Chapter 27
CHAPTER 26
I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 26 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”
http://www.ashblogg.com.ng/2022/02/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-26.html
“Sai an wuce asibiti gidansa yake ko kuwa kafin a kai? Ina tunanin na ɗan manta takamaimai inda gidan yake.” Maryam ta cewa Zahara da sigar wasa.
Zahara gyara ɗakin da ta duk yamutse tayi, ita kuwa Maryam ta zauna bakin gado tana kallonta.
“Well, ina ga kinada gaskiya, ba shawara ce mai kyau ba zuwa gidan Kamal koda kuwa ina son zuwa. Bansan me zan ce masa ba, kuma nasan lamarin ne zan ƙara dagulewa maimakon inyi gyara.” Cewar Maryam.
“Naji daɗi da kika gane hakan, ban son yayi tunanin ni marar yawo ce da ba zan iya mantawa da komai ba, na cigaba da harkar gabana. Ina son cigaba da rayuwata kamar baya, wacce nake yi kafin in san shi.” Cewar Zahara.
“Ba rashin wayo bane gareki, ke mutum ce shi yasa. Wannan ce wahalar soyayyarki ta farko, kuma kinada ƴancin yin kuka. Amma kinada gaskiya, yanada kyau kiyi gaba, ki ƙara sanin wasu sabbin abubuwan rayuwa. Saidai ba zai yiwu na barki ki koma rayuwarki ta baya ba, a'a wannan ba yiyuwa bane. Zahara lokaci yayi da zaki zauna kiyi tunani akan ƙarancin yardarki. Ya kamata mu nemo wata hanyar canza hakan.”
“Ba abu bane da za'a iya zancawa, yau ko gobe." Cewar Zahara.
“Haka ne, amma ke babu wani ƙoƙari da kike yi. Zan kama miki amma kece zaki yi aikin mafi muhimmanci.”
“Eh na sani Maryam, ki yarda da ni, ina son na canza."
“Toh, yanzu mu ɗan fita. Mu je muci wani abun a waje."
“Ina?”
“Suprise ne!”
“Idan mijinki ya kira fa?"
“Bah what? Ni ba prisoner shi bace, ina zuwa inda nake so. Essential shine nasan inda nake saka ƙafata. Ya yarda da ni kuma yasan adadin yanda nake sonsa.” Maryam ta faɗa tana murmushi.
“Mtsw sannu Romeo da Juliet. Well.. ina son fita amma na gaji ba zan iya ba.” Zahara ta faɗa tareda komawa bisa gado tayi kwanciyarta.
Ba tareda ta shirya ba taji Maryam ta janyo ta daga bisa gadon, sai gata ta faɗo ƙasa.
“Wayyoo karya ni kike son yi ko me? Da fa na karya hannu.”
“Hannun naki ya karye ne?” Maryam ta tambaye ta.
“Ina tunanin bai karye ba amma...”
“Good, tashi kiyi wanka, ni zan fiddo miki kayan da zaki saka.”
“Hum ban yarda da ke ba, idan basu mini ba, ba zan saka ba."
“Ban damu da ra'ayinki ba, oya je kiyi wanka sai wari kike!”
“Nan fa ƙarya kike yarinya.” Zahara ta fada tareda tashi daga ƙasa.
“Ki je kiyi wanka ki daina wannan surutun dan Allah!” Cewar Maryam tareda jefawa Zahara pillow.
“Zan je dan Allah, daina ɗaga murya.” Zahara ta faɗa tareda shigewa bathroom kafin Maryam ta tashi gidan.
BANGAREN KHADIJA
Khadija na tunanin ciki ne da ita. Bata da wani ƙonƙonto akan hakan. Tun bayan wasu makonni, take jin alamar symptoms na mai ciki. Tana yawan jin kasala, ga yawan fitsari duk bayan mintuna goma alhali da tana iya riƙewa na yini guda bata yi fitsari ba. Da farko ta fara tunanin ita ce ke sa hakan a ranta, amma mamanta suka fara yi mata ciwo, da safe ƙwarnahi bai rabuwa da ita. Kuma wannan safiyar bayan ƙwarnahi sai ga yawan jiri. Ba coincidence bane idan hakan ya faru.
“Karɓi je kiyi gwajin." ƙawarta Sa'adiya tace mata.
Karɓa tayi ta sauka daga kan gadon ta nufi ban ɗaki.
Khadija karɓar test pregnant ɗin tayi. Murna ce da damuwa suka cakuɗe mata wuri ɗaya. Bata san takamaimai me take ji ba. Ta so irin wannan ya biyo bayan aurenta da masoyinta Kamal amma ƙaddara ta ɓullo mata ta wani wurin daban. Yanzu bata sani ba idan ya dace ta damu domin bata san ya Kamal zai ji ba. Tasan Kamal ba zai taɓa musa cewa ba nashi bane. Tambayar shine jin zai yi amanna da cikin kuma ya zamar masa uba?
Tambayoyi ne da dama cikin kanta.
Gwajin kuwa ya nuna bata yi kuskure ba tana dauke da cikin Kamal.
Fitowa tayi daga cikin ban ɗakin. Sa'adiya da ke faman jiranta ta warce test pregnant ɗin daga hannun Khadija. Lokacin da taga result din ta juya gun ƙawarta tareda rungumeta.
Khadija cikin kuka tace mata :
“Zan je na faɗawa Kamal, zan je wajenshi yanzu."
“Bansan me zan ce miki ba, amma ki kwantar da hankalinki nasan Kamal ba zai taɓa barinki ba. Amma ina baki shawara da ki bari har gobe sai ki je wajenshi kafin nan kin samu nutsuwa."
“Kinada gaskiya.” Khadija ta bata amsa tana goge hawaye. “Zan kwanta yanzu, domin ina buƙatar hutu."
“Me kike ji yanzu?” Sa'adiya ta tambaye ta tana mai taimaka mata dan ta zauna bisa gado.
“Ban sani ba, a halin yanzu komai confusion ne.”
“Yaro a kullum albarka ce daga gun ubangiji. Kuma kin jima kina son ɗa, duk da ba irin wannan hanyar ba amma abinda ya faru ya riga ya faru. Kuma abu na karshe da nake son faɗa miki ko ba komai yanzu ke da Kamal kun zama ɗaya har abada."
Khadija tayi nisa cikin tunani, ƙawarta tanada gaskiya wannan cikin zai ƙara haɗa soyayyarta ne da masoyinta.
“Ni ina ga cikin ba komai zai kawo miki ba face alkhairi nan gaba. Bayan kin haihu, wata ƙila Kamal ya aure ki. Kin ga kin samu abinda kike so da jimawa. Dan haka ki daina yiwa kanki wasu dubban tambayoyi.”
“Shikenan, may be kinada gaskiya. Bari na ɗan huta."
“Ok, nima bari naje na haɗa dinner. Kafin nan zaki iya yin baccinki.”
Sa'adiya ta bar ɗakin bayan ta taimakawa Khadija ta kwanta. Ta rufe mata rabin jikinta da bargo kafin ta kashe mata wutar ɗakin.
Duk da tayi alƙawarin ba zata yi ba, Khadija bata daina tunanin rayuwarta nan gaba da wannan cikin ba. Bayan ɓata awowi tana tunani daga ƙarshe bacci ya ɗauke ta.
Saidai bata sani ba, baccin nata shima ba wurin hutu bane.
Cikin bacci, Khadija ta tsinci kanta ƙofar gidan Amriya. Ta tuna haɗuwarsu ta farko a nan. Kallon baƙaƙen busassun fulawowin da suka kewaye gidan take. Wanda hakan koda yaushe ke sa mata tsoro. Wannan karon bata jira sai ta shiga ciki ba kafin ta ga Amriya. Jin alamunta tayi a bayanta. Ba zata taɓa sabawa da sauyawar temperature ɗin jikinta ba idan Amriya na ga wuri.
Shafa kafaɗarta Amriya tayi da ya sanya ta zabura amma tayi saurin daidaita nutsuwarta domin kar ta nunawa Amriya ta tsorata. Kallonta Khadija tayi wannan karon cikin ido. Amriya na da idanu mafi kyawo a duniya ko kuma ince Khadija bata taɓa ganin wani da kyawun idanu irin Amriya ba. A duk lokacin da ta haɗa ido da ita sai taji komai na jikinta ya daina motsi, ta kasa kallon wani wurin.
“Kar ki tsorata." Amriya ta raɗawa Khadija a kunne kafin ta kama hannunta.
Kamar da ƙyaftawar ido suka bayyana cikin wani ɗaki na jariri da wani ƙaton madubi gaban ɗan gado na jariri. Kyakkyawan ɗaki ne sosai kuma mai girma da yasa Khadija taji ta zama ƴar ƙarama a ciki.
Tuni ta sani kenan? Khadija ta raya a zuciyarta.
“Ba dai kina tunanin ki ɓoye min ba?” Amriya ta faɗa.
“A'a..nima..ban daɗe da sani ba. Bansan inada ciki..”
“Munada ciki dai zaki ce." Cewar Amriya. “Ni ce keda ciki...ba ke ba.”
“Kamar yaya?”
Khadija ta faɗa tareda juyowa ta kalli Amriya amma Amriya ta ɓace kuma ɗakin babyn da yake duka fari ya sauya launi zuwa ja.. jini ya bayyana ko'ina a jikin bango, a ƙasa, a jikin labulaye har ma bisa ɗan gadon jaririn. Khadija ji tayi ƙafafunta sun kasa ɗaukanta. Bata yi aune ba tayi wata muguwar faɗuwa ƙasa sai kuma ga Amriya ta bayyana cikin madubi.
“Kina tunanin idan bani nan, Kamal zai kwanta da ke? Duk wannan da kika ga ya faru saboda ina cikin jikinki ne. Ni yaji yana sha'awa, shi yasa har hakan ta faru. Duk wannan sha'awar da kika ga ya nuna a kanki a wannan daren, saboda ina wurin ne. Ni yake so ba wai ke ba."
“Ƙarya kike, maƙaryaciya ce ke!” Cewar Khadija.
Ɗakin ne ya fara wani girgiza, ƙwan fitilar dake ɗakin ya fashe kuma kujerar dake kallon ɗan gadon jariri ta juyo da ƙarfi tana fuskantar Khadija.
“Bana jin daɗi idan bil'adama na zagina. Amma ke ba zan yi miki komai ba domin kina ɗauke da ɗana. Zan cigaba da kulawa da ke har lokacin da zaki haife shi.
Khadija da ƙaraji tace
“ƊANA NE NI KAƊAI KINA JINA? KUMA BA ZAN TAƁA BARI KI ƘWACE MIN SHI BA.” Ta faɗa cikin ɓacin rai.
“Kina tunanin kinada zaɓi?” Amriya tace da ita kafin ta ɓace a jikin madubin.
Jariri ne ya bayyana gaban Khadija da ya kusa sa zuciyarta bugawa. Jaririn da fuskar Kamal amma baida wani abu na mutane, ko ƙafafunsa ba'a gani.
“Ranar da zaki haihu, lokacin da likitoci zasu ga jini a maimakon jariri, a ranar zaki gasgata da nawa ne."
Ƙwalla ƙara Khadija tayi ta yi. Jaririn ya ɓace sai ga Amriya ta bayyana wannan karon da ƙaton ciki a jikinta. Durkushewa Khadija tayi ƙasa wannan karon babu abinda ta iya cewa, so take kawai ta farka daga wannan mummunan mafarkin.
“Zan iya barinki a raye idan kina so. Amma idan kin amince zaki yi min wani abu.”
“Ɗana kawai nake so, dan Allah kar ki cutar da mu.” Khadija ta shiga roƙonta.
“Yaron nan dama nawa ne, kuma zai kasance a duniyata. Babu abinda zan iya yi. Na faɗa miki Kamal da ni ya kwanta a daren nan, ke kawai.. me ma zan ce..matsakaiciya yauwa kin ji sunanki.”
“Wannan yaron zai rayu cikin duniyata ko ma me zaki yi. Abinda kawai zan iya yi miki shine na barki a raye ki je ki cigaba da rayuwa da masoyinki wanda daman shine abinda kike so. Saidai zan yi hakan ne idan kinyi abinda nake so.”
Ba tareda ta jira jin abinda Khadija zata ce Amriya ta cigaba
“Ina son ki cire layar da ke hannun Zahara. Bansan yaushe ko ta yaya zaki yi hakan ba, amma idan har kika yi hakan ina mai tabbatar miki zan shafa miki lafiya kuma zan baki duk wata dukiya da kike so. Nayi miki wannan alƙawarin."
“Na ƙare haɗa dinner.”
Khadija ta farka tana ta haƙi da zufa. Muryar ƙawarta Sa'adiya ce ta cece ta daga Amriya. Amma tasan Amriya zata cigaba da dawo mata har sai ta amince tayi abinda take buƙata.
TO BE CONTINUED...
[04/03 à 10:09] ASHTAR: AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story📖
By Malik al-Ashtar 🖋
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35