Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

CHAPTER 15

Amriya Hatsabibiyar Aljana Book 1 Complete Hausa Novel 2,460 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚

Zahara bata taba jin nauyi irin na yau ba. Karasowa tayi a sanyaye ta gaishe su da siririyar murya. Tambayoyi ne birjik a cikin kanta wanda ta gagara amsa su...

“Zo ki zauna 'yata, bari na kawo abin sha.”
Tashi Mama tayi ta nufi hanyar kitchen. Da kallo Zahara ta bita kafin ta yanke shawarar zaunawa domin jin me ke tafe dashi. Karasawa tayi a hankali ta zauna kusa da yayan ta da ta jima rabon ta da shi. Koda ta zauna, suka fara magana. Ji tayi suna maganar zane (art), suna fadar wasu abubuwa da bata taba jin su ba a rayuwar ta. A bakin Kamal, ba abin mamaki bane, domin ganin zanukan dake cikin falon sa, ta tabbatar shi mai son zane ne amma bata taba tunanin yayan ta yasan wani abu ba a harkar zane.

Mama ce ta dawo dauke da jus da ruwa, kama mata Zahara tayi wajen zubawa su Kamal. A yanda take a rikice, addu'a take kar ta barar da lemun. Bayan ta zuba musu lemun, Mama tayi shigewar ta daki. Yayan ta kuma baida niyyar tashi ya barta tare da Kamal. Duk da ba wasu makusanta bane sosai ita da yayan nata, amma kowa a gidan yasan yanda yake bata kariya. Bayan wasu mintuna, ya yanke shawarar basu wuri.

Kamal shan lemun sa yake cikin kwanciyar hankali, ita kuwa na ta kokarin ganin ta sarrafa tambayar da take son yi masa. Jira take har ya gama shan lemun, bai kuwa bata lokaci ba ya ajiye kofin.

“Ya kike?” Ya tambaye ta yana kallon ta.

“Lafiya lau...”

Tayi niyyar yi masa tambayoyin amma kamar an toshe mata baki. Sunkuyar da kanta tayi, domin bata iya jure kallon sa... bare kuma da yace yana son auren ta.

“Na sani, da na sanar da ke kafin nazo gidan ku amma kuma bana son ki ki karba ta. Nazo ne kawai na gabatar da kaina gidan ku, domin nuna da gaske nake ba da wasa ba. Abinda kika fada min rannan yasa nayi nazari sosai. Bai dace ki yarda da ni ba, alhali bamu wani san juna ba. Ba zan takura ki ba, domin ki aminta da ni. Nasan kina da tambayoyi da dama, ki sani zaki iya fada min komai. Zan kokarta ganin na amsa duk wasu tambayoyin ki.”

Shuru yayi kafin ya cigaba
“Kuma bana son kiyi tunanin zuwa gidan ku da nayi saboda wata manufa ce ta daban. Idan kina so, ba zan sake zuwa ba, har sai idan ke kika ce nazo.”

Sauraron shi take da kyau kuma ta kasa daina zuzuta kanta kan cewa yayi wannan tattakin ne saboda ita, domin tabbatar mata da gaske yake. Ba zata iya cewa ba ta yarda dashi, amma tasan ba yanda za'a yi ya dinga duk wannan kan abinda baida muhimmanci a wajen sa.

“Me yasa ni? Me yasa sai ni kake son aure?”

“Ba zan iya amsa wannan tambayar taki ba Zahara...”

Tana jin dadin yanda yake kiran sunan ta.. cike da yanga da dadin ji.

“Ba zan iya amsa tambayar ki ba, domin ni kaina bani da amsar ta. Ba zan ce ina miki mahaukacin son nan domin idan na fadi hakan nayi karya, amma kina daukar hankali na sosai. A da ina tunanin hakan a matsayin birgeni kawai kike, amma na gane yafi hakan. Ni ba yaro bane, ba wai dan kina daukar hankali na ba zan yi wata alaka da ke, mu rabu bayan na samu wacce nake so. Addini na yayi min hani da yin hakan. Kina daukar hankali na ne kawai, domin kamar yanda kika ce bamu wani san juna ba. Dan haka zan yi kamar yanda masu cewa soyayya wata aba ce dake ginuwa ta hanyar sanin masoyi, sanin halin sa har ma da kurakuran sa. Dan haka ina son sanin wacece ke kuma idan kema a lokacin kin ga wani abun da yayi miki game da ni. Ki sanar da ni zan zo na nemi auren ki.”

Shuru yayi domin barin ta taji da abinda ya koro mata.

“Of course, idan baki da ra'ayin yin hakan, zan fahimta. Zan ji ba dadi amma zan fahimta, zan yi kokari ganin ban dauki abun da nauyi ba. Ina son kiyi tunani sannan ki fada min abinda kika yanke. Waya ta a kunne take a koda yaushe, zaki iya kira na kowanne lokaci, a lokacin da kika so, zan kasance cikin kaguwar jin amsar ki da sa ran ki amince.” Ya fada da dan guntun murmushi.

A ranta tace, yana tunanin ba abinda zata yi da shi alhali a rikice ne take. Bata san amsar da zata bashi ba, dole ma ta samu nutsuwa tayi tunani.

“Ni zan tafi kafin dare yayi. Kar ki manta, zaki iya kira na a kowane lokaci. Zan zauna zaman jiran amsar ki.” Ya sake tunatar da ita kafin ya mike tsaye.

Mikewa tayi itama da sauri kamar wacce aka sawa remote, tana jiran ya tafi amma ya matso inda take tare da miko mata wani kwali. Hannun sa ta kalla, ta kalli kwalin sannan ta kalle shi.

“Chocolate ce, ban sani ba ko kina son irin wannan abubuwan. Ina son kawai yi miki kyauta ne.”

“Ba zan karba ba..” Ta fada murya cen kasa.

Hannun ta ya kama tare da dora mata kwalin.

“Zaki iya zubarwa, amma ina tabbatar miki chocolate akwai dadi. Ki karba, zan ji dadin haka.”

Karba tayi tare da yi masa godiya. Murmushi yayi sannan yayi hanyar fita daga falon. A daidai lokacin Mama ta fito daga kitchen.

“Ina zaka je? Girki ya kusan kaiwa.”

“Zan dawo wani lokacin Mama, inda nake ne akwai nisa.”

“Toh Allah ya tsare ka gaishe da mutan gidan.”

“Zasu ji Insha Allahu.” Ya fada tare da nufar hanyar fita. Zahara na biye da shi domin rufe kofa idan ya fita. Lokacin da ya fita, sai da ya juyo ya kalle ta tare da yi mata sai da safe.

“Allah ya kaimu and thanks for chocolate.”

Murmushi yayi mata kafin ya shiga mota. Tayar da motar yayi, har sai da yayi nisa sannan ta koma gida.

Da shigar ta gida, Mama ta shiga kallon tana mata murmushi. Kunya ce ta kama ta tace
“A'a Mama, babu abinda zaki ji...”

“Ban taba tunanin my little girl tana da saurayi ba, kuma kyakyawa dashi. Me yasa baki fada min zai zo yau ba? Da na gama girki da wuri.”

“Lahh Mama ba fa saurayi na bane, kuma bansan zai zo ba.” Zahara ta fada tare da hayewa sama da tunanin ko Mama ta bar zancen, amma Mama ta biyo ta har daki.

“Mama...”

“Ba fa zaki ce min kawai aboki ba ne. Naga yanda yake kallon ki kuma ke baki son kallon shi.”

“Ba wanda nake iya kallo cikin ido Mama.”
Tayi kokarin kare kanta amma dariya hakan yaba Mama.

“Ni dai nasan akwai wani abu tsakanin ku. Me ya fada miki kenan?”

“Please.. Mama ki daina. Bana son yin maganar da ke...” Zahara ta fada tana boye kanta bayan pillow.

“Toh ai baki da kawayen da zaki fadawa. Ni gani nan, zan iya baki shawara. Oya, yarinya ina sauraron ki."

Mama tana da gaskiya Zahara bata da wata kawa da zata iya hira da ita. A irin wannan yanayin ne take nadamar yanda take amma bata shirya irin wannan hirar da Mama ba.

“Zan fada miki komai Mama, i promise.”

“Shikenan, ina jira. Zan je in karasa girkin.”

Bayan Mama ta fita, Zahara ta koma ta kwanta bisa gado, ta shiga juye-juye kamar hakan zai taimaka mata wajen gyara hargitsin dake cikin kanta. A confusing take sosai. Yace yana son relation ta gaske, amma ita bata taba yin saurayi ba, tana da raunin experience a wannan fannin, ta yaya zata fara maganar aure? Shida bama ya cikin tsarin ta, aure da yake karshen list na objective din ta.

Kamal yana birge ta, wannan ko tantama bata da amma bata tunanin zata iya kasancewa matar da yake buri...

A BANGAREN KHADIJA

A yau ta karbi albashin ta, ta shirya zuwa gidan Kamal domin yi masa wata kyauta. Odan dinner tayi daga “Eden restaurant” inda ake soya lafiyayyu kaji. Tana sa ran da wannan kazar, yau ta samu kanshi domin tana tunanin kamar gudun ta yake. Ta sani aikin da yake dole ya kasance busy amma a da yana samun damar kiranta dan jin ya take.

Tayi kewar shi sosai, yana wahala rana ta wuce bata yi tunanin sa ba. Idan ta kira shi baya dagawa sai bayan wasu awanni yake sake kiranta, kuma shima dan yace mata yana wani aiki ne ya sake kiranta. Kiran da ba zai yi ba kenan. Bata san dalili ba, amma a da baya mata irin wannan halin. Dole akwai abinda ke faruwa wanda bata sani ba. Dan haka ta yanke shawarar yi masa bazata.

Salmah har yanzu tana gidan ta, bata jin dadin barin ta ita kadai a gida bare ma yanzu da take cikin wannan yanayin, amma kafin ta fito ta tabbatar mata da babu abinda ke damun ta, ita ma ta taimaka mata wajen zaben kayan da zata saka.

“Bakin abu na yi maki kyau.” Cewar Salmah tana mai ja mata zip din riga.

“Thanks my dear. Rigar tana da tsada, tayi min ne ba yanda na iya dole na siya.” Cewar Khadija.

“Zaki yi kwalliya ne?” Salmah ta tambaye ta.

“Eh amma ba da yawa ba, babu lokaci gaba na. Gashi odan da nayi yana hanya. Me zaki yi bayan tafiya ta?”

Sai da Salmah taja dogon numfashi kafin ta bata amsa.
“Da ina tunanin fita, amma ban sani ba.”

“Kizo muje tare gidan Kamal din. Hakan zai dan debe miki kewa.”

“Bana bukatar ganin ko daya daga cikin dangin Ammar kuma bana so na takura ku.”

“Ba fa wajen soyayya zan je ba.”

“Eh amma, zaki iya amfani da wannan damar ki fada masa abinda kike ji game da shi.”

“Bani da wannan kuzarin, yana dauka ta a matsayin best friend din sa ce.”

“Kece kike daukar kanki matsayin best friend. Idan da kin fada masa tun farko da tuni kuna ta shan soyayyar ku.”

“Idan yana sona, da tuni ya fada mini.”

“Ai kin fi kowa sanin shi, kinsan yanda yake da dan shan kai.”

“Banda lokacin da yasan yana san abu.” Khadija ta bata amsa.

“Eh, ai baida budurwa ko kuwa? Mai yiyuwa yana jira ki fara fada ne.”

“Baida budurwa, amma shi ba irin mai jiran nan bane, idan da gaske yana son na zama budurwa sa, da tuni ya sanar da ni. Daina bani fake hope Salmah.”

“Ba zaki samu duk abinda baki gwada neman shi ba, nidai na fada miki.”

“Kafin ki tura ni gun Kamal, ki fara gyara tsakanin ki da Ammar.”

“Daina yimin wannan zancen. Kema kin sani ta kare tsakanin ni da shi. Ba zan so na dawo baya ba. Ke kuwa kar ki yarda ki rasa damar ki.”

_“Tana da gaskiya, babban kuskure ne rasa namiji irin Kamal.”_

Juyawa Khadija tayi da sauri ganin wanda ya rada mata wannan maganar a kunne. Amma babu kowa daga ita sai Salmah.

“Kece kika fadi haka?” Ta tambayi Salmah.

“Na fadi me?”

“Kika ce « babban kuskure ne rasa namiji irin Kamal. »”

“A'a ban fadi haka ba, sai idan mafarki kike dai. Mai yiyuwa kin fadi hakan ne a zuciyar ki.”

A'a.. ita bata fadi hakan ba a zuciyar ta, da kyau taji wata muryar da ta gayi hakan. Ko kuma Salmah tana da gaskiya, mafarkin tsaye ne take.

Daidai lokacin da ta gama kwalliya aka danna kararrawar kofa. Turare ta fesa sannan ta dauki karamar jakarta.

Kazar da tayi oda ce, karba tayi ta biya kudin. Sannan ta nufi bakin hanya, tayi saurin samun dan sahu, ta fada masa inda zai kaita. Ba bata lokaci ya ajiye ta bakin kofar gidan Kamal. Konkwasa kofar tayi, wutar gidan a kunne take hakan ya tabbatar mata da yana nan.

Sautin tafiya taji yana tunkaro kofar. Kamal ne ya bude mata.

“Khadija..” Ya fada da mamaki.

“Ni da kaina.” Ta fada tana murmushi.

“Me kike a nan, daidai wannan lokacin?” Ya tambaye ta.

“Kamar ya me nake yi? Nayi kewar ka ne. Ko bani da 'yancin kawo maka ziyara ne?” Ta tambaye shi.

“A'a, amma ban yi tsamanin ganin ki bane. Ok, shigo.” Ya fada tare da kaucewa dan ta shiga, babu bata lokaci ta shige.

Tasan gidan sosai, dan haka kai tsaye ta wuce falo tayi dare-dare bisa kujera. Komai na falon a tsare yake, kamar yanda ta saba tarar da shi, TV a kunne amma tana tunani yana cikin yin zane ne.

“Na takura ka ko?” Ta tambaye shi lokacin da ya dawo cikin falon, yana sanye da T-shirt da ta fito da kirar shi.

“No, kar ki damu. Ina cikin yin zane ne.”

“Nasan ka tsani a takura maka lokacin da kake zane amma ba zan iya kara kwana daya ba tare da na ganka ba, nayi kewar ka sosai. Ban sani ba ko nice na sa a kaina, amma naga kamar da gaske gudu na kake.”

Da farko dan daure fuska yayi, amma bayan yan sakanni ya saki fuskar. Khadija ta dauka ko wani kwakwaran bayani zai yi mata amma sai yayi mata murmushi kawai kafin ya tambaye me ta kawo. Yayi hakan dan ya janye hirar.

“Soyayyar kaza ta Eden restaurant, nasan kana sonta.”

“Cool, daman ban kai ga cin abinci ba.” Ya fada. “Je ki wanke hannu, bari na dauko plates.”

“Ok, bari na fara ajiye ledar nan.”

Tashi yayi ya nufi kitchen. Itama ta mike ta nufi hanyar bathroom dan ta wanke hannuwan ta. Taje wucewa ta corridor, ta hangi dakin da yake yin zanukan shi a bude. An dau lokaci rabon da ta ga zanukan shi. Shiga tayi ta tarar da ya lullube zanen da yake cikin zanawa, a hankali ta kwaye dan ganin me ya zana domin itama Allah yayi mata jarabar son zane.

Sai da ta dau lokacin kafin ta gane fuskar wacce Kamal ke zanawa. Daidai lokacin Kamal ya shigo dakin da sauri ya koma ya lullube zanen. Ita kuwa Khadija kokarin fahimtar dalilin da yasa Kamal ke zana yarinyar nan, ta yaya suka san juna kume meye alakar shi da ita. Ita da shi sun san juna tsawon shekaru amma bai taba zana ta ba.

Khadija a ranta tace, bayan ruguza soyayyar Ammar da Salmah da tayi, har ta iya samun kuzarin tunkaro Kamal? Kamal din ta?

_“Ya ishe ta haka abinda tayi, ki hana ta kwace abinda yake mallakin ki.”_

Ta sake jin muryar da tayi mata rada dazu, ta fada.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
  2. 2 CHAPTER 1
  3. 3 CHAPTER 2
  4. 4 CHAPTER 3
  5. 5 CHAPTER 4
  6. 6 CHAPTER 5
  7. 7 CHAPTER 6
  8. 8 CHAPTER 7
  9. 9 CHAPTER 8
  10. 10 CHAPTER 9
  11. 11 CHAPTER 10
  12. 12 CHAPTER 11
  13. 13 CHAPTER 12
  14. 14 CHAPTER 13
  15. 15 CHAPTER 14
  16. 16 CHAPTER 16
  17. 17 CHAPTER 15
  18. 18 CHAPTER 17
  19. 19 CHAPTER 18
  20. 20 CHAPTER 19
  21. 21 CHAPTER 20
  22. 22 CHAPTER 21
  23. 23 CHAPTER 22
  24. 24 CHAPTER 24
  25. 25 CHAPTER 23
  26. 26 CHAPTER 25
  27. 27 CHAPTER 26
  28. 28 CHAPTER 27
  29. 29 CHAPTER 28
  30. 30 CHAPTER 29
  31. 31 CHAPTER 30
  32. 32 CHAPTER 31
  33. 33 CHAPTER 32
  34. 34 CHAPTER 33
  35. 35 CHAPTER 34
  36. 36 CHAPTER 35
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});