Chapter 20
CHAPTER 19
⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚
HAFSAT
Wajen karfe bakwai lokacin da ta fara jin gajiya a jikinta. Daren jiya yana daya daga cikin darare mafi bakin ciki a gare ta. Tamkar kwalwarta ta shirya da gangan ta dinga nuna mata cin mutunci da ta gani jiya. A ranta tace ita ta jawa kanta, bata san dalilin da yasa take manta waye Ammar ba, wanda tun suna yara ya tsane ta, toh me zai sa wani abu ya canza yanzu?
Tana jin kunya idan ta raya a zuciyarta taji dadin wannan kiss din da yayi mata. A jiya tasha kuka cikin dan sahun da ya kawota gida. Ba wai tana kukan damuwa bane kawai, har da kukan haushi da takaici. Ba shi kadai take jin haushin sa ba, har da kanta. Wannan yanayin da take ciki ya sake tabbatar mata da irin galabar da Ammar yayi a kanta. Babu wani namiji da ya isa ya sata a wannan halin bayan shi. Ta kasa gane abinda take ji game da shi, idan ma sonshi take, shi ba sonta yake ba. Kuma dab take da yin hauka koda sunyi auren, koda kuwa auren wasa ne.
Tana tunanin lokaci yayi da iyayen su zasu fahimci ba mai yiyuwa bace tsakaninta da Ammar.
Da wannan tunanin tayi bacci jiya. Yanzu da ta tashi, taga baccin da tayi bai wuce na awa biyu ba. Ba wai dan ya isheta ba, ta tashi ta shiga wanka. Bayan ta fito, ta shirya tayi sallah sannan ta sauko kasa wajen mahaifiyarta dake karyawa.
Koda ta sauko, Mahaifiyar tata ta shiga yi mata fada.
“Saida fa na fada miki kece zaki yi girki yau. Tun karfe bakwai ya dace ki tashi dan ki fiddo nama. Kin fi kowa sanin lokacin da yake dauka kafin ya daskare sannan a soya.”
“Please Mama, kaina ne ke yimin ciwo. Ban yi bacci ba jiya.”
Tashi Mami tayi ta karaso inda Hafsat take tareda kallon idanun Hafsat da suka yi ja.
“Meke faruwa? Me ya hana ki yin bacci?”
Bata sani ba ko ya dace ta fadawa mahaifiyarta amma sanin halin da ake ciki shi yafi. Bayani tayi mata kan wulakancin da Ammar yayi mata da kuma korar karen da yayi mata daga gidan dan uwanshi. Wajen kiss ne kawai ta cire bata fadawa Mama ba.
Akasin abinda tayi tunani, cikin sanyin murya Mama tace
“Me kike son ayi yanzu kenan? Kinsan wannan auren yanada muhimmanci a family nan. Alakar ki da shi na sani da wahala, amma kema baki ganin ya kamata ki dinga jurewa? Kiyi kokarin fahimtar shi da kuma rarrashin sa? Maza kamar yara suke, saida rarrashi. Tattalin su kawai ake, yanzu zaki ga ya sauke duk wani aji nashi, yana miki biyayya yanda kike so.”
“Ina ga baki fahimta ba Mama. Mutumin nan ba sona ne baya yi ba, ya tsane ni ne. Ki yarda da ni abinda yayi min jiya, kalilan ne akan wanda ya shirya min idan na aure shi. Ina son taimakon baba da kamfani, haka ina son lafiyar kwalwarta kuma na cancanci namiji mai sona ba wanda yake kamanta ni da karya ba.”
“Kenan kina nufin ba zaki aure shi ba?” Mama ta tambaye ta da mamaki.
“Shi da kanshi ne ma ba zai amince da auren ba.”
“Mahaifiyarshi zata ji da wannan, ke dai ki fada min idan kina son auren.”
“Koda Mahaifiyar shi tayi abinda zai amince, nice zan wahala..”
“Kiyi tunani da kyau, kar ki watsawa mahaifinki kasa a ido. Kinsan iya adadin yanda ya kwallafawa abun nan rai.”
“Mama kinsan ina sonku, kuma bani da kamar ku a duniyar nan. Zan iya yin komai a kanku amma wannan gobena ce, kuma kin fi kowa sanin haka. Idan har na aure shi, zan kasance daga ni sai shi a cikin gidan, babu wani da zai kawo min dauki.”
“Hafsat me kike son na cewa mahaifinki? Yanzu ki barni inyi magana da mahaifiyar Ammar, zamu nemi mafita tare.”
“Mafita kawai ita ce a bar zancen auren nan, domin farin cikina ne a hatsari.”
“Kar kiyi gaggawar yanke hukunci, na tabbatar zamu nemi mafita bari yanzu zan kira Hajiya Karima.”
“Shikenan bari na fiddo naman.”
Bayan Hafsat ta bar wurin, Mahaifiyarta ta dauki waya dan ta kira kawarta Hajiya Karima. Ba'a dau lokaci ba Hajiya Karima ta daga. Bayan sun gaisa mahaifiyar Hafsat tace
“Na kira ki ne, ina son muyi wata magana.”
“Ina jinki.”
“Hafsat ce tace min jiya Ammar yaci mutuncinta tare da korarta daga gidan Kamal. Abun ya taba ta, tace min tana jin tsoron abinda zai biyo baya idan suka yi aure. Har so take a fasa auren a cewarta Ammar ba zai yarda ba. Kuma koda ya yarda a kanta zai huce.”
Bayan mahaifiyar Hafsat ta gama kora mata bayani, sai da Hajiya Karima ta dau lokaci kafin tayi magana.
“Yaron nan ya fara kaini bango. Abinda yaga dama shi yake yi, amma kawata kar ki damu kanki. Ki cewa yarki kar ta damu. Ina nan, nima mahaifiyarta ce kuma zan gyara komai da yardar Allah. So yake ya ja da ni saboda na hana shi auren karuwa amma zai san ban sha wahalar banza ba wajen haifo shi duniya. ”
“Hajiya Karima, ban fada miki hakan ba dan kiyi masa wani abun ba. Ki tambaye shi kawai idan yana son auren 'yata.”
“Zai ma aureta, ni na fada miki. Zai auri Hafsat kuma zai mayar da ita tamkar sarauniya idan ba haka ba, ba sunana ba Karima.”
Hajiya Karima ta kara da cewa
“Zan zo gidan naku cikin weekend din nan. Zaki ga yanda komai zai canza daga yau.”
“Ok, shikenan. Na yarda da ke kawata. Ina fatan komai yazo mana da sauki.”
(....)
HAJIYA KARIMA
“Da wa kike waya?” Cewar mijinta.
“Danka ne yake kokarin ya haukata ni, za'a yita ta kare yanzu yanzu nan. Ciwa Hafsat mutunci yayi gaban Kamal, gashi yanzu tace tsoron auren sa take.”
“Me zaki yi yanzu?” Ya tambaye ta.
“Rashin ladabi ne abinda yayi, family meeting nake son muyi yanzu. Saka kaya, ka same ni a falo.”
Bata jiran jin amsar shi ba, ta bar dakin. Zuwa tayi dakin Afnan ta tarar da ita har yanzu bacci take.
“Afnan, Afnan.."
“Hummmm.”
“Tashi, ki wanke fuska ki same ni a falo.”
Murza idanu Afnan tayi, ta tashi a hankali sannan ta kalli Hajiya Karima.
“Meke faruwa ne?” Ta tambaye ta hankalinta a dan tashe.
“Yi sauri kar ki bata min lokacin.”
Fitowa Hajiya Karima tayi daga dakin Afnan tare da rufo kofar, sannan ta nufi dakin Ammar. Kamar yanda tayi tunani baya nan. Ta tabbatar yana wurin aiki. Ta yanke kiran shi bayan ta kira Kamal.
Falo ta dawo inda ta tarar da mai aikin su Rakiya har ta gyara shi. Yanzu tana cikin goge corridor.
“Rakiya, hada min tea marar suga dan Allah."
Daidai lokacin, Afnan ta sauko sanye da abaya da gyale.
“Meke faruwa Mommy? Lafiya?"
Afnan ta fada fuskarta da yanayin firgici da ita kanta Mommy ta lura.
“Kar ki damu, ya shafi dan uwanki ne Ammar. Kira shi kice ya dawo gida da gaggawa ina neman shi.”
“Ina tunanin yana wajen aiki.” Cewar Afnan.
“Eh, ki kira shi kice masa yazo da hanzari ina jiran shi. Bari ni in kira Kamal."
“Ok, bari naje na dauko wayata daki, sai in kira shi.”
Koda Afnan ta tafi, Mommy ta dauki waya ta kira Kamal. Bugu na biyu ya dauka. Bayan yayi sallama ta amsa.
“Wa alaika salam, Kamal kazo gida yanzu yanzu ina son ganinka.”
“Lafiya meke faruwa?”
“Kowa lafiya, ni ke son ganinka kuma yanzu nake son kazo.”
“Ok gani nan.”
Yana katse kiran, sai ga Afnan ta dawo.
“Mom, Na kira shi amma yace min meeting gare shi mai muhimmanci, ba zai iya zuwa ba.”
“Ok, bani wayar je ki karbo min tea din da nace Rakiya ta hado min."
Debe password din tayi, sannan ta mika mata wayar. Sake kiran Ammar Mommy tayi. A ringing na biyu ya dauka.
“Afnan, wai ba nace miki meeting gare ni...” Bai karasa fada ba Mommy ta katse shi.
“Nice ba Afnan ba, Ammar idan baka zo ba nan da minti goma, na rantse maka sai kayi nadama."
“Amma Mom..” Katse kiran Mommy tayi tareda ajiye wayar kan center table.
Ammar da saurin shi ya shigo gidan, yana tunanin wani babban abu ne ke faruwa duk da jin muryar Mommy kamar ranta a bace yake. Koda ya faka mota, yaga ta dan uwanshi a bayanshi. Fitowa yayi tare da kulle motar.
“Kasan meke faruwa ne?” Ya tambayi Kamal da alamun shima cikin rudu yake kamar shi.
“A'a.. Mom ce tace nazo da gaggawa..” Kamal ya bashi amsa.
“Fatan dai Allah yasa lafiya, domin ni inada meeting mai muhimmanci."
Knocking kofa suka yi, Rakiya tazo ta bude musu. Gaishe ta suka yi ta amsa kamar kullum da murmushi.
Kai tsaye falo suka nufa, inda suka tarar kowa na gidan ya halarta, har da Daddy ma yana nan. Koda Ammar ya hada idanu da Mommy, ta galla masa harara da yasa shi shan jinin jikin sa. Tambayar Afnan yayi da kallo, amma ita ma da alama bata san meke faruwa ba. Sai ma gyangyadi da take yi, amma da Mommy tayi magana da babbar murya tayi firgigit ta tashi.
“Tunda dukan mu mun hadu, zan je kai tsaye akan abinda ya tara mu. Ammar ina son ka min bayanin abinda ya hadaka da Hafsat jiya.
Ammar a ranshi yace «ba dai ta kira ni bane dan ta yimin zancen yarinyar nan.»
“Kin kira ni daga office ne dan ki min zancen yarinyar cen? Kuma fa na fada miki inada meeting mai muhimmanci.”
“Ammar tambaya ta karshe zan maka, me ka yiwa Hafsat?”
A ranshi yace «Me kuma wannan sakaryar tazo ta fada?»
“Fada kawai nasan nasan munyi..."
“Ammar me yasa kake so ala dole sai ka cutar da ni? Ni kake cutarwa idan kana cutar da ita. Kuma kana ja min abun kunya gaban dangin aminiyata. Kana tunani kuwa kafin ka aikata wasu abubuwan ?”
“Amma mom..”
“A'a saurare ni Ammar, wannan ne na karshe da za'a kira ni dan kawo min koken bakin halinka. Shekarunka nawa? Ya kamata kasan ka girma.”
“Idan kana min haka ne domin nuna min jin haushina da kake saboda karuwar budurwarka, to ka sani ina kan bakana. Ka daina ciwa yarinyar nan mutunci, babu abinda tayi maka.”
“Mahaifiyarka na da gaskiya.” Cewar Mahaifinsa. “Yarinyar nan babu abinda tayi maka, banga dalilin da yasa kake wulakanta ta ba. Ba wannan tarbiyar muka baka ba. Abinda kake aikatawa ba wai mutuncinka kadai kake zubarwa ba, har da namu. Bana son irin haka ta sake kasancewa.”
“Ni fa duk wannan ba laifina bane. Me yasa kuke son na aure ta alhali kunsan ba sonta nake ba kuma ba zan taba sonta ba. Zamani ya sauya, an wuce zamanin da iyaye zasu tursasa 'ya'yansu auren dole. Kenan na tsoraci goben Afnan? Ita ma zata yi rayuwa irin wacce nake yi yanzu? Tursasa ta zaku yi ta auri wanda bata so?"
“Daina cakuda mana komai, babu irin haka da zata faru. Mu farin cikin ka ne kawai muke so, mu ga rayuwarka tayi kyau.” Cewar Daddy.
“Ni wannan ba farin ciki bane gare ni. Kuna tarwatsa rayuwar da na shiryawa kaina ne, kuma Mom kin fara min abinda bana jin dadin sa."
“Idan da kayi min biyayya duk da hakan bata faru ba. Ba zan taba kokarin sanya ka alakar da zata bata maka rayuwa ba. Nasan wacece Hafsat, yarinya ce ta gari."
“Kin gani ko? Baki saurare na. Har abada ba zan samu farin ciki da wannan yarinyar ba. Mu nemawa kamfanin su mafita idan har wannan shine ke damunki.”
“Kamal me zaka ce game da dan uwanka?” Mommy ta tambaye shi.
“Rayuwar sa ce, ina ga bai dace ki takura masa ba."
“Daman kai baka taba min biyayya ba, ban ma san me yasa na tambaye ka ba. Bansan me na yiwa Allah ya bani 'ya'ya irinku ba. Idan baka amince da auren nan ba, ka nemi wata uwar ba ni ba.”
“Karima kin fara wuce gona da iri." Cewar Daddy.
“Mom kiyi kokarin fahimtar shi.” Cewar Afnan.
Shi kuwa Kamal bai ce komai ba, sai sauraron su da yake.
“Idan ba zai bi umarnina ba, bana son ya cigaba da amsa sunana a matsayin mahaifiyar sa."
“Shikenan.. tinda.. haka take so." Cewar Ammar.
“Bana son shashanci Ammar!” Cewar Daddy. “Kasan me hakan ke nufi? Kasan illar girman abinda take kokarin yi maka?”
Me hakan zai canza? A halin yanzu alakar shi da mahaifiyar sa tayi kasa sosai. Daga yanzu babu abinda zai dawo kamar baya, dan haka ya shirya sallama shi da zata yi.
Kallon Kamal yayi da tun dazu bai ce komai ba, koda suka hada ido Kamal ya girgiza masa kai alamar kar ya yarda yanke wannan mummunan hukunci. Saidai shi Ammar yana ganin aikin gama ya gama.
Maida kallonsa yayi zuwa kan mahaifiyar shi, suka hada ido. Firgici, tsoro, damuwa da bacin rai.. ne tattare a cikin kallon su.
“Tinda a shirye take na cutu a wannan auren da take kokarin yi min.. nima a shirye nake nayi makokin rashin uwa.”
“YA AMMAR !” Afnan ta kwalla kara tare da dora hannu a kai.
“I want to be free, ban taba samun wani 'yanci ba a tare da ita. I want to be free, nayi rayuwata yanda nake so kuma na auri wacce nake so.”
Shuru Mommy tayi.
“Kana tunanin zaka iya samun wani farin ciki ba tare da sa albarkar mahaifiyar ka ba? Ina mai baka shawara da kayi tunani Ammar.” Cewar Mahaifin shi. “Kamal ka yiwa dan uwanka magana. Kar ka barshi ya bata rayuwar sa. Allah baya tare da wanda tsinuwar mahaifiyar sa ke binshi.”
“Ita ta sallama ni ba ni ba. Allah yana tareda da masu gaskiya. Ban yi komai ba ni, kare kaina kawai nayi.”
“Good.. ka fice min daga gida yanzu. Daga yanzu ban sanka ba." Cewar Mahaifiyar sa tareda barin falon.
“Good, daga yanzu ni maraya ne banda uwa.”
“Ya isa haka..” Cewar Kamal.
Mommy ta fice daga falon, Daddy ya rufa mata ba tareda ya sake kallon inda Ammar yake ba.
“Ka wuce gona da iri.” Cewar Kamal.
“Ina ruwana, su basa ganin adadin yanda nake cutuwa? Eh nine mugun cikin labarin.”
“Abinda ka aikata yanzu, ba komai kayi ba illa kara jagule lamarin. Kuma ina baka shawara da ka bata hakuri gobe ko jibi idan komai ya laba.”
“Ba wani hakuri da zan bayar... I just want to stay alone.”
SARAT
Karfe 12 na dare
A gajiye take sakamakon aiki da ta sha gaba daya yinin yau. Tana shirye-shiryen bacci taji wayarta na ringing. Tayi tunanin ko yayanta ne dake kasashen waje, domin shi kadai ke kiranta irin wannan lokacin. Baccin da take ji ne ya kaurace lokacin da tayi arba da sunan oganta a jikin wayar. Da saurinta ta daga kiran.
“Hello?”
“Bacci kike?” Ya tambaye ta.
“A'a, a'a kwance dai nake, kana lafiya?”
“Zo ki bude min kofa..”
Rudewa Sarat tayi, jin Mr. Ammar na bakin kofarta. Zuwa tayi bakin kofar, ta leka ta huda ta tabbatar da shine a tsaye. Har yanzu yana sanye da suit dinsa tun na safe, jacket din a kafadarsa, rabin mabbalan rigarshi kuwa a bude, ya bar kirjinsa waje.
Bata gama kare masa kallo ba, ya rungume ta. Bata sani ba ko farin ciki zata yi ba ko damuwar yanayin da ta ganshi ciki. Sai da suka dau lokaci a haka kafin ya sake ta su shiga ciki. Zaune yayi cikin kitchen yana kallonta tana hada masa coffee. Ganin sa take kamar wanda yayi dambe, bata yi gangancin tambayar sa meke faruwa ba.
“Sorry na zuwa da nayi a wannan lokacin.”
“Kar ka damu... da yake ba komai nake yi ba.” Ta bashi amsa.
Coffee yasha ba tareda ya sake cewa wani abu ba, ita kuwa Sarat kallonsa take yanda yake kai kofin coffee a nutse zuwa bakin sa. Ta kasa dauke idanunta daga kanshi, domin ko a wannan yanayin kyanshi take gani. Kasa tsayar da kanta tayi, taje inda yake tareda rabashi da jacket dinsa. Kissing dinsa tayi shima ya mayar mata da martani. Da son zuwa nesa, a hankali ta cire masa riga, ta shiga sumbatar ko'ina na jikinsa, shi kuwa ya tsayar da ita ta hanyar ture ta.
“Ba wannan bane..ya kawo..ni.. Ina son muyi magana ne.”
Kallon sa tayi ta kara tabbatar da yana cikin damuwa kuma ba kadan ba. Hannun sa ta kama ta jashi zuwa dakinta. Tagogi ta bude sannan ta cire masa takalmi. Kwance tayi bisa gado tareda gayyatarsa shima.
“Zo ka huta, komai zai dawo daidai.”
Sai da ya kalleta na wasu yan dakiku sannan ya gyada mata kai. Kwantawa yayi gefenta tareda dora kansa bisa kirjinta. Rufe su tayi da zani, a hankali ta fara shafa shi dan ya samu nutsuwa. Tana tunanin haka ne yake bukata a halin yanzu.. domin bayan wasu yan mintuna taji numfashinsa ya karu alamar yayi bacci.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story 📖
By Malik al-Ashtar 🖋
For more novels https://bit.ly/3Egdy1m
On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35