Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

CHAPTER 32

Amriya Hatsabibiyar Aljana Book 1 Complete Hausa Novel 1,628 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 32 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”

http://www.ashblogg.com.ng/2022/03/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-32.html

Zahara bata daina yin kuskure ga files ɗin da zata kai ba. Yanayin oganta ba top ba ga kuma kurakuran Zahara da ke ƙara ɓata masa rai. Haɗuwarta da Kamal ta takura ta yanda ta dena baccin dare.

Tunanin jin Amriya ta dawo ya tsorata ta. Bata sani ba ko ta yarda da maganar Kamal ko a'a. Ko ma dai meye yana iya ɓacewa na tsawon kwanaki daga baya ya dawo ya yi mata ƙarya. Me yasa ma ba zai yi mata ƙarya ba dan ta dawo gare shi? Tambayoyi da dama ke mata kai-kawo cikin kai.

Saidai ba su kaɗai ba ne wanda hankalinsu baya jikinsu. Sarat, ita ma ba daidai take ba kwana biyu. Tana jin kamar ta rasa komai. Tana jinta a ƙazanta, wacce aka yi amfani da ita aka jefar. Bata san me zata yi ba dan dawo da mutumin da take so. Komai zulle mata yake.

“Ya isa haka Zahara... Idan kin yi kuskure na farko zan iya karɓa amma nan baki aje hankalinki ba. Idan bakida ra'ayin aiki yau sai ki faɗa min.” Cewar Ammar cikin tsawa gaban ofishin Zahara rai a ɓace.

Batada wani zaɓi da ya wuce ta bashi haƙuri, miƙewa tayi tare da ba ogan nata haƙuri.

“Ka yi haƙuri, zan mayar da hankali daga yanzu.”

“Abinda ya kamata ki yi kenan, matsalolin da ke gare ni sun isa haka.” Ya faɗa kafin ya koma cikin ofishinsa ba tare da ya manta da rufo ƙofar da ƙarfi ba domin nuna rashin jin daɗinsa.

Sarat da gaban idonta aka yi komai, ta yanke shawarar ajiye girman kanta ta nufi ofishin nasa ganin meke faruwa. Ta gaji da zama cikin duhu.

Ta gaban Zahara ta bi da ke ta faman zubar da hawaye amma Sarat bata bi ta kanta ba. Ta kunna kai cikin ofishin Ammar ba tare da tayi knocking ko ta rufe ƙofar a hankali bayan ta shiga ba.

“Na gaji da ajiye ni gefe da kake yi, ba zaka dinga amfani da ni kana yar wa ba duk lokacin da ta raya maka !"

“Saurare ni Sarat, yanzu ba lokacin irin wannan...”

“Ba ruwana ko lokacin ne ko ba lokacin ba ne. Tsawon makonni kenan ban ce komai ba toh ya isa haka. Idan baka son aurena ne ka faɗa min ba wai ka bar ni cikin duhu ba. Na gaji da zaunawa jiran gawon shanu kamar wata sakarya.”

“Domin Allah Sarat, bana son yin aure da ke. Bana son ɓata miki ne shi yasa ban...”

“Ya isa haka, bana son wani tausayi ko wani abu daga gare ka. Amma ka sa wannan a ranka kowa ya ci zomo, ya ci gudu. Ka yi wasa da ni, kuma ina fata zaka cutu kamar yanda nake cutuwa a yanzu.” Sarat ta faɗa tana iya ƙoƙarinta ganin ta rike hawayen da ke son zubo mata.

Miƙewa tsaye Ammar ya yi yana ƙoƙarin zuwa kusa da ita amma ta ja baya. Jiki na mata rawa, ta fice daga ofishin. Koda ta saka ƙafa waje hawaye suka fara zubo mata, da gudu ta shige toilet.

Ammar bai kai ga samun lokaci na tunanin abinda ya faru yanzun ba, wayarshi ta yi ringing na kiran da tun ɗazu yake jira. Ɗaga kiran ya yi ba ɓata lokaci. Wanda ya kira shi yana ƙoƙarin gaishe shi Ammar yace
“Please Farouk mu ajiye gaishe-gaishen nan. Faɗa min komai ko hankalina zai kwanta.”

“Ok." Cewar wanda ya kira da Farouk. “Na samu bayanai da yawa cikin ƙanƙanin lokacin nan. Sai da ma nayi hacking duka wayoyinta. Na ɓata duka daren jiya ina karanta chatting ɗinta. Fatan dai ba zata ji haushina ba?”

“Ina jinka Faruk, ka faɗa min abinda nake son ji kawai.” Ammar ya faɗa tare da zaunawa dan kar ya faɗi.

“Ina tunanin abu ne da zamu iya saurin shawo kansa. Ta haɗu da wani saurayi ne a cikin gari... Suna magana amma kuma suna exchanging nude pics sosai. Saidai saurayin ya fara yi mata barazana lokacin da ya gano ƴar gidan mai Shakur Company ce. Da fari tana yin abinda suka ce, saidai a hankali ta fara yi musu tawaye, hakan kuwa ya sa abun ya juya kanta. Saurayin ya fara bibiyarta har zuwa ranar da ta zo gidan yayanka mutanen sun doke ta kuma sun mata barazanar zasu dawo idan ta faɗawa wani. Yanzu haka suna son ta same su a hotel ran asabar.”

“What? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Ammar ya faɗa cikin tashin hankali.

“Bana tunanin babu abinda mutanen nan zasu yi mata. Amma inada sunan saurayin da kuma adress ɗinsa. Zamu iya cafke shi da mutanensa.”

“Nagode sosai da wannan aikin naka Farouk. Ka turo min duk wani abu da ka samu, zan turo maka ladan aikinka zuwa gobe. Ni zan ji da sauran.”

“Game da mahaifinka kuwa, zan yi maka bayani zuwa gaba idan mun haɗu. Har yanzu ina kan abinda muka tattauna a baya.”

“Ok, nagode Farouk. Na yarda da kai. Sai mun haɗun."

Ya kasa yarda har yanzu ana yin irin wannan abun. Bai taɓa tunanin Hafsat zata aikata hakan ba. Ta iya turawa wani hotunan tsiraicinta har ya yi mata barazana da su. Dole shine zai gyara komai tun da har ya saka kansa tsundum a ciki.

Hafsat zata ƙara tsanar sa idan ta san ya shiga rayuwarta amma idan hakan shi zai yi ya ceto ta, a shirye yake ya sake maimaitawa.

ƁANGAREN KHADIJA

Gaban madubi take tana shiryawa rai a jagule. Da ƙyar take iya jiyo me aminiyarta take cewa. Tana tunanin yanda zata yi ta cire layar hannun Zahara. Bata san meye amfanin wannan layar ko abinda yasa Amriya take son ta cire ta ba. Abinda kawai ta sani, shi ne ba zata so ta shiga tsama da wannan aljanar ba.

“Idan na matsa miki, faɗa min ya kamata ki yi Khadija.”

Juyowa ta yi ta kalli Salmah.

“A'a wallahi..ina sauraron ki.. kawai na ɗan yi nisa cikin tunani ne.”

“Ina faɗa miki, Mansoor ya nemi da na yi tunani akan tayin da ya yi min. Yace min yana son mu tsayar da magana kafin ya koma USA. Ni yana burge ni, kuma na san idan muka yi aure zan kamu da son shi, guy ɗin ne ya haɗu sosai. Amma ina tunanin anya zan iya jiran sa har na shekara ɗaya... Yace min zai yi iya ƙoƙarinsa ganin na je cen nima. Amma bana tunanin son ƙara barin garin nan.”

Miƙewa Khadija ta yi wannan karon !

“I'm sorry Salmah.. amma inada abubuwa da dama cikin kaina... Ban san me zan yi ba. Yanzun ma fita nake son yi amma zan dawo ba da jimawa ba, na yi miki alƙawari."

“Ina zaki je? Me yasa baki faɗamin komai ba? Lafiya babyn yake? Kina saka ni cikin damuwa Khadija." Cewar Salmah tana saukowa daga bisa gado.

“Kar ki damu, zan ji da komai. Na yi alƙawarin da komai ya tafi daidai zan baki labarin komai.” Khadija ta faɗawa ƙawar tata ba tare da ta yi mata wani ƙarin bayani ba.

Fita ta yi ta bar Salmah zaune cikin damuwa da ruɗu.

ƁANGAREN ZAHARA

Zahara ce ta fito daga office. Yinin yau sam bai mata daɗi ba, sai ma da ta ga Khadija tsaye bakin motarta tana jiranta. Ta yanke yin kamar bata ganta ba saidai tuni ta makaro domin Khadija ce ta ƙaraso inda take da sauri.

“Cen saurayinki... yanzu kuma ke...gaba kuma waye zai zo?”

Khadija jin saurayinta yazo gurin yarinyar nan, ta ji kalaman tamkar sukar wuƙa. Sai da ta jajurce kafin ta iya controling fushinta gaban Zahara. Ta zo ne aiwatar da wani aiki, dan haka ba zata so yin abinda zai kawo mata cikas ba.

“Ban zo nan dan faɗa ba, na zo ne mu yi magana."

“Babu maganar da zamu yi, yanzu na fito daga aiki kamar yanda kike gani, a gajiye nake dan haka ki min afuwa, bana da lokacin yin magana yanzu.” Zahara ta faɗa kafin ta gifta ta gaban Khadija da niyyar wucewa. Saidai Khadija ta fizgo hannunta da sauri.

“Please ki bani mintuna goma, ba daɗi ba ragi.”

Numfashi Zahara ta ja na wasu ƴan daƙiƙu kafin duk da haka ta yanke tafiya. Ba zai yiwu ta tsaya saurarar wannan matar ta faɗa abinda ita kaɗai ta sani ba.

“Wata ƙila ki yi nadamar tafiya ba tare da kin ji me zan faɗamiki ba."

Tsayawa Zahara ta yi, ta juyo a fusace.

“Barazana kike min yanzu? Ki saurare ni da kyau, ba zan bari a taka ni ba, ko ki tafi kowa ya je gida lafiya, ko ki tsaya ki ga ɓacin rai iya ɓacin rai.” Zahara ta faɗa da yanayin da ita ma bata san shi da ita ba.

“Me kike yi nan Khadija?”

Suka ji wata murya ta faɗa a bayansu. Dukansu sun san me wannan muryar ba kowa ba ne face Ammar.

Ja baya Khadija ta yi tare da kallonsa ta yi murmushi wanda da ka gani ka san ƙirƙirar sa ta yi.

“Na zo ne na ga Zahara..”

“Ko na kira Kamal ne?” Ammar ya tambaye ta.

“A'a... Tafiya ma zan yi yanzu. Zamu haɗu an jima.” Khadija ta faɗa tare da juyawa.

Komai ya tafi da sauri da ya sa Zahara bata san Khadija ta fizge layar hannunta ba.

Ammar tambayar Zahara ya yi da kallo. Ya san duka me yake faruwa amma baya son saka baki ne.

“Ko na zo na ajiye ki gida ne?” Ammar ya ce wa Zahara.

“A'a.” Ta bashi amsa tare da nufar bakin titi inda zata tari mai adaidaita.

To be continued...

AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story📖

By Malik al-Ashtar ??

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
  2. 2 CHAPTER 1
  3. 3 CHAPTER 2
  4. 4 CHAPTER 3
  5. 5 CHAPTER 4
  6. 6 CHAPTER 5
  7. 7 CHAPTER 6
  8. 8 CHAPTER 7
  9. 9 CHAPTER 8
  10. 10 CHAPTER 9
  11. 11 CHAPTER 10
  12. 12 CHAPTER 11
  13. 13 CHAPTER 12
  14. 14 CHAPTER 13
  15. 15 CHAPTER 14
  16. 16 CHAPTER 16
  17. 17 CHAPTER 15
  18. 18 CHAPTER 17
  19. 19 CHAPTER 18
  20. 20 CHAPTER 19
  21. 21 CHAPTER 20
  22. 22 CHAPTER 21
  23. 23 CHAPTER 22
  24. 24 CHAPTER 24
  25. 25 CHAPTER 23
  26. 26 CHAPTER 25
  27. 27 CHAPTER 26
  28. 28 CHAPTER 27
  29. 29 CHAPTER 28
  30. 30 CHAPTER 29
  31. 31 CHAPTER 30
  32. 32 CHAPTER 31
  33. 33 CHAPTER 32
  34. 34 CHAPTER 33
  35. 35 CHAPTER 34
  36. 36 CHAPTER 35
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});