Chapter 35
CHAPTER 34
I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 34 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”
http://www.ashblogg.com.ng/2022/04/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-34.html
Yau Ammar da wuri ya tashi daga aiki. Zahara bata nan yanzu dan haka wahalar ji da ayyuka a kwanakin nan yake. Hakan ne yasa ya ɗauki tsohon sakataren mahaifinsa da ke aiki yanzu a wani kamfanin domin ya taya shi. Da yake sakataren yanada ƙwazo sai ya zamana Ammar ya samu isasshen lokacin ji da wasu matsalolinsa na in da cen.
Yanke shawarar zuwa gidansa ya yi domin yin magana da Hafsat da kuma ganin ko ta dawo hayyacinta. Saidai lokacin da ya je gidan ya yi mamakin ganin Afnan ita kaɗai. Bai yi wani mamaki sosai ba, shi yasa ya yi abinda ya yi domin hana ta tafiya a halin da take ciki.
Kasa ɓoye fushinsa Ammar ya yi, ya sa ran ko magana su yi kafin ta yi tafiyarta. Ya ji haushi sosai da yasa ya sauke kan kanwarsa Afnan.
“Ko ƙoƙarin tsayar da ita da kin yi ai..” Ya ce wa Afnan cikin ɗaga murya.
Afnan da ke saka takalmi domin komawa school ta yi saurin ɗagowa jin abinda ɗan uwanta ya ce. Da sauri ita ma ta ce :
“Ta yaya zan iya tsayar da ita idan kai ma ka kasa? Ba ƙaramar yarinya ba ce, na yi ƙoƙarin lallaɓa ta amma ko kula ni bata yi ba.”
“Ai da sai ki kira ni ki faɗa min. Abinda ya kamata ki yi Afnan ! Bansan me yake damun ki cikin kai ba.”
“Ni ce ko kuwa sauke fushinka kake a kaina? Ni zan tambayi me yake damun ka, matar nan bata son tsayawa nan, ina ga ya kamata ka yi tunani kuma ka shafa mata lafiya. Ka cece ta, toh me kuma kake so bayan wannan? Ta yi maka godiya? Idan baka fahimta ba, bari na sanar da kai, wannan yarinyar ta tsane ka. Ya kamata ka daina ƙoƙarin shi-shige mata.” Afnan ta faɗa masa.
Kalamanta sun shiga kunnuwan Ammar kuma sun ƙara haura fushinsa.
“Ki tafi daga nan kafin raina ya ƙara ɓaci.” Ammar ya ce wa Afnan ƙasa da murya.
“Eh ai haka zaka ce..” Cewar Afnan saidai duk da haka ta yanke tafiya ganin adadin yanda ta fusata yayan nata.
Rufe kansa Ammar ya yi cikin ɗakinsa. Rai a yamutse. Ya kasa fahimtar me yasa ransa ke ɓaci har haka. Ba ƙaunar juna suke ba tun asali amma me yasa ji daga bakin ƙanwarsa ya fusata shi haka? Yasan tsakanin shi da Hafsat ba wata ƙwaƙwarar soyayya ke akwai ba, kuma hakan bai dame shi ba. Saidai yau Ammar yana jin wani sauyi a cen cikin zuciyarsa.
“Na tabbatar tausayinta ne kawai..” Ya faɗa cikin ransa.
Bayan duk abinda ya faru da ita, tabbas ya ji tausayin ta. Wannan yasa yake ƙoƙarin ƙulla wata sabuwar alaƙa da ita.
“Ko ma dai meye Afnan tayi gaskiya. Na taimake ta, shikenan yanzu. Ya kamata in mayar da hankali ga rayuwata da kuma Shari'ar ƴar uwata. Wannan ne yafi muhimmanci.” Ya faɗa.
Bayan wasu kwanaki, Ammar ya kasa manta Hafsat. Yarinyar nan ta ƙi fita daga cikin kwanyarsa hakan kuma ya kusan mayar da shi mahaukaci. Kamar wanda aka yiwa sihiri, hargitsi ne cikin kansa. Kuma babban abun, har yau yana tunanin iya tausayinta ne kawai yake ji. Wata rana, ya yanke zuwa gidansu Hafsat domin ganin yanda take. Idan ya tabbatar tana nan lafiya wata ƙila ya ɗan samu sukuni cikin ransa. Da wannan tunanin Ammar ya tafi neman Hafsat.
Mahaifiyar Hafsat tayi mamaki saidai tayi murna da ganin Ammar. Ƴarta kusan bata cin komai kuma kullum rufe kanta take cikin ɗaki, bata fitowa kuma ta daina zuwa wajen aiki. Kowa damuwar halin da take ciki yake, amma ita bata yi komai da zata kwantar wa da dangin nata hankali ba.
“Shigo ɗana, ya kake?”
“Lafiya lau nake Mama, fatan kuma haka?” Cewar Ammar yayin da yake bin bayan mahaifiyar Hafsat zuwa falo.
“Lafiya lau Alhamdulillah, ya momynka?” Ta tambaye shi.
“Tana nan lafiya.”
Ammar ya bata amsa a gaggauce da gudun kar ya tuna memories masu ɗaci.
“Masha Allah. Na kawo maka abun sha ne?"
“A'a nagode Mama, ina son ganin Hafsat ne.”
Shuru mahaifiyar Hafsat tayi na wasu ƴan daƙiƙu kafin ta ce masa :
“Bana son shiga sha'aninku amma ina tunanin baku rabu ta daɗi ba haɗuwarku ta ƙarshe. Zan iya cewa ko kun sake haɗuwa kuma saboda kai ne take cikin wannan halin? Idan haka ne Ammar, ba zan..."
Katse ta Ammar ya yi.
“Kiyi haƙuri Mama, amma ba abinda kike tunani ba ne. Ban ma san bata jin daɗi ba, na zo ganin ta ne kawai domin sasanta tsakaninmu. Tun bayan abinda ya faru tsakaninmu, bana jin daɗi. Ina son samun sukuni da kaina. Ko wani abu yana damunta ne?”
Ammar ya tilasta kanshi yin ƙarya, domin abinda ya fahimta Hafsat bata faɗawa mahaifiyarta komai ba.
“Ah har naji daɗi ɗana, da ba kai ne silar damuwar ƴata ba. Kuma abu ne mai kyau da ka zo ku sasanta tsakaninku. Halin musulmin kirki ne, nayi murna sosai. Wata ƙila kai ka yi nasarar saka ta ta yi magana, hankalinmu a tashe yake.”
“Kar ki damu zan yi hakan Mama, tana ina yanzu?” Ammar ya tambaya.
“Tana ɗakinta, a sama ɗaki na ƙarshe. Kar ka biye mata idan ta gwada yin wani abun, kamar yanda na faɗa maka ba a hayyacinta take ba a halin yanzu.”
“Kar ki damu da ni Mama, nasan me zan yi."
Mahaifiyar Hafsat ta yi wa Ammar izini ya hau sama wajen Hafsat, tana addu'ar Allah yasa shi ya shawo kan ƴar tata.
Knocking yayi sau uku, sannan ya jira. Cikin ƙaramar murya Hafsat ta tambayi waye ke knocking.
“Ni ne." Ammar ya faɗa.
Cikin bacci-bacci Hafsat ta ɗauka mahaifinta ne ya yi magana. Bata yi tunanin Ammar zai yi gangancin zuwa gidansu har ƙofar ɗakinta ba, shi yasa da ta ji muryar namiji ta zata mahaifinta ne. Saidai lokacin da ta buɗe ƙofar ta yi ido huɗu da Ammar kusan faɗuwa ta yi. Ƙoƙarin rufe ƙofar ta yi amma Ammar ya yi saurin sa ƙafa ya tare ƙofar. Ƙarfi Ammar ya sa ya shigo sannan ya rufo ƙofar.
Cikin takaici, Hafsat ta juya ta koma bisa gadonta.
“Idan ka zo ne ka tsokane ni, Bismillah ga guri nan." Hafsat ta faɗa a hankali.
“Me yasa zan tsokane ki Hafsat? Kar ki ce min saboda haka ne kike gudu na?” Ammar ya tambaye ta.
“Eh ni sakarya ce, na je nayi sakarcin da bai dace ba a wurin da bai dace ba, ban ga dalilin da zai sa ba zaka tsokane ni ba? Ba abinda kullum kake min ba kenan?” Hafsat ta faɗa da shaƙaƙiyar murya.
A hankali Ammar ya ƙaraso inda take.
“Yi min wuri please, ina son muyi magana.”
Bayan dogon nazari da Hafsat ta yi, ta ƙara matsawa nesa da inda take zaune domin bashi guri ya zauna. Ammar bai yi mamaki ba da ganin hawaye cike da idanun Hafsat.
“Na taimake ki ne domin ba zai taɓa yiyuwa na ƙyale ki cikin wannan matsalar ba. Idan ina nan saboda na damu da halin da kike ciki ne, ba wai dan na yi miki izgilanci ba. Ba mutumin da kika sani a baya ba ne, stupid and dumbass. Ina son kawai na ga kin dawo daidai. Bana yin hakan domin samun wani abu daga gare ki, zan iya yin hakan ga kowace mace domin nasan adadin yanda hakan ke wargaza rayuwa.”
“Ban nemi taimako daga gare ka ba, kuma bana buƙatar tausayinka. Tambayar da nake wa kaina, yanda kasan duk wannan zancen, wa ya sani ma ko kana da hannu a ciki? Wa ya sani ko kai ne ka saka shi ya yi min barazana domin daga baya ka zo a matsayin jarumi a haka zai sa in sauko ta yanda zaka iya samu na cikin sauƙi.”
Mamakin jin abinda ta faɗa, sai da ya ɗauki lokaci kafin ya yi magana.
“Ban yi mamakin jin hakan daga gare ki ba, na ji haushin hakan sosai. Har abada tunanin yin hakan ba zai taɓa zuwa kaina ba. Na yi bincike a kanki ne saboda na damu sosai. Dole ne na fitar da ke daga nan domin kamar yanda na faɗa miki ba wanda kika sani ba ne a baya. Amma ina ga Afnan tana gaskiya, kin tsane ni kuma babu abinda zai canza hakan. Idan kin shiga wannan halin ne da tunanin zan tsokane ki kuma na sanarwa duniya abinda kika aikata, zaki iya cigaba da rayuwarki domin ni inada abubuwa mafi muhimmanci a gabana. Hankalin familynki ya tashi, dan haka kiyi wani abu domin kwantar musu da hankali.” Ya ƙarasa maganar tareda miƙewa tsaye.
“Ina mai baki haƙuri akan duk abinda nayi miki domin ina tunanin hakan ne ya sa kike tunanin zan iya komai domin na ƙuntata miki. Bugu da ƙari, ni ba wanda kika sani ba ne a baya amma hakan ina tunanin abinda ba zaki iya gwada ganewa ba ne. Na barki lafiya Hafsat. Ki kula da kanki.” Ya ƙara da hakan kafin ya bar ɗakin.
Hafsat bata san ma me zata yi tunani ba, wannan mutumin ya taimake ta da gaske amma ta kasa daina tambayar kanta dalili, ganin basu taɓa jituwa daidai da rana ɗaya ba. Tana tambayar kanta me yasa lokaci guda yake son shiga al'amuranta. Tana tunanin ta wuce iyaka na zarginsa da ta yi amma ta yi hakan ne kawai domin kare kanta daga tsokanar da zai yi mata. Bata son saurarar muryar da ke ta mata yawo cikin kai akan cewa wannan mutumin ya sauya. Bata son sauke makamai kuma ta sake faɗawa wani tarkon. Ta cutu iya haka, ya kamata ta yi nesa da maza a halin yanzu, har sai ta dawo hayyacinta.
To be continued....
AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story📖
By Malik al-Ashtar 🖋
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35