Chapter 13
CHAPTER 12
⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚
Kwanaki hudu kenan Zahara ta kasa tashi daga bisa gado. Domin duk jikin ta a mace yake, babu karfi ko kadan. Bata cin abinci ko taci ma ba mai yawa ba. Koda Mama ta tursasa ta taci, mintuna talatin sun yi yawa ta amaye shi. Yanayin da ya tsorata duk dangin ta kenan. Karon farko da Mama da Abba suka samu matsala sosai, kamar Abba zai kai ga jikin Mama. Dalilin yana ganin Mama ce silar shiga halin da Zahara take ciki. Ganin Zahara kwance ba tare da ta iya yin wani abu ba, na kara harzuka Abba. Ita kuwa Mama bata nuna wani tashin hankali, kamar koda yaushe, amma duk da haka Zahara tasan boyewa kawai take. A bangaren Zahara ma tana iya kokarin ta ganin ta tashi ta samu sauki amma ta kasa. Tayi neman tayi neman cikin kwanyar ta ganin ta tuna abinda ya faru a makabarta amma, kawai abinda ta sani ta fita hayyacin ta ne yayin da Malam Shehu ya zuba mata wasu ruwa, kuma ta dawo hayyacin ta a cikin dakin ta bisa gado, da wata laya daure a hannun ta. A lokacin da ta farka ba taso tayi tambayar abinda ya same ta ba, amma bayan wasu kwanaki ta tambayi Mama. Saidai Mama bata yi mata wani karin bayani ba. Dan haka duk a cikin rudu take, gashi babu alamun ta samu sauki.
Kwanaki biyar bayan zuwan su makabarta, Zahara ta fara samun sauki. Lokacin da Mama tazo kawo mata break fast din ta, bata tarar da ita kwance bisa gadon ta kamar kullum ba. A dan kankanin lokaci, taji gabanta ya fadi ta dauka wani abun ne ya sake faruwa, amma ganin Zahara ta fito daga ban daki, tana tafiya lafiya lau kamar komai bai faru ba, yasa Mama ta sauke doguwar ajiyar zuciya tare da jin kamar tayi tsalle dan murna. Ajiye plate din abincin tayi, ta nufi wajen Zahara tana yi mata ya jiki.
“Ya jikin naki? Da kanki kika iya yin wanka? Me ya faru? Na kasa fahimta, jiya fa ko hannu baki iya motsawa.” Cewar Mama cike da farin ciki da mamaki.
Zahara ma farin ciki take ganin Mama ma haka. Saidai ita kanta mamakin warkewar ta take farat daya.
“Bansan me ya faru ba Mama, amma lafiya lau nake jin kaina. Ina jin har zan iya tashi na kewaya gidan nan da gudu.” Zahara ta fada tana murmushi.
Nufar inda wardrobe dinta take tayi, ta dauko wata doguwar riga da zata saka. Mama da har yanzu cikin mamaki take, a zuciyar ta tana tunanin ko layar hannun Zahara ce silar warkewar ta. Daman ta yiwa Zahara kashedin kar ta yarda ta kunce layar daga hannun ta. Ganin yanda Mama ke yi mata kashedi, ya isheta gane cewa layar tana da muhimmanci. Dan haka tayi alkawarin ba zata taba cire ta ba.
“Ki ci abincin ki 'yata. Zan je in kira Abban ki dan sanar da shi. Shi ma hankalin sa a tashe yake dalilin halin da kika shiga.”
“Toh, zan sauko na taya ki aiki idan na gama.”
“A'a.. a'a kar ki ma fara, ya kamata ki kara hutawa.”
“Ki yarda da ni Mama, na warke babu abinda ke damuna. Ba zan iya jure zama a dakin nan ba, ko na minti daya.” Zahara tana fada tana mai nunawa Mama a fuskarta irin yanda ta tsani kwanakin da tayi a ciki a kwance.
“Toh shikenan zaki iya saukowa, amma ba zaki taba komai ba.” Cewar Mama da sigar gargadi.
“Shikenan Mama.”
Murmushi Mama tayi mata kafin ta bar dakin. Zahara taji sauki in dan sauki, amma bata daina tunanin ogan ta da kuma abinda Amriya ta aikata ba. Murmushin ta bacewa yayi lokacin da ta tuna, tana ganin kawai zata rubuta takardar barin aiki domin bata jin zata iya hada ido da Mr. Ammar bayan raba shi da wacce zai aura da tayi. Kunya take ji sosai, duk da ba ita bace asalin wacce tayi laifin.
Yanke shawarar rubuta takardar tayi, gobe sai taje ta kai a office. Daman tsawon kwanaki kenan bata je wajen aikin ba, kuma babu wanda ya kira ta. A ranta tace, wata kila ya samu labarin abinda tayi. Wata kila Kamal ya fada masa komai. Yace kuma kar ta fadawa dan uwan nashi, dan haka bata tunanin shi ya fada masa. Koma dai meye, zuwa gobe zata ajiye aiki. Bata san ko zata kara samun wani aikin da yakai wannan ba, da kuma ogan da yakai Ammar mai saurin fahimta. Koma dai meye kunya ba zata kashe ta.
Zahara rubuta takardar barin aikin tayi a ranar, washe gari taje kamfani kai takardar. Mama bata so ta fita ba, amma tayi mata bayanin kwararan dalilan da zasu sa taje. Wannan karon Zahara tayi shigarta ta mutunci irin wacce take yi a baya.
Koda ta dora kafarta a cikin farfajiyar kamfanin, idanun kowa ya dawo kanta ta yanda har Zahara taji ta tsargu. Sauri ta fara na ganin ta bacewa idanun mutane, sai da tayi hamdalar murna ganin ta karaso bakin kofar ofishin oganta. Konkwasawa tayi da sauri, yayi mata izini da ta shigo. Bayan ta shiga, a hankali ta rufe kofar tana mai tuna abinda ta shirya fada masa. Daga kai tayi..saidai ba shi kadai bane..yana tare da dan uwan sa.
“Ina kwanan ku.” Zahara ta fada da sauri, suka amsa a tare.
“Yaya jikin naki Zahara? I'm so sorry, ayyuka ne suka rike ni shi yasa ban je ganin ki ba. Fatan dai baki yi fushi da ni ba?”
“Nice ya dace na baka hakuri...” Ta fada a sanyaye ba tare ta dago kanta ta kalle shi ba.
“Hakuri? Saboda me? Idan dan rashin zuwan ki ne kwana biyu, kar ki damu baki yi laifi ba. Nasan Salmah tayi miki rauni, kina bukatar hutu.”
Idanun Kamal taji a kanta, domin tana kokarin fadawa Ammar abinda ya faru ne. Amma sai tace bari ta dakata har ya tafi dan ta samu damar magana da oganta. Ba zata iya barin hakan a zuciyar ta ba, dan idan tayi hakan ba zata samu zaman lafiya ba.
“Nazo na kawo maka wannan ne.” Ta fada tana dora takardar a gaban sa.
“Takardar barin aiki kuma?” Ya fada da mamaki. “Me yasa kike son barin aikin ki Zahara? Baki jin dadin wani abu ne? Koh kin samu aikin da yafi wannan ne?”
“A'a...euh.. ba wani aiki na samu ba kuma babu abinda aka yimin."
“Toh me yasa kike son barin aiki? Bro ko zaka bamu wuri muyi magana please?” Cewar Ammar. Saidai Kamal bai bashi amsa ba kuma baida niyyar motsawa.
“Babu damuwa. Tafiya zan yi. Daman na kawo maka takardar ne.”
“Sorry, amma ba zan yi accepting wannan ba. Ba zaki tafi ba haka kawai. Idan saboda abinda Salmah tayi miki ne, ina mai baki hakuri a madadin ta. Kuma insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba.”
“Ba..saboda..hakan ba...ne..na..”
Tana son ta fada masa amma kalaman sun kasa fita daga bakin ta.
“Ba zan karbi wannan takardar ba, kije ki kara tunani ko nan da one month ne kinji? Zamu sake zaunawa muyi maganar a tsanake.”
Gyada kai Zahara tayi.
“Ya jikin naki? akwai abinda yake miki ciwo?” Ya tambaye ta.
“A'a, lafiya lau nake.”
“Toh masha Allah, kenan zaki iya zuwa gobe ko jibi ki cigaba da aikin ki ok?”
Gyada kai tayi, sannan ta tashi da niyyar tafiya. Sai da ta dan kalli inda Kamal yake kafin ta fita... Sai da ta dauki lokaci sosai a bakin kofar tana tunani kafin ta farga ta juya da niyyar hawa lifter taji ana kiran ta. Juyowa tayi taga Kamal Elh. Yusuf ne. Kamar kullum fuskar sa, babu alamun murmushi babu alamun fushi. Da tafiyar sa taku na kasaita. Yana da faffadan kirji, kafadun sa sun dan yi baya da wuyan sa a dan mike. Idan da ancewa Zahara wata rana Kamal zasu yi magana kamar yanda yayi mata toh zata karyata. Yana bata tsoro, kuma ta lura ba ita kadai ba a kamfanin...
“Are you okay?” Ya tambaye ta yayin da ya karaso inda take.
Gyada masa kai kawai tayi a matsayin amsar shi.
“Nayi kokarin kiran ki bisa wayan ki amma bata shiga. Hankali na ya dan tashi kuma ba zan iya zuwa gidan ku ba kai tsaye.”
“Bansan a ina waya ta take ba tun ranar nan.” Cewar Zahara.
“Me yasa zaki bar aiki?” Ya tambaye ta.
Juyawa yayi yana yan dube-dube kafin yace
“Muje inda babu mutane sosai, ina son fada miki wani abu.”
“Na yiwa Mama alkawarin dawowa da wuri.”
“Ba zamu dau lokaci ba. Muje cafeteria.”
Sai da tayi dan nazari na wasu yan mintuna kafin tabi bayan sa. Bayan sun shiga cafeteria yayi kokarin yi musu odar abinci amma Zahara tace ba zata wuce 5 min. Kuma gashi akwai mutane a wajen, dandanan magana zata iya watsuwa cewa an ganta tare da shi alhali babu wani abu tsakanin su.
“Nayi magana da wani malami. Nayi masa magana game da matsalar ki kuma yace zai warkar da ke. Nace masa sai nayi magana da ke. Idan kin yarda, sai ki zabi rana sai muje wajen sa.”
Zahara a ranta tace, da gaske yaje wajen malami saboda ita. Bata san yanada saukin kai har haka ba.
“Naji dadi zuwa da kayi wajen sa saboda ni kuma nagode, amma ina tunanin bani da bukatar sa a halin yanzu. Tuni an korar min ita, Amriya ta tafi.”
“Kamar yaya? Rukiya aka yi miki?”
“A gaskiya, bansan yaya aka yi ba. Abinda kawai na sani tsohon ya kaimu ni da Mama a makabarta. Daga nan na fita hayyaci na, bayan na farfado, na ganni a daki na, wannan layar a hannu na.” Ta fada tana nuna masa layar.
Kallon layar da ake tunanin itace kariyar ta Kamal yayi na wasu yan dakiku.
“Bansan me zan ce miki ba, ko me wannan tsohon yayi miki ba. Amma ki sani duk wani abu da za'a yi idan babu Allah to a banza ne. Ba zan ce baki warke ba, amma wannan shedaniyar zata iya dawowa a kowanne lokaci idan ba tashi tsaye kika yi ba ga yin zikiri, addu'o'in kariya da kuma karatun alkur'ani. Dan haka ina mai baki shawara, duk da haka kizo ayi miki rukiya domin tabbatar da Amriya ta bar jikin ki baki daya.”
“Na fahimce ka, amma nasan Amriya ta tafi. Zan fara karatun alkur'ani da kuma zikirin yau. Amma bana tunanin ina da bukatar rukiya.”
“Ki dai yi tunani. Idan kin yi hakan babu abinda zaki rasa, sai dai ma ki kara samun kariya.”
“Bana bukatar rukiya amma tabbas yau zan fara zikiri insha Allahu. Nagode sosai da taimakon ka.”
“Ok, duk da haka dai ina son jin yanda kike lokaci-lokaci. Yaushe zaki sake wata wayar?” Ya tambaye ta.
“Ban sani ba, amma zan fara neman tawa kafin nayi tunanin siyan wata.”
Bai yi magana ba.. ya fiddo waya daga cikin aljihun sa.. kyakyawa da alamun mai tsada ce sosai. Zahara ko a mafarki, bata taba tunanin rike irin ta ba. Fidda layin sa yayi, sannan ya miko mata. Baki sake Zahara ta kalle shi.
“Karbi, zaki iya amfani da wannan kafin ki samu wata wayar.” Ya fada har yau wayar na hannun sa. Ita kuwa Zahara bata ma yi kuskuren taba ta ba dan ma kar ta bata ta.
“I'm sorry, amma ba zan iya karbar wannan wayar ba. Zan samu wata wayar nan da ba da jimawa ba. Idan ka bani taka, yaya zaka yi kai?”
“Ina da wata a gida, nayi synchronizing all abubuwa na. Kar ki damu da ni.”
“Gaskiya ba zan..”
Katse ta yayi
“Ba kyauta na baki ba, na ara miki just na wani lokaci. Daga baya sai ki dawo min da ita, ban ga wani abu ba a ciki. Saidai idan baki yarda da ni bane.”
“Ok....”
Ta fada, murmushi yayi mata kafin ya kama hannun ta ya dora mata wayar.
“Kafin na tafi, ina son ki sani ba amfanin da zai yi idan kika fadawa Ammar, babu abinda zai canza. Abinda ya faru ya riga da ya faru, idan kika fada masa komai yana iya kasa fahimta. Babu abinda kika aikata bad, I advise you to keep everything for you a yanzu. A halin yanzu rikicin da yake fama dashi kadai ya ishe shi, dan haka abinda zaki fada masa zai zama karin ruruwar wata wutar ne.”
Bata san ya zata iya rayuwa da wannan sirrin ba, amma kuma yanada gaskiya. Ba zata iya rike hakan ba har karshen rayuwar ta, amma zata jira idan komai ya laba sai ta fada masa.
“Ok.” Ta bashi amsa.
“Ok, ni zan tafi yanzu. Zan dinga jin yanda kike lokaci zuwa lokaci.”
“Nagode da abinda kake yi a kaina. It touches me a lot.” Ta fada kanta kasa...
(.....)
A BANGAREN AFNAN ELH. YUSUF
A jiya ma saida tsohon najadun nan ya sake shigo mata daki. Bata san ko zata iya kara yin wata juriyar kamar a baya ba.. Tayi kakorin nuna jarunta da tsora ta shi ta hanyar yi masa barazanar fallasa shi. Amma lokacin da ya shigo taji ta rasa duk wani kuzarin ta, tsoran sa duk ya dabaibaye ta. Tamkar wanda yake zuwa da asiri. Wahalar da take sha kowanne dare tana nunka ta baya. Yayi ta murmushi yana nuna kamar wata 'yarshi a gaban mutane. Har ana cewa uba ne abin koyi amma ita kadai tasan mummunar fuskar da baya so a gani. Idan ya dawo daga tafiya, ya kan siyo mata abubuwa da dama. Ta tsani karbar abun hannun sa, amma tasan Mommy zata iya kallon ta a matsayin butulu. Yana tunanin siyan ta da abubuwan ado masu tsada. Bata san sai yaushe ba, amma wata rana zata fita da wannan kangin azaba.
Mutane da dama suna mata daukar yar gidan, daya daga cikin ahalin, ba kowa yasan yar riko bace, wani lokacin ita kanta Afnan tana mantawa da ba mommy bace ta haife ta. Amma duk lokacin da mijin ta ya kwabe kayan sa gabanta, son kona illahirin gidan da mutanen cikin sa yana dabaibaye mata zuciya.
Kalaman sa marasa dadi da basu daina mata yawo cikin kwalwa “Kin fi wannan jagulalliyar tsohuwar dake wai matsayin matata dadi.” “You are all tight, I like that.”, “kasa controlling kaina nake idan kina kai komo a falo.”, “I hope you like?” “Nasan kema kina so munafuka.”
Wannan kalaman su ke mata yawo a cikin kwalwar ta ba kakkautawa. Kalamai marasa dadin ji masu cike da takaici da kayan haushi. Daga baya ta gane laifin ta ne, domin shi bayan ya gama wulakanta ta, ya kan koma ya cigaba da rayuwar sa. Ita kuwa da dare ta sha kuka har gari ya waye... Ta tsani kanta ta yanda ba'a zato. Komai zai iya zuwa karshe idan da ta tona masa asiri, amma tana tsoron a kasa gasgata ta, tana tsoron mutane su tsane ta su kira ta da butulu bayan duk gatan da mutanen gidan suka nuna mata. Gashi tasan yanada contact lungu da sako na kasar, ta tabbatar ko kwana daya ba zata yi ba zai sa a nemo ta.
Zata cigaba da nema iya nema ganin ta tona masa asiri, ta nunawa duniya asalin fuskar sa.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story 📖
By Malik al-Ashtar 🖋
For more novels https://bit.ly/3Egdy1m
On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35