Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

CHAPTER 7

Amriya Hatsabibiyar Aljana Book 1 Complete Hausa Novel 2,410 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

⚖HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSOCIATION📚

Hajiya Karima matar Yusuf cike da samun nutsuwa. Daman ko ba dade ko ba jima tanada kudirin raba alakar tsakanin danta da wacce yake ikirarin yana so amma abinda yarinyar nan ta fada mata yanzu, bata bukatar hade sama da kasa ganin ta kawo karshen wannan soyayyar. A ranta tace wata kila dan nata bai san da wannan ba, da bai nemi ya aure ta ba. Wani namiji ne zai so auren "Yar gantali"? Kuma koda ma ya amince da wannan alakar, Hajiya Karima ba zata taba yarda ba, haka ma mahaifin sa Alhaji Yusuf.
Kowacce uwa zata so abun kwarai ga danta kuma tasan yar aminiyar ta ita ce wacce ta dace da Ammar. Duk da dan rawan kanta amma yarinya ce da ta samu tarbiya mai kyau daga mahaifiyar ta kuma tasan ba zata taba bada kanta ga namiji ba kafin aure.

“Zan samu baccin kirki ne kadai idan Ammar ya aure ta.” Ta fada a zuciyar ta.
Saukowa tayi daga kan stairs ta shiga neman Salmah. Bata ko bi ta kan bakin da ke kokarin gaishe ta ba. A cewar ta tanada abinda yafi wannan. Iya saurin raba danta da wannan yarinyar iya saurin samun sukunin ta.
Kusan ko'ina na wajen taron ta duba amma bata ga alamar Salmah ba. Ganin mahaifiyar shi daga nesa da alamun tana neman wani, Ammar Yusuf ya nufo inda take.
“Mama, koh Kamal kike nema? Ina tunanin har yanzu yana sama. Ya kai Fatima dan ta huta. Yanzu ma nake cewa naje na ganta.” Cewar Ammar ga mahaifiyar tashi da bata daina waige-waigen neman Salmah ba.

“Ina budurwar ka?” Mahaifiyar tashi ta tambaye shi, shi kuwa a take zuciyar sa ta wani buga.
Me yasa take neman Salmah? Ya tambayi kanshi, ganin yanda ran mahaifiyar tashi yake kamar a bace, ba idea bace mai kyau ya barta taga Salmah.
“Mama kin mini alkawarin fah ba zaki yi komai ba, a wajen walimar nan.” Dan nata yayi mata tuni cikin sigar lallaba.
“Rabu da ni..! Ka fada mini kawai idan ka ganta.”
“Nasan abinda tayi bata kyauta ba, amma nayi miki alkawarin zata baiwa Zahara hakuri, idan ta dawo hayyacin ta. Na rantse miki tayi nadama.”
“Ba zaka fada min inda yarinyar nan take bane?” Ta fada da dan daga murya wanda hakan yayi silar janyo hankalin wasu daga cikin bakin.

Ganin haka yasa Ammar ya yiwa Mahaifiyar sa jagora inda Salmah take ba dan yaso ba. Lokacin da Hajiya Karima taga Salmah kwance kan gadon danta kamar wata matar shi, dandanan yanayin fuskarta ya sauya kamar wacce aljanu suka shafa.
Salmah koda jin kofa ta bude da karfi, tayi sauri ta mike daga kan gadon. Tsoro ya dabaibaye ta ganin mahaifiyar saurayin ta. Jikin ta ya shiga rawa, ta kasa yin tsayuwa kuma ta kasa komawa ta kwanta.
Juyawa tayi ta kalli saurayin nata ko Allah yasa akwai wani taimako da zai yi mata, saidai shima duk a rude yake. Ya kasa fahimtar dalilin da yasa mahaifiyar sa ke ta duk wannan alhali tayi masa alkawarin ba zata yi wani abu ba wajen walimar shi. Addu'a yake tayi a ransa, kar ta yiwa Salmah wani abun. Sai dai ya makaro.

“Eh ai dole ki zo kiyi rashe-rashe kan gado, tinda a gidan ku kike ko a dakin mijin ki...!” Cewar Hajiya Karima rai a bace.
A rikice, Ammar ya kama hannun mahaifiyar sa, ya dan jata gefe dan suyi magana a nutse amma Hajiya Karima ta fizge hannun ta ta dumfaro inda Salmah take, da tuni ita ta fahimci lallai wannan matar ba son auren su take ba. Tuni taji kunci ya mamaye ta, a ranta tace me tayi da ta cancanci irin wannan tsana ga mahaifiyar Ammar. Tasan idan har bata amince da auren su ba, toh ba zasu taba samun kwanciyar hankali ba bayan sun yi auren.
Zuciya na mata zugi, jikin ta na rawa ta duka ta kwashi takalmin ta da nufin barin gidan baki daya.

Saidai ba wannan bane Hajiya Karima take so, bata gama magana ba.

“Ina zaki je? Ban gama magana ba da ke. Yau za'a yita ta kare. Ina son idan kika bar gidan nan, ki sa a kanki ba zan taba amincewa ba dana ya aure ki. Ta yaya kike tunanin zan amince da ke a matsayin matar dana bayan kin gama yawo a hotels din garin nan. Daina kallo na da wannan idanun naki, gaskiya ce na fada. Kin dauka ba wanda zai san da wannan danyen aikin? Duniyar nan karama ce yarinya, kar ki yi abu da tunanin wai wani ba zai sani ba.”

“Mama, dan Allah.. ki daina...”

Ammar a sanyaye yake kokarin dakatar da mahaifiyar sa, saidai ita sai da ta tabbatar da ta juye duk abinda ke ranta.

“Daina taba ni Ammar, ko kasan da yarinyar nan karuwa ce? Na tabbatar baka sani ba, dan ba zaka taba yarda ka aure ta ba. Yau na bude maka idanu ka gani ko ita wacece a zahiri. Ina son ka kawo karshen alakar ka da ita yanzu-yanzu.”

Salmah... ji tayi tamkar an daba mata wuka a kirji.
“Ammar...” Ta kira sunan sa cikin dusashiyar murya. “Ammar...ya..zaka..min..haka..?” Ta tambaye shi a sanyaye.

“Na rantse miki da Allah ba ni na fada mata ba, ki yarda da ni.”

“Ba gaskiya bane, kai kadai ne wanda na fadawa. Idan baka son aure na ne, da ka fada min tun farko ba sai daga baya kazo kaci mutunci na ba cikin dangin ka. Nasan nayi kura-kurai amma ban cancanci wannan ba.” Ta fada masa a sanyaye kafin ta bar dakin, tana kuka.

“Kenan kana sane ma? Kake son ka aure ta alhali kasan ballagaza ce? So kayi ka jawo min abun kunya koh, toh ka sani Allah baya bacci.” Ta fadawa danta dake kokarin bin bayan masoyiyar sa.

Yasan irin yadda Salmah ke shiga matsanancin kunci idan aka tuna mata da wannan bangaren mai bakin duhu na rayuwar ta. Dole taji ba dadi har ma ta tsane shi. Amma Allah ne kadai shedar shi kan sanin ba shi ya fadawa mahaifiyar shi ba. Haka bai san ya aka yi ta san da wannan labarin ba. Bai taba yiwa wani wannan zancen ba. A ranshi yace zai ji da wannan daga baya, yanzun ya kamata ya nemi inda Salmah take.

A bangaren Salmah, tafiya take a titi ba takalmi a kafar ta, ba tare da tasan inda zata je ba. Tayi da nasanin fadawa Ammar wannan zancen. Ta yarda da shi ne sosai kuma tayi tunanin ba zai taba fadawa kowa ba, amma jin maganar yanzu a bakin mahaifiyar sa ya karyar mata da zuciya. Bata taba tunanin irin wannan ranar zata riske ta ba. Amma ba wanda zata zarga sai kanta. Laifin ta ne idan an alakanta ta da hakan. Tasan dole wata rana rayuwar da tayi a baya zata yi mata dirar mikiya a sabuwar rayuwar ta amma ba zata zata yi mata ciwo ba har haka.

(...)

Lokacin da Kamal Yusuf ya fito daga cikin dakin da Zahara take, library ya nufa. Tunanin yarinyar nan ne Zahara ke ta yi masa yawo a kwanya, shi kuwa nata kokarin ganin ya yakice shi amma ya kasa. Ya saba da nuna ko in kula a harin da mata ke kawo masa, amma wannan karon, ya kusan fita hayyacin sa. Wannan yarinyar da bata ko kai sa'an kanin shi ba, tana kokarin dagula masa lissafi.

Abun ya zo masa a bazata kuma a baibai, rufe idanun sa yayi da nufin korar duk wani tunani amma muryoyin dake tashi ta window dakin dake kusa da library yasa ya kasa samun nutsuwa. Dakin da mahaifiyar shi da Zahara suke ciki ne kuma window a bude take. Mikewa yayi da niyyar barin wurin amma kukan da Zahara take ya tsayar da shi. Matsowa yayi dan ganin meke faruwa, tsaye yayi cike da mamakin jin abinda Zahara ke fadawa mahaifiyar su. Yayi matukar mamakin jin maganganun ta yanda ya kasa sanin abun yi. Yace koma me yarinyar nan ta sani game da Salmah bai dace ta fadawa Mahaifiyar su ba, balle kuma dama mahaifiyar tasu makama take nema na raba masoyan.

Ba karamin haushi Zahara ta bashi ba, kuma ya yanke shawarar seta mata zama. Ya tsani shiga harkokin wasu amma wannan karon ya shafi dan uwan shi. Ya kamata yayi wani abun. Fitowa yayi daga library ya nufi dakin da Zahara take, amma tuni mahaifiyar su ta fita neman Salmah. Tarar da Zahara yayi, tayi kwance rairan bisa gado kamar ba abinda ya faru. Haushi ne ya kara turnike shi.

“Ko kin san abinda kika aikata yanzun?” Ya tambaye ta.

Zahara ta juya ta kalli kofa, sannan ta tashi zaune a hankali tace:

“Oh..kai ne... Ka dawo..? Yauwa daman bamu karasa maganar mu ba a dazun, amma idan kana so.. zaka iya rufe kofa, dan muyi maganar da kyau.”

“Ba wannan bane ya kawo ni, me yasa kika fadawa mahaifiyar mu duk wannan?” Ya tambaye ta fuska a murtuke.

Saukowa Zahara tayi daga kan gadon a hankali ta matso inda yake. Duk da fuskar shi ba annuri, dambe yake ta yi da shedanun cikin kansa dan kar ya kalli surar jikin ta da duk ta bayyana cikin doguwar rigar ta. Sai dai lokacin da Zahara ta matso dab da Kamal Yusuf, taji duk jikin ta ya saki. Dafe kanta tayi kafin ta zube kasa.

Kamal a tunanin sa duk cikin sharrin su ne na mata yayi tsaye yana kallon ta, amma ganin sai murkususu take, hankalin sa ya tashi.

“Ka..taimake..ni..dan Allah..” Zahara take fada tana kokarin tashi.

Da sauri Kamal ya karaso inda take.

“Lafiyar ki kuwa?”

“Dan..Allah..ka taimake ni..kaina..”
Idanun ta rufe amma bata daina fadin wannan kalmar ba. Kamal durkusawa yayi ya shiga kokarin tashe ta. A hankali ta bude ido ta rufe kafin ta sake budewa da sauri tana bin dakin da kallo.

“A ina nake? Ta fada kafin ta ja jikin ta da karfi ganin namiji kusa da ita.

Sunkuyar da kai tayi, ta ga rigar da ke jikin ta. A take miyagun tunani suka ziyarci kwakwalwar ta. Ko dai kidnapping dinta aka yi? Ko kuma fyade aka mata? Tunanin da take kenan. Sai dai taji hankalin ta ya dan kwanta jin babu wani ciwo tsakanin kafafuwan ta. Kanta yayi dub, ta kasa tuna komai. Abinda kawai take iya tunawa shine, tana kokarin shiryawa zuwa wajen walima daga nan shuru.

“Are you ok?” Kamal ya tambaye ta.

Ita da har ma ta manta da shi a wurin, Zahara ta dawo hayyacin ta, nan ta gane mutumin da ke kusan ta ba kowa bane face dan uwan ogan ta. Hankalin ta taji ya dan kwanta, amma wani sabon tsoron ya sake shigan ta.

“Me nake yi a nan?” Ta tambaya tana kokarin mikewa tsaye amma jin kanta ya sara mata ta koma ta zauna.

Kamal a bangaren sa bai san me zai yi ba ganin wannan drama ta Zahara. Wani lokacin ta dawo tamkar bomb dake shirye ta watse kan kowa, wani lokacin kuma ta dawo mai sanyin hali da tsoron mutane. Yanke shawarar bin wani bangare na zuciyar shi dake son taimakawa yarinyar yayi.

Kamal zira hannayen sa yayi daidai kugunta da nufin taimaka mata ta tashi amma Zahara ta saki kara tare da cewa kar ya taba ta.

“Dan Allah.. bana so.. kar ka taba ni dan Allah..”

Wata kila ta dan ji sanyi na ganin dan uwan Mr. Ammar ne a dakin, amma har yanzu bata san me take yi a nan ba. Cikin wannan shigar.

Zahara ta kasa tuna ko kadan abinda ya faru a marecen ranar nan. Abinda kawai zata iya yi shine ta tambayi wannan mutumin duk da tasan aikin Amriya ne. Ta san ita ce ta shiga jikin ta, amma a baya koda ta shiga jikin ta idan ta dawo hayyacin ta, kusan tana iya tuna komai amma wannan karon shuru ne. Kamar wacce aka debi wani bangaren na kwakwalwarta.

“Malam dan Allah ka fada min abinda ya faru..”

Shine karon farko gare ta, da ta tsaya kusa da shi amma ba karamin haushi take ji ba da yake kallon ta a cikin wannan shigar. Bata san me tayi ba da ta kare nan kusa da shi. Tana bukatar amsoshi kafin tabin hankali ya kama ta. Tana son sanin abinda Amriya tayi.

“Kinga ina ganin kina bukatar hutu.” Ya fada yana sake kokarin taimaka mata ta tashi amma ta sake ture shi.

“Ina son sanin me ya faru please...”

“Then.. tinda kin matsa. Ban san me ya faru tsakanin ki da Salmah ba amma ta ture ki ne har kika buge kika fita hayyacin ki. Shine na kawo ki nan domin ciwon da kanki yake bayan kin fadi. Sannan mahaifiyar mu tazo ganin ki, nan ne naji kina fada mata cewa ...”

Shuru yayi, ita kuwa tsoro ya kara kamata. Tana tunanin me kuma Amriya ta aikata.

“Please ka fada min komai..”

“Kin fadawa mahaifiyar mu cewa, Salmah tana bin maza a waje. Fatan kin gane me nake nufi?”

“A'a..a'a.. ba zai yiwu ba... Ba ni na aikata hakan ba..”

“Wai kina yin kamar kin manta ne? Ko kuwa da gaske kin manta abinda kika yi?”

“Please Malam, ka taimake ni na fita daga gidan nan.”
Bata san dalilin da yasa Amriya tayi hakan ba, amma ta dau alkawarin ba zata sake bari ta cutar da wannan matar ba. Ya kamata ta bar gidan nan, kafin ta sake shiga jikin ta, ta sake aikata wani abun.

“Kina son in kai ki gidan ku ne? Amma kafin nan ina son sanin meke faruwa? Ko baki lafiya ne?”

“A'a ba zan iya zuwa gida a irin wannan shigar ba. Ka fidda ni nesa da nan kafin ta dawo, please.” Ta shiga rokon sa.

“Kafin ta dawo?”

“Zan yi maka bayanin komai, bayan mun fita daga gidan nan. Nayi maka alkawari.”

Kamal kansa ya kulle, amma duk da haka ya yanke shawarar taimakon ta. Kafin su bar gidan, ya shiga dakin kanwar su, cikin kayan ta, ya daukowa Zahara doguwar jallabiya kamar yanda Zahara ta nema, ba zata iya tashi tsaye ba sai ta canza kaya.

Fita suka yi ta kofar bayan gidan ba tare da wani ya gansu ba. Kamal komawa yayi ya dauko motar sa, ya dawo ya dauki Zahara.

Suka tayar da motar, suka bace cikin duhun dare.

-----------------------------------------------------------------

AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
  2. 2 CHAPTER 1
  3. 3 CHAPTER 2
  4. 4 CHAPTER 3
  5. 5 CHAPTER 4
  6. 6 CHAPTER 5
  7. 7 CHAPTER 6
  8. 8 CHAPTER 7
  9. 9 CHAPTER 8
  10. 10 CHAPTER 9
  11. 11 CHAPTER 10
  12. 12 CHAPTER 11
  13. 13 CHAPTER 12
  14. 14 CHAPTER 13
  15. 15 CHAPTER 14
  16. 16 CHAPTER 16
  17. 17 CHAPTER 15
  18. 18 CHAPTER 17
  19. 19 CHAPTER 18
  20. 20 CHAPTER 19
  21. 21 CHAPTER 20
  22. 22 CHAPTER 21
  23. 23 CHAPTER 22
  24. 24 CHAPTER 24
  25. 25 CHAPTER 23
  26. 26 CHAPTER 25
  27. 27 CHAPTER 26
  28. 28 CHAPTER 27
  29. 29 CHAPTER 28
  30. 30 CHAPTER 29
  31. 31 CHAPTER 30
  32. 32 CHAPTER 31
  33. 33 CHAPTER 32
  34. 34 CHAPTER 33
  35. 35 CHAPTER 34
  36. 36 CHAPTER 35
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});