Chapter 24
CHAPTER 24
⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚
Ammar bai iya tuna ko ta yaya yazo gidansu ba, domin sam hankalinsa baya jikinsa sosai yake cikin shock. Tambayoyi ne a cunkushe cikin kansa. Da saurinsa yake tafe da son yaga ya karasa ƙuryar gidan amma gidan kamar kara tsayi yake. Ko mai gadi bai yi gangancin gaishe shi ba ganin yanayin da yake ciki. Yanada gaskiya domin Ammar baida lokaci da ƙarfin tsayawa amsar wata gaisuwa.
Shiga yayi cikin falon tattare da duk wani ƙunci da yake ji a zuciyarsa. Yana tafiya ne kamar wani saƙago mai aiki da remote, burinsa ya san gaskiya ko nauyin da yake ji a zuciyarsa zai ragu. Har Ammar yana ganin kawai saɓanin fahimta ne kuma zai fanshi kanshi ne yayin da yaji gaskiyar lamarin, domin a cen ƙasan zuciyarsa yasan ba gaskiya bane. Duk da maihaifinsu ba mazauni bane, amma ɗan zaman da yayi da shi ya isheshi yace mahaifinsa yana cikin mutanen kirki da ya sani.
Koma dai meye ya kamata ya ƙara tabbatarwa da kansa.
Hawan sama yayi zuwa hanyar ɗakin mahaifin nasu kamar yanda yasan hanyar tamkar yunwar cikinsa. Wannan ne na farko da jimawa sosai da yaji tsoron tunkarar shiga ɗakin. Wannan yanayin ya tuna masa da shekaru da dama baya, lokacin da idan yayi laifi dole yazo yayi bayani gaban iyayensa. Bambanci a wannan ranar shine za'a yiwa bayani. Kuma wannan karon yaji ina ma ace shine dai yaron nan da zai zo yayi bayanin laifin da ya aikata.
Daga ƙarshe ya iso bakin ƙofar, tafiyar da yaga tayi masa tsayi sosai. Knocking yayi sau biyu sannan ya jira.
Jiran da yayi na wasu sakanni yaji kamar yayi jira na awanni ne kafin mahaifinsa yazo ya buɗe.
“Ah kai ne. Daga asibiti kake?” Cewar Mahaifinsa.
Kallon sa Ammar yayi da alamar tambaya.
“Bakada labari ne? Ɗan uwanka baida lafiya. Mommynka na cen, nima yanzu nake ƙoƙarin tafiya."
Ammar a ransa yake tambaya idan tunani ne mai kyau ya yiwa maihaifinsa zancen yanzu. Wani tunanin ne ya kara zo masa : ba kowane irin zance bane wannan, ana maganar fyaɗe ne, gara suyi maganar yanzu a yita-ta-kare.
Wata tambayar ce ta sake zuwar masa wacce ke da wahalar amsawa : Ta ina zai fara yiwa mahaifinsa wannan zancen?
Alhaji Yusuf ganin yanayin da ɗansa yake ciki, ya fara jin zufa na karyo masa.
“Meke faruwa ne?" Cewar Daddy.
“Ina son muyi magana ne akan Afnan.” Ammar ya faɗa a wahalce.
Tsayuwa ce ta so ta gagari Daddy jin dansa ya ambaci sunan ƴar ƙanwar matarsa. Zuciyarsa ta shiga dukan uku-uku, yayi kokarin ya daidaita nutsuwarsa amma hakan yaci tura hakan yasa ɗansa ya fahimci akwai abinda mahaifin nasa ke ɓoyewa.
“Wani abu ya same ta ne?” Daddy ya tambaya.
“A'a lafiya lau ko kuma in ce ina tunanin lafiya take har lokacin da doctor ya faɗa min wasu abubuwa da na kasa fahimta."
“Ba an hanasu fitar da sirrin patients ba?” Cewar Daddy.
“Sai idan babu wani crime da ya auku.” Ammar ya bashi amsa.
Ta ƙare masa Daddy ya faɗa a ransa. Jiya ya kira, wani ɗan abokinsa wanda yake yi masa duk wani abu da yake so. Ya faɗa masa su shirya yin kidnapping ɗin Afnan su yi nesa da shi. Ya shirya kuɗaɗe masu yawa da zai bata da zata iya wata sabuwar rayuwa nesa da su. Ya cewa ɗan abokin nasa da ya bashi nan da sati ɗaya ya yi tunanin ƙasar da zasu kai Afnan.
«Da na kawar da ita, tun lokacin da na samu dama.» Daddy ya faɗa a zuciyarsa.
“Daddy, dagaske ka yiwa wannan yarinyar fyaɗe?" Ammar ya tambaye shi da tsananin ƙuna a zuciyarsa, yana jin wahalar ambatar sunan fyaɗe da kuma mahaifi a lokaci guda.
Shuru Daddy yayi, amma tashin hankali ne a cen cikinsa. Muryoyi biyu ne ke faɗa cikin kansa. Kuma wacce tafi naci tayi nasara, ba zai taɓa yiyuwa ya amsa wannan laifin ba. Kuma duk yanda aka yi ma babu shaida, maganarsa ce against maganar Afnan. Daddy yana tunanin tasirin da yake da ga Afnan yanada karfi sosai ta yanda zai iya juye laifin kaf a kanta.
Dole ma ya jajurce.
“Maganar me kake yi Ammar? Ta yaya ka iya tunanin daidai da rana daya zan iya aikata irin wannan abun? Afnan kamar ƴata take, na rene ta da duka iya soyayyar duniyar nan. Ta yaya zan iya aikata hakan? Ita ta faɗa maka haka?”
“A'a Doctor ne, kuma nasan..”
“Toh kuma shine zaka zargeni, ba tareda kayi magana da Afnan din ba? Kana son ka tozarta ni ne ba tareda ka samu wata ƙwaƙwarar hujja ba? Me kake nufi ne Ammar?"
“Wani buri Doctor zai cimma idan yayi min karya akan abu mai muhimmanci haka? Zai iya rasa komai idan ta tabbata abinda ya faɗa ba gaskiya bane. Bana tunanin mutum mai ilimi irin Dr. Abdallah zai iya yin hakan."
“Ai wannan ƙazafin zai iya taɓa mutuncina !” Cewar Daddy wannan karon da ɗaga murya. “Zan yi ƙarar wannan likitan.”
“Kafin hakan yayi nisa, zan yi magana da Afnan. Ita ce wacce abun yafi shafa, idan tace hakan ƙarya ne. Toh nan zamu iya shari'a da Dr. Abdallah."
“Yi sauri ka kirata. Amma ka sani ban ji daɗi ba ace ɗana bai yarda da ni ba.”
“Kai ka koya min sanin gaskiya kuma abinda nake ƙoƙarin yi ne yanzu a matsayina na mutum kuma babban yaya. Ko me zai faru ba zaka taɓa sauyawa daga matsayin mahaifina ba.” Cewar Ammar kafin ya fita ya bar mahaifinsa cikin zulumi.
Ammar bai ƙara jiran ko minti daya ba, ya wuce gidansa. Sai da yayi ta knocking sau ba adadi kafin Afnan ta zo ta buɗe masa.
“Zo ina son yin magana da ke.” Yace da ita.
Afnan ba tareda sanin abinda ke faruwa ba, taje ta samu ɗan uwanta.
“Fatan komai lafiya?” Ya tambaye ta dan kar ya rikita ta.
“Lafiya lau. Meke faruwa?" Ta tambaye shi domin hankalinta ya fara tashi. Zaunawa tayi saman kujerar da ke kusa da shi.
Juyowa Ammar yayi yana fuskantar ta a take yaji wani bakin ciki ya hayo masa zuciya. Bai taɓa kawowa a zahiri ko a tunani za'a ce mahaifinsa ya aikata makamancin hakan ba.
“Nayi tunanin idan wani abu ya same ki zaki iya faɗa min?" Ya faɗa ba tareda ya kalle ta ba.
Afnan ta fara tunanin akwai abinda ke faruwa, a take ta fara jin zufa kuma numfashi na kokarin ya gagare ta. A ranta tana tunanin ya aka yi ya sani.
“Eh.” Ta bashi amsa.
“Afnan, ko akwai abinda Daddy yayi miki?”
Daman tasan bai dace ta yarda da Doctor Abdallah ba, domin shi kaɗai ne zai faɗawa Ammar komai. Hajiya Karima da mijinta ba zasu taba yin hakan ba.
“Ki bani amsa Afnan!" Ya faɗa da yar tsawa.
Afnan bata ce komai ba, sai ma ƙasa da ta kurawa idanu. Tana tunanin me yasa ma zata bashi amsa. Tasan babu wanda zai yarda da abinda zata faɗa.
“Kalle ni Afnan."
Ammar ya tashi ya durkusa gabanta tareda dafa kafaɗunta.
“Ki faɗa min gaskiya. Kar kiji tsoron komai. Zan yi iya ƙoƙarina wajen kare ki, nayi miki alkawari. Amma dan na iya taimaka miki sai kin faɗa min komai. Kar ki barni cikin duhu."
Shuru Afnan taki magana.
“KIYI MAGANA AFNAN.” Ya faɗa da ƙarfi tareda girgizata har sai da ta fara kuka.
Ja baya yayi tareda komawa yayi zaune a ƙasa yana bata hakuri, amma Afnan sai ma ƙara sautin kukanta take. Nan ya fahimci lallai akwai abinda ya faru, yanayin da mahaifinsa ya shiga yanzu kuma ita. Babu wata tantama yanzu.
“Tashi muje.” Ya umurce ta bayan shima ya miƙe tsaye.
Kama hannun Afnan yayi ya nufi hanyar fita da ita.
“Yau za'a yita ta ƙare. Idan dagaske Daddy ne mai laifi, ina son ki fallasa shi. Kar kiji komai, ki fallasa shi. Nasan hakan ba sauki gareshi ba amma zan goyi bayanki ko me zai faru.”
“Babu abinda..ya faru..ka rabu da ni dan Allah.” Ta faɗa tana cigaba da kuka.
“Listen.." Ya faɗa yana fuskantar ta. “Ba zaki taɓa samun sukuni ba idan har baki ƙwaci ƴancinki ba ga wannan mutumin. Wata ƙila ki makaro ranar da zaki ji kin shirya fallasa shi. Kin san yadda ƙasar nan take kuma kin san yadda Daddy yake da ƙarfi. Ana dukan ƙarfe ne tun da zafinsa. Wannan jarabawa ce mai ciwo amma kowa zai goyi bayanki. Ba zan taɓa bari ki faɗi ƙasa ba. Kin ji koh?”
Gyaɗa kai Afnan tayi, shi kuwa Ammar ya rungumeta domin ƙara kwantar mata da hankali.
“Kawai ni zaman lafiya nake so.” Afnan ta faɗa kasa da murya.
“Zaki samu bayan zuwan wannan mutumin prison. Rufe shi ba zai maido miki da darajarki ba amma ko ba komai shari'a zata hau kansa. Zaki iya samun wannan kuma takun farko ne zuwa ga waraka.”
Ammar yana magana yana lallashin ƴar uwarsa amma har yanzu ya kasa yarda mahaifinsa ne ya yiwa Afnan fyaɗe. Yasan idan ya nuna rauninsa, Afnan zata ɗaga hankalinta fiye da yanda take a yanzu.”
Yana buƙatar zaunawa shi ɗaya yayi tunani amma kafin nan zai kira family meeting yanzu-yanzu domin sanar da kowa abinda ke faruwa.
Mommy da Khadija ne a ɗakin da aka kwantar da Kamal da ya kasa daina tambayar kansa me yasa Zahara bata zo ba.
Ya yanke shawarar share tunanin da ke ta yi masa yawo a ƙwalwa cewa budurwarsa ita ce silar wannan kai-komo din da yake asibiti.
Abinda yake ji game da Zahara ƙarfi gareshi sosai ta yanda baya fatan wani abu yazo ya raba shi da ita.
“Na ɗauko maka ko ayaba ka ci ne?” Mommy ta tambaye shi.
“A'a..bana jin yuwa." Ya bata amsa.
Khadija kallon inda mahaifiyar Kamal take tayi kafin ta juya tace
“Na kira Zahara amma bata ɗaga ba. Tace min zata dawo amma har yanzu shuru."
Kamal bai ce komai ba, yasan Khadija ba gaskiya ta faɗa ba amma gudun matsala yayi shuru.
“Kamal ina son muyi magana akan yarinyar nan." Cewar Mommy tana kallon ɗan nata ko yanayinsa zai sauya.
Cigaba tayi ganin Kamal bai ɓata rai ba.
“Ina ji a jikina ya kamata ka yi nesa da yarinyar nan...”
Kallon mahaifiyarsa Kamal yayi.
“Kar ki ce zaki rabani da ita ko ma me kike tunani a kanta.” Ya faɗa da sanyin murya.
Wannan maganar tashi ta sa ɗakin yayi shuru. Kallon Khadija Mommy tayi tareda daga kafada irin ai sai da na faɗa miki.
Lokacin da Khadija ta tarar da Mommy ta faɗa mata irin haɗarin da ke tattare da Zahara akan Kamal, Mommy tayi mata bayanin babu abinda zata iya yi. Kamal bai taɓa bari wani ya saka masa baki a cikin al'amuransa ba, kuma hakan tun yarinta yake.
Hajiya Karima ta damu lokacin da Khadija ta faɗa mata amma tasan babu abinda take iya sauyawa. Zata iya yiwa yarinyar da ake cewa Zahara magana, amma Kamal ba zai taɓa yin abinda zata sanya shi ba. Haka abun yake tun asali. Ta gargaɗi Khadija akan hakan amma sai da ta yiwa Kamal maganar.
“Ya kamata ka saurari mahaifiyarka.” Cewar Khadija cikin jin haushi.
“Babu ruwanki.” Cewar Kamal.
“Na gaji, ku barni na yi bacci." Ya sake faɗa.
Tashi Mommy tayi ta bar ɗakin.
“Gaskiya baka kyautawa abinda kake yiwa mahaifiyarka.” Cewar Khadija.
“Khadija... Nasan ke kika je kika faɗa mata wasu abubuwa game da Zahara. Wannan ne gargaɗina na ƙarshe da zan yi miki, a karo na gaba zan datse alakar da ke tsakaninmu. Ki shafawa Zahara lafiya. Ina son Zahara, dan haka ke ko wani ba zai canza hakan ba.”
“Ni zaka kora daga cikin rayuwarka akan wannan yarinyar?”
“Idan kina son ki cigaba da zama a matsayin friend dina, ki daina muzgunawa Zahara! Wannan ne na ƙarshe da zan faɗa miki hakan. Kuma wannan yarinyar da kike cewa ita zan aura dan haka ina son kiyi respecting ɗinta.” Ya faɗa babu alamar wasa yana kallonta cikin idanu.
“Kawai ina son..."
“Ni ina son ki fahimci wannan ne.” Ya katse ta.
Khadija taji kamar ta kama da wuta. Bata ce komai ba amma a cikin zuciyarta, tasan ba zata iya kallon mutanen nan biyu suyi aure ba. Amriya tayi mata alkawarin zata raba su kuma aiki ya fara kyau domin a yanzu Zahara bata iya shan inuwa daya da masoyinta Kamal.
“Kuma ai basu ga komai ba." Khadija ta faɗa a zuciyarta.
To be continued...
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story 📖
By Malik al-Ashtar 🖋
For more novels https://bit.ly/3Egdy1m
On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35