Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

CHAPTER 18

Amriya Hatsabibiyar Aljana Book 1 Complete Hausa Novel 2,189 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚

ZAHARA

Koda suka isa gidan Kamal, yayi mata nuni da ta zauna. Ajiye files din tayi bisa center table, ta fara aikin gyaren su kafin ya dawo. Dawowa yayi falon, ya sauyo kayan jikin sa, sannan yaje ya kawo mata abin sha duk da tace masa bata jin kishi. Bayan anyi haka, ya kama mata suka fara gyara documents din. Sai wajen karfe tara na dare sannan suka kare.

“Bari na hada wani abun da zamu ci.” Cewar Kamal. Ita kuwa Zahara gida take son zuwa ganin har dare ya fara yi.

“Nagode, amma gida zan je, bana son hankalin mama ya tashi. Domin ban fada mata zan kai warhaka ba.”

Mikewa yayi tare da ce mata ba zai dau lokaci ba, zai dafa wani abun marar nauyi ne. Ya fada ba tare da ya jira jin me zata ce ba, ya shiga kitchen.

Yanke shawarar kara yan mintuna tayi, da wannan damar tayi amfani ta shiga gyara wasu documents din.

Mintuna da dama suka zo suka wuce, amma Zahara bata ga Kamal ba, saidai motsi da take jiyowa daga kitchen, gajiya tayi da jira har ta kai ga tashi domin leka shi. Dariya ta kusan kwace mata lokacin da ta tarar dashi ya rike murfin tukunya da niyyar garkuwa da shi kar mai ya waltsar masa. Fiddo farfesun kaza yayi daga cikin freezer, yana kokarin soyawa.

“Kar ki karaso nan, dan zaki kone.” Cewar Kamal.

“Kawo, bari inyi..” Zahara tace tana mai kokarin karasawa.

“A'a.. kar ki matso dan zaki kone. Zan yi kar ki damu.”

“Ba lallai mu samun cin abun nan ba a yanda yake yi, bari ni zan yi ka yarda da ni.” Zahara ta fada tana mai karbar murfin tukunyar daga hannun sa. Dan ja baya yayi kafin ya yarda ya bar mata.

Sai da ta jira man ya daina turiri sannan ta kalle shi, tana tunanin reaction din da yake jira kenan domin dan murmushi yayi mata. Ita kuwa tayi sauri ta mayar da hankalin ta kan suyar farfesun kafin ta sume dan kunya.

Nacewa yayi sai yayi miyar farfesun, ita kuwa ta cigaba da suyar. Suna cikin shirya dinner, suka ji ana knocking kofa. Annurin fuskar sa ne ya sauya zuwa wacce ke dan ba Zahara tsoro. Wanke hannu yayi sannan yaje ya bude kofar.

“Me kika zo yi nan?” Zahara taji ya fada amma bata jin me dayan ke cewa.

Ji tayi an rufe kofa, taji sautin tafiya na nufo inda take. Cokalin dake hannunta ta damke sosai, tana tunanin ko mahaifiyar su Kamal ce. Har ta fara tunanin kunyar da zata kwasa idan ta hada ido da mahaifiyar Kamal. Wani tunani zata yi a kanta? Ta ganta tsamo tsamo cikin gidan danta a daidai wannan lokacin, ba wata uwa da zata yarda da wannan. Duk da ba komai suke aikatawa ba, ba zata fahimci hakan ba ita. Wayyo Allah, yanzu ya zata yi? Da tun dazu tayi tafiyar ta amma ta biyewa son zuciyar ta na kara son kasancewa da Kamal.

Saidai tsoron Zahara ya ragu lokacin da taga wata matashiyar budurwa ce ta shigo kitchen din. Kusan farin ciki ne ya saukarwa Zahara ganin ba daya daga cikin yan gidan su Kamal bane. Amma sai ta fara tambayar kanta wannan kuma wacece kuma me take yi nan a wannan lokacin?

“Ooh kenan da wannan yarinyar ce kake cin amanata?”

Wani irin bugu zuciyar Zahara tayi, kafafuwanta suka yi sanyi, hannuwanta suka hau bari. A ranta tace kenan yana da budurwa.

“Hafsat stop.” Kamal ya fada yana shigowa cikin kitchen din shima. Zahara tayi zaton zai mata bayanin dalilin da yasa yake kulata alhali yana da budurwa, amma sai taga ya saki fuska ba tare da ya kula wacce ya kira da Hafsat ba.

Yanada kwarin gwiwa har haka? Dole ma tayi tafiyar ta gida ! A hankali ta ajiye cokalin hannunta saidai a daidai lokacin wacce ya kira da Hafsat ta tuntsure da dariya.

“Dubi yanda duk ta tsorata! Kwantar da hankalin ki yar uwa, wasa nake yi. Kamal, me yasa dan uwanka bai daukan kirana?”

Juyowa Kamal yayi gun Zahara yace
“Are you okay? In kama miki ne? Ko murfin tukunyar zan iya rike miki, tinda ni na kare miyar.”

Zahara har ta manta da wai ana numfashi. Me take iya yi bayan abinda ya faru yanzu? Hafsat tace mata wasa ce take mata amma ita ta kusan suma. Tana tunanin ita kadai ta damu da abun, domin a yanda ta lura da Kamal, ta saba da yi masa irin haka. Sai da ta dan yi jim tana tattaro nutsuwar ta sannan ta bashi amsa.

“No, kar ka damu. Nima na kusan gamawa.”

Tambayar da ke mata yawo cikin kai ita ce. Wacece Hafsat kuma meye tsakanin ta da Kamal?

“Kamal wai mafarki nake yi ne? Ai bansan kaima kana dukowa mace har haka ba.” Hafsat ta fada tana kallon Zahara kamar taga bakuwar halitta, ita kuwa Zahara tayi sauri ta kauda kanta.

“Hafsat you shut up, ko na kora ki waje.”

“Ba zan tafi ba, Ammar bai daukan kirana. I hate when he treats me irin haka, ina son yin magana da shi.”

“Toh ni meye nawa a ciki?” Ya tambaye ta. “Idan kinada matsala dashi, shi zaki gani ku warware matsalar ku. Me kike so ni nayi?”

“Ka ce masa ya dinga daukan call dina idan na kira shi. Idan kuwa ba haka ba..”

“Tsakanin ku ne, ni babu ruwana. Kina tunanin zan iya saka shi abinda bai niyyar yi ba? Ki je ki neme shi kuyi magana zai fi, batawa kanki lokaci kawai kike yi nan.”

“Daman nasan ba nan ya dace inzo ba mtsw..”

“Zaki iya tafiya please.. muna son karasa girkin nan.”

“Toh ba zaka gabatar da ni ba gareta?” Ta tambaye shi.

“Sunanta Hafsat Abubakar..” Katse shi Hafsat din tayi, sannan ta kama hannun Zahara suka gaisa tare da yi mata murmushi.

“Sunana Hafsat, kuma ni kawar shi ce tun muna yara.”

Tabe baki Kamal yayi, ita ma Zahara tayi mata murmushi tare da nuna mata jin dadin haduwar su ba tareda Hafsat ta sakar mata hannu ba.

“You are still very young compared to him. Soyayya kuke? Yaushe kuka hadu? Injin dai kinsan dan ta'adda ne shi, zai miki wankin kwalwa sannan... AHHHH SAKE NI!” Kamal ne yaja hannunta da karfi domin ya fiddata daga kitchen, yana fidda ta ya rufo kofar da key.

“I'm really sorry for that, bansan zata shigo haka ba.”

“Kar ka damu na fahimta.”

Hafsat bugun kofar kitchen din take ba kakkautawa. Amma jin Kamal yace idan bata daina ba zai fitar da ita daga gidan gaba daya sannan ta daina. Hakan har dariya ya baiwa Zahara.

Koda suka gama hada farfesun kazar, suka dawo falo. Kamal duk da dan haushin da Hafsat ta bashi sai da ya dauko mata ita ma plate. Lokacin da suka dawo falo, suka tarar da ita kwance bisa doguwar kujera, da yanayin damuwa a fuskarta. Daina kallonta Zahara tayi kafin ta lura da yanda ta kura mata idanu.

Ajiye komai suka yi bisa center table, Kamal ya koma ya dauko juice da ruwa.

Zaune Zahara tayi bisa daya daga cikin kujerun, shi kuwa duk da yalwataccen wurin dake akwai, kusa da Zahara ya zauna. Bai dade da zaunawa ba yaji ana knocking kofa. Tashi yayi yaje ya bude.

Zahara bata gama tunanin wannan karon waye yazo ba, taga Mr. Ammar ya shigo falon tareda hade gira yayinda ya ganta. Idan da kunya na kashewa da tuni Zahara ta dade cikin kasa. Kara tumbuke fuska yayi lokacin da yaga Hafsat kwance bisa kujera. Da sauri Hafsat ta tashi zaune. Zahara ta fahimci akwai wata kullalliya tsakanin su, a yanda taga suna harar juna.

“Me kike yi anan?” Mr. Ammar ya tambayi Hafsat.

“Kana raye ashe. Ni da nayi tunanin kana kin daukan kirana ne saboda aiki yayi maka yawa.”

“A'a.. ina jin dadin ganin kallon wayata yayin da naga sunanki ya bayyana. Ban ma san me yasa har yanzu nake da contact dinki ba.”

“IDIOT..” Hafsat ta fada cikin daga murya, tareda tsalle da niyyar kama shi da kokowa, shi kuwa ya kauce ta fadi kasa. Har tana kokarin jiwa kanta ciwo, amma bata kula hakan ba, ta mike ta sake nufar Mr. Ammar din.

Zahara kallon scene din take da mamakin ganin yanda matasan ke nuna zallar tsanar junan su. Bata yi gangancin cewa wani abu ba, sai ma tattara kayanta da ta shiga yi da niyyar barin gidan sai ga Kamal ya shigo falon.

“Please, idan kashe junanku kuke son yi ku koma kitchen. Yinin yau aiki muka yi kuma yunwa muke ji yanzu. Please respect us, ku samu wani wurin ba nan ba.” Kamal ya fada cikin sigar lallashi.

“Me take yi anan ne? Me yasa ka gayyato ta?”

“Nazo na fada masa ya ja maka kunne, ko ka manta I have your future in my hands. Ni ce wacce zaka aura.” Cewar Hafsat.

“Wacce zan aura fa kika ce? Ai nafi gwammace na mutu da na aure ki. Dan haka zo ki fice ki bar gidan nan.”

Da wannan umarnin da ya bata, ya kamata da niyyar fitar da ita amma ta subule tareda komawa kan kujera ta zauna.

Dogon numfashi Kamal yaja tareda daukan plate biyu yace Zahara tabi bayanshi. Tattare kayanta Zahara tayi ta sudada tabi bayan Kamal ba tare da ta kalli inda su Ammar suke ba. Key din mota Kamal ya bata riko, sannan yace ta biyo shi. Taimaka masa tayi wajen bude motar, sannan suka shiga ciki.

“Barinsu su kadai zaka yi a ciki?” Zahara ta tambaye shi.

“Su kashe kansu, muna zaunen mu sun zo sun takura mana. Nan gaba best restaurant na garin nan zamu je, inda babu irinsu a wurin.”

Yar dariya ta kwacewa Zahara, domin har nan suna jiyo su Ammar.

“Mu ci abun nan kafin yayi sanyi. Daga nan sai na kaiki gida kar dare ya kara yi.”

“Thanks for this kuma nagode da taimaka min da kayi. Da ba dan kai ba da yanzu ban karasa aikin nan ba.”

“Me yasa kike gode min? Believe me, I did it with pleasure. Dan haka ki daina gode min, kin ji ko?”

Murmushi tayi sannan ta bashi amsa
“Ok.”

“Yanzu ci abincin nan.."

Idan ta cigaba a wannan yanayin ba lallai ta iya barinshi ba. Domin wannan ne karon farko da ta dade tareda wani irin haka, duk wannan sabon abu ne gareta. Tana jin wasu abubuwa wanda bata taba jinsu ba a baya. Tana kara samun kusanci da shi, alhali bata taba tunanin samun irin wannan kusancin ba da wani. Idan tana ita kadai, tana kan yi nadamar duk wannan domin tana tsoron wata rana ya kare da bakin ciki. Amma idan tana tare da Kamal sai ta manta da komai.

Har ina hakan zai dore?

(...)

AMMAR DA HAFSAT

Ganin bata da niyyar tsagaita masifar tata dole shi yayi shuru.

“Yanzu me kike so ne Hafsat?”

Zaunawa tayi nesa da shi, tayi irin zaman kamar wacce take jiran kai farmaki.

“Ina son ka daina share ni da kake yi. Kawai ina son mu zauna mu tattauna mu nemi mafita kan matsalarmu.”

“Ni fa ba zan aure ki ba, kuma game da neman mafita na nema duk inda ya dace amma banga wata mafita ba.”

“Mahaifiyata taki daina damuna da wannan zancen, nima inada matsalolin da nake son warwarewa. Idan fa muka yi aure domin rufe bakunan su na dan wani lokaci?”

“Kiyi tunani, zamu yi aure ne domin farfado da kamfanin mahaifin ki da yake kokarin durkushewa. Idan muka rabu bayan wasu yan watanni, kara jagule matsalar ne zamu yi.”

Dafe kai Hafsat tayi tare da jan dogon numfashi.

“Idan da ta nice da tuni kamfanin ya dade da durkushewa, amma mahaifina na son kamfanin sosai.”

“Nasan abinda kike tunani, amma ba zan aure ki ba, koda da wasa ne."

Kallon shi tayi.
“Tsanar da kake min har takai haka?” Ta tambaye shi kamar zata yi kuka.

“Ba wani sabon abu bane, bari yi kamar yanzu ne kika sani.”

“Ok good.. na fahimta, ina ga ni zan tafi gida.”

Mikewa tayi ta nufi hanyar fita. Shima mikewa yayi ya dauki makullen motar shi saidai a daidai lokacin Hafsat ta juyo tace masa.

“Nima na fara jin tsanarka, kuma idan baka daina abinda kake ba, na rantse maka sai kayi nadama.”

A hankali ya tako inda take, ganin jikinta yayi sanyi. Ya hade bakunan su.

Mayar masa da martani itama tayi, tana kokarin zagayo da hannuwanta a wuyansa, ya dakatar da ita ta hanyar janye jikinsa.

“Yanzu na fahimci dalilin da yasa kike son aure na ko ta yaya. Wannan kiss din zai kwantar miki hankali, zaki iya tafiya.”

Marinshi tayi tareda kwada masa jakar hannunta.

“Banza kawai..” Ta fada tana kokarin boye hawayen da ke son zubo mata. Saidai tuni ya riga da ya gani.

Ficewa tayi da gudu tana kuka, shi kuwa ya kada kafada irin ko a jikin sa.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
  2. 2 CHAPTER 1
  3. 3 CHAPTER 2
  4. 4 CHAPTER 3
  5. 5 CHAPTER 4
  6. 6 CHAPTER 5
  7. 7 CHAPTER 6
  8. 8 CHAPTER 7
  9. 9 CHAPTER 8
  10. 10 CHAPTER 9
  11. 11 CHAPTER 10
  12. 12 CHAPTER 11
  13. 13 CHAPTER 12
  14. 14 CHAPTER 13
  15. 15 CHAPTER 14
  16. 16 CHAPTER 16
  17. 17 CHAPTER 15
  18. 18 CHAPTER 17
  19. 19 CHAPTER 18
  20. 20 CHAPTER 19
  21. 21 CHAPTER 20
  22. 22 CHAPTER 21
  23. 23 CHAPTER 22
  24. 24 CHAPTER 24
  25. 25 CHAPTER 23
  26. 26 CHAPTER 25
  27. 27 CHAPTER 26
  28. 28 CHAPTER 27
  29. 29 CHAPTER 28
  30. 30 CHAPTER 29
  31. 31 CHAPTER 30
  32. 32 CHAPTER 31
  33. 33 CHAPTER 32
  34. 34 CHAPTER 33
  35. 35 CHAPTER 34
  36. 36 CHAPTER 35
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});