zasu samu su yi magana.
Ammar bayan ya sauko daga aiki a gajiye yake amma haka ya biya makarantar su Afnan ya ɗauko ta. Afnan tace masa kar ya ƙara wahalar da kansa, tafi son komai ta yi da kanta saidai Ammar ba zai iya hana kanshi hakan ba. Yana ma so ya ɗauki wani da zai dinga aikin kai ta da ɗauko ta, har ma kula da ita.
Ƙarfe takwas da arba'in da biyar na dare Ammar ya iso gidan Kamal. Knocking Ammar yayi na wasu ƴan daƙiƙu kafin Kamal yazo ya buɗe masa. Ammar koda ya ga ɗan uwan nasa ya fahimci ba lafiya ba, ya ji tsoron ko rashin lafiya ɗan uwan nasa yake yi ba tare da ya sani ba.
“Lafiya kuwa? Ya naga duk ka koɗe?” Ammar ke tambayar Kamal yana rufe ƙofa bayan ya shigo.
“Yauwa Ammar gara da kazo."
“Idan haka ne me yasa baka kira ni ba?" Ammar ya tambaye shi.
“A'a bana son takura ka ne. Kai ma kana da naka matsalolin a halin yanzu."
“Ai da ka kira ni." Cewar Ammar.
Falo suka shiga tare da zaunawa bisa kujera. Ammar bin ko'ina yayi da kallo ya ga yanda falon yayi. Littafai ne ko'ina. Bai san dalili ba.
“Duk me ya kawo wannan littafan nan, kuma me yasa naga duk littafai ne game da aljanu? Ban fahimta ba." Cewar Ammar bayan ya ga sunayen da ke jikin littafan.
“Akwai wani abu dake faruwa a rayuwata kuma na tabbatar Amriya tana da hannu a ciki."
“Wacece kuma Amriya? Ko zaka iya min bayani?" Ammar ya tambaye shi.
“Ya kamata in ga Zahara, ina son inyi magana da ita."
“Wace alaƙa Zahara take da da wannan? Abinda na lura da shi, ba kun rabu ba? Ai sai da na faɗa maka nace idan kasan ba aurenta zaka yi ba, kar ka fara soyayya da ita. Bayan ka gama wasa da hankalin baiwar Allah yarinyar nan, daga ƙarshe ka koma ga best friend ɗinka alhali sai da ka rantse min ba son Khadija kake ba." Ammar ya faɗa rai a ɗan ɓace.
Kamal ajiye littafin da ke hannunsa yayi a hankali sannan ya dubi ɗan uwansa.
“Ka saurari me zan faɗa maka, ina son Zahara, ba ƙaramin so ba. Ka yarda da ni har zuwa yau na kasa fahimtar me yasa naji ta fita a raina. Lokacin da na ganta ɗazun, kamar duk wata soyayyar da nake mata da ta goge, ta dawo. Na fahimci duk wannan yana daga cikin siddabarun Amriya. Ta shigo rayuwarmu, kuma a halin yanzu tana wasa da hankalina har ma da na Khadija. Bani da tabbaci amma ina tunanin tana nan kuma idan haka ne Zahara, Khadija, ni wata ƙila har da kai muna cikin haɗari."
“Bansan me ka sha ba amma ko ma meye yanada ƙarfi sosai da zai sa ka ƙirƙiro wannan labarin marar ma'ana. Ina tunanin ya kamata na kai ka asibiti domin ka fara cin kai Kamal." Ammar ya faɗa yana taɓa gishin ɗan uwansa da yayi zafi gau.
Ammar ƙarawa yayi da cewa
“Ka gani, zazzaɓi ma gare ka. Na fahimci dalilin da yasa kake faɗar duk wannan shirmen. Kwanta, bari na kira doctor..”
“Daina ɗauka ta mahaukaci, dagaske nake ! Wannan aljanar ta shiga jikin Zahara... Shi yasa ta dinga yin wasu abubuwa bizarre a baya. Ya kamata ka san hakan domin kai ma hakan ya shafe ka."
A hankali Ammar ya fara tuna wasu abubuwa bizarre da Zahara ta dinga yi a baya. Kuma bata daina sauyawa ba. Zaharar yau daban, ta gobe daban. Amma hakan ba shi ke nuna akwai shafar aljanu a ciki ba.
“Ka yi tunani, zaka ga abinda na faɗa yana da ma'ana. Ni shaida ne akan duk wannan, kuma yau ɗinnan naga irin sauyin ga Khadija. Ta canza lokaci guda ! Ya kamata mu kora ta daga nan kafin ta cutar da mu da kuma baby."
“Wane baby?" Ammar ya tambaye shi har yau kansa a ɗaure.
“Khadija tana ɗauke da cikina, bansan ta yaya ko tun yaushe Amriya take cikin jikinta ba amma ya kamata na tseratar da su."
Ammar iya ƙoƙarinsa yake ganin ya iya lodar duk zancen nan da ɗan uwansa ya yi masa amma sun yi girman da ƙaramar ƙwaƙwalwarsa ba zata ɗauka ba. Yana so ya gaskata Kamal amma ya kasa.
Ɗauko wayarsa yayi yana ƙoƙarin kiran Doctor a sace amma wani ya shiga dukan ƙofa da iya ƙarfinsa.
“Waye wannan ke dukan ƙofa haka? Ko akwai wani da kake jira ne?" Ammar ya tambayi Kamal.
Girgiza masa kai Kamal ya yi alamar a'a kafin Ammar ya je ya buɗe.
Kasa motsawa yayi tsabar mamakin ganin mai bubbugar ƙofar cikin wani irin yanayi.
To be continued...
Like, Comment and Share Please.
AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story📖
By Malik al-Ashtar 🖋
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35