Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

CHAPTER 31

Amriya Hatsabibiyar Aljana Book 1 Complete Hausa Novel 1,612 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 31 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”

http://www.ashblogg.com.ng/2022/03/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-31.html

Bata taɓa tunanin ganin mutumin da take tunani kwana biyu a ƙofar gidansu ba. Abu na farko da ta so tayi shine ta maida ƙofa ta rufe kamar bata ganshi ba. Saidai a daidai lokacin wani ƙwarin gwiwa ya ziyarce ta.

“Me kazo yi nan?" Zahara ta tambaye shi.

Kamal bai san takamaimai abinda zai yi ba, duk da haka yace
“Ya kike Zahara?"

“Lafiya lau daƙiƙu kaɗan baya nake, excuse me now akwai inda zan je." Ta faɗa kafin ta rufe ƙofar gidansu. Ta gabansa ta bi da niyyar tafiya amma ya riƙo hannunta.

“Zahara, please ki saurare ni, ki bani mintuna biyar dan Allah. Idan ba gaggawa bane ba zan zo nan ba."

“Ba so kake ka tafi ba? Kayi tafiyarta kafin raina ya ɓaci kuma ka yarda ba zaka so gani na rai a ɓace ba."

“Ni da Khadija zamu..."
Katse shi tayi.

“Ni bana son jin komai, ba zan saurare ka ba dan haka kayi tafiyarka kuma kar ka sake dawowa nan ko kuma ka ji maganganun da ba zasu yi maka daɗi ba..."

“Shikenan ba zan yi maganata da Khadija ba, babban abinda ya kawo ni nan shine Amriya." Kamal ya faɗa.

“Meye Amriya?" Zahara ta tambaye shi da mamakin ta inda ya ɓullo.

Dawowa Kamal yayi suna fuskantar juna sannan yace :
“Ina tunanin tana nan...tana ƙoƙarin tarwatsa min rayuwa da kuma ta Khadija. Ba wai ina faɗar haka ba ne domin neman uziri a gare ki amma ina tunanin ita ce silar sa inyi nesa da ke. Ita ce silar rashin lafiyar da nayi ta yi. Ina tsoron ta cutar da ke, da ni da kuma bab...da kuma dangina."

“Bravo... Ka zo ne ka bani wannan labarin kawai dan na yafe maka? Ɓata lokacinka kake, ni ba sakarya ba ce Kamal."

Tafiya Zahara tayi kafin ta waiwayo.

“Da ka samo wani labarin ba wannan ba, tsoho ya riga yayi maganin Amriya kuma wannan layar tana nan koda zata dawo. Yanzu ka koma ka sake ƙirƙiro wani labarin da yafi wannan sannan ka dawo mu gani ko zan yarda da kai." Ta faɗa kafin tayi tafiyarta ta bar Kamal tsaye jiki a sanyaye.

Jiki a sanyaye, yanzu ya fahimci adadin yanda Zahara ke fushi da shi. Abinda yayi mata ba ƙaramin laifi ba ne, daidai idan tayi fushi. Shi ma zai iya shiga wannan yanayin idan Zahara tayi nesa da shi babu wata ƙwaƙwarar sheda.

Ya kamata ya nemo hanyar da zai yi mata bayanin komai cikin kwanciyar hankali kafin ya makara. Ba zai taɓa yafewa kanshi ba idan har Amriya ta cutar da ita.

ƁANGAREN AMMAR

Tun da sassafe ya tashi domin kai Hafsat gida. Ya yiwa ɗan uwansa alƙawarin kula da ita da kyau. Kuma ko babu wannan alƙawarin, ba zai yi komai ba wanda zai cutar da Hafsat. Ya ga halin da take ciki jiya, kuma koda basu jituwa, ya damu da halin da take ciki kuma yana son sanin abinda ya faru da ita.

Bayan ya iso ƙofar gidan Kamal, ya yi knocking ƙofa. Bayan wasu mintuna... yana ta jira amma babu wanda yazo ya buɗe masa. Ƙara nocking yayi, wannan karon sai ga Hafsat ta buɗe masa.

Bai yi mamakin ganin yanda fuskarta duk ta kumbura ba.

“Da sauki jikin naki?" Ya tambaye ta. Ji wata banzar tambaya kuma. Ya faɗa a ransa.

Saidai Hafsat bata bashi amsa ba. Juyawa tayi ta koma cikin ɗaki, kafin ta rufe ƙofa Ammar yace :

“Ni ne zan mayar da ke gida, idan kin shirya ina falo." Ya faɗa mata.

A matsayin amsa, Hafsat ta rufe ƙofar ɗakin da ƙarfi. Ammar yaji kamar sun yi musayar hali. Da fari shi ke yin duk abinda zai yi ganin yayi nesa da yarinyar nan amma yanzu ita ce ke gudunsa. Shi ma ba wani son su zama friend yake ba lokaci guda, saidai yana binta a sannu ne ganin abinda ya faru da ita. Daga ƙarshe sai da ya fara nadamar sakar mata fuska da yayi.

Sai da yayi jiran kusan awa uku kafin Hafsat ta fito daga cikin ɗaki. Sosai ya kai wuya, shi da har aiki ya baro office dan yazo ya taimaka mata, amma duk da hakan ba zai ce komai ba dan kar ransa ya ƙara ɓaci.

“Muje ne?" Ya tambaye ta.

Hafsat bata bashi amsa ba ta nufi ƙofar fita. Rufe gidan Ammar yayi da keys. Ɓude mata ƙofar motar yayi ta shiga ta zauna ba tare da tayi ko tari ba. Ammar bai yi tunanin kasancewa da Hafsat guri ɗaya ban haushi gare shi ba sai yau.

A hankali Ammar ya fara jin sa a takure. Bai san me yasa wannan situation ɗin take sa yake jin sa a takure ba. Kuma abinda Hafsat take yi ba gyara komai yake ba.

Ko kaita wani wurin yake yi ta ci wani abun kafin ya kaita gida? Yanke shawarar kaita restaurant da babu nisa da inda suke ya yi. Wata ƙila bayan taci wani abun ta ɗan saki jiki da shi. Saidai koda ta lura da Ammar ya sauya hanya kuma tashin hankalin yana dab da zuwa restaurant ɗin da ta yiwa farin sani tace

“Me kuma yake ƙoƙarin yi ne?" Hafsat ta faɗa ranta.

Yayi alƙawarin ba zai yi wani scene ba amma wannan guy ɗin ya fara kai mata wuya. Koda yaushe cikin faɗa suke toh me yasa yanzu yake son dole sai yayi kamar su wasu shaƙiƙan abokai ne? Ita ba zata iya munafuncin yin kamar komai bai faru ba tsakaninsu.

Kamar yanda tayi tunani, Ammar ya faka daidai restaurant ɗin.

“Meye haka kake ƙoƙarin yi? Ka yiwa girman Allah ka kaini gidanmu." Ta ƙwalla ƙara tare da jefo masa jaridun da ke gefenta cikin motar.

“Ra'ayi fa kawai nake son canza miki.” Ya faɗa shima da ɗaga murya tare da dukan steering mota.

“Babu abinda nake so daga gare ka, gida kawai nake son zuwa!"

Tunawa yayi da maganar da ɗan uwansa ya faɗa yace
“Kamal.. yayi gaskiya.. ina ɓata komai koda nayi niyyar yin abun ƙwarai. Gwara nayi saurin kaita gidansu kafin ta min hauka anan."

Tayar da motar yayi, fuska a murtuke. Yana nadamar amincewa da kaita gida da yayi. Babu abinda yake tafiya daidai idan suna tare.

“Kana son ka nuna min kai yau mutumin kirki ne, alhali ni da kai mun san ka tsane ni da iya zuciyarka." Hafsat ta faɗa.

Ammar ƙoƙarin share ta yayi, domin yasan idan har ya mayar mata da martani, zai haddasa yaƙin duniya ne na uku. Hafsat ta cigaba
“Ka adana tausayinka, bana buƙata. Zan kasance mafi farin ciki a duniyar da babu kai ! Ni ma na tsane ka amma ni bana pretending. Ka mayar da ni gidanmu babu hayaniya hakan zai sa komai ya je daidai."

Ammar bai kula ta ba ya cigaba da tuki. Bayan kamar mintuna goma kuma sai Hafsat ta cigaba da cewa
“Daga nan kuma sai me? Zaka kai ni gidanmu ne, sannan ka haɗa min abinda zan ci sannan ka cigaba da kula da ni?”

Wani wawan birki Ammar ya taka, da yasa kaɗan ya rage Hafsat ta buga kanta gaban mota ba.

“Are you crazy? So kake ka kashe ni ne ko me?" Cewar Hafsat ta faɗa cikin tsawa.

“Ba abinda kike so ba kenan? Mu kashe junanmu? Bah, gashi kin yi nasara kin tayar da sheɗanin da ke jikina. Sauka !"

.........

“Nace ki sauka !" Ya daka mata tsawa.

Ƙin motsawa Hafsat tayi sai ma kuka da ta fashe da shi.

Dogon numfashi yayi yace “Me kuma na ƙara janyowa kaina?"

“Yanzu faɗa min me yasa kike kuka? Ba so kike na cigaba da nuna ƙetata a kanki kamar yanda nayi yanzu ba.. yanzu kuma da nayi kina kuka? Me yake damunki ne wai ! Kina ta ihun kina son ki sauka yanzu nace ki sauka... Kin ƙi ki sauka. Meye matsalarki?”

“Please ka mayar da ni gidanmu... Ba zan sake magana ba."

“Eh amma ni kuma ina son sanin dalilin wannan sabon sauyin naki?” Ya tambaye ta cikin sanyi wannan karon.

“Bana son yin maganar yanzu.” Ta faɗa bayan ta ɗan nutsu.

“Shikenan kamar yanda kike so." Ya bata amsa kafin ya tayar da motar.

Kamar yanda yace ya kaita har gidansu. Fitowa tayi daga motar ta nufi ƙofar gidansu.

“Hafsat." Ya kira sunanta.

Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba, Ammar yace
“Nasan bai taɓa jituwa ba tsakaninmu amma idan kina buƙatar wani taimako ko kuma kin shirya maganar abinda ya faru da ke zaki iya zuwa ki gan ni. A'a.. kuma ba wai tausayi ba ne... Kawai na gane babu wata fa'ida ne faɗan da babu wani dalili.”

Cigaba da tafiya Hafsat tayi ba tare da ta juyo ba ko tace masa ƙala amma abinda ya faɗa sosai ya shiga kunnenta.

BANGAREN KHADIJA

Bayan kwanaki da ta yi tana tunani, ta yanke shawarar aikata abinda Amriya take so. Tana son tseratar da kanta, soyayyarta da kuma cikin da ke gare ta. Kuma yin abinda Amriya take so shine kaɗai mafita. Ta nemi da ta cire layar da ke hannun Zahara.

Khadija bata yi tambaya ba kuma bata san me hakan zai amfanar da Amriya ba amma duk da haka zata aikata abinda take so. Babu wanda zata cutar idan ta aikata hakan. Khadija ta faɗa a zuciyarta, kawai tana son tseratar da familynta ne. Wa zai ji haushinta idan yaji dalilin da yasa ta aikata hakan?

Dan haka ta shirya zuwa gurin Zahara da wani ƙulli a ranta.

To be continued...

AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story📖

By Malik al-Ashtar 🖋

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
  2. 2 CHAPTER 1
  3. 3 CHAPTER 2
  4. 4 CHAPTER 3
  5. 5 CHAPTER 4
  6. 6 CHAPTER 5
  7. 7 CHAPTER 6
  8. 8 CHAPTER 7
  9. 9 CHAPTER 8
  10. 10 CHAPTER 9
  11. 11 CHAPTER 10
  12. 12 CHAPTER 11
  13. 13 CHAPTER 12
  14. 14 CHAPTER 13
  15. 15 CHAPTER 14
  16. 16 CHAPTER 16
  17. 17 CHAPTER 15
  18. 18 CHAPTER 17
  19. 19 CHAPTER 18
  20. 20 CHAPTER 19
  21. 21 CHAPTER 20
  22. 22 CHAPTER 21
  23. 23 CHAPTER 22
  24. 24 CHAPTER 24
  25. 25 CHAPTER 23
  26. 26 CHAPTER 25
  27. 27 CHAPTER 26
  28. 28 CHAPTER 27
  29. 29 CHAPTER 28
  30. 30 CHAPTER 29
  31. 31 CHAPTER 30
  32. 32 CHAPTER 31
  33. 33 CHAPTER 32
  34. 34 CHAPTER 33
  35. 35 CHAPTER 34
  36. 36 CHAPTER 35
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});