Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

CHAPTER 22

Amriya Hatsabibiyar Aljana Book 1 Complete Hausa Novel 3,023 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚

Suna zuwa asibiti aka kwantar da shi. Sai da ta jira na wasu mintuna kafin aka ce ta shiga ta ganshi. Da ta shiga ta tarar wata nurse na saka masa ruwa. Nan take fada mata zai samu waware bayan anyi masa karin ruwan.

Zaunawa tayi kusa da shi.

“Ki je gida kafin dare ya kara yi sosai.” Ya fada da gajiyayiyar murya da alamun bacci.

“Tun dazu na kira Mama, tasan ina nan.”

“Ina son ki tsaya amma bana son ki tafi gida ke kadai bayan nayi bacci.”

“Ba zan tafi ba, kayi hutawar ka. Idan ka tashi zaka gan ni.”

“Kira Khadija ki ce mata taje gida. Duba cikin wayata zaki ga number ta.”

“Ok zan yi hakan daga baya. Ya jikin naka yanzu?” Ta tambaye shi.

“Abun mamaki na fara jin sauki. Ayyuka ne da dama nayi kwanan nan, kuma bana cin abinci sosai.”

“Iya wannan ne kawai?” Ta tambaye shi.

“Sai kuma wata matsala da ta taso gidan mu.”

“Ok zamu yi maganar daga baya, naga alamun bacci kake ji yanzu. Zan je na kira Khadijar ka.”

Dariya yayi sannan yace da ita.

“Wannan ba Zahara da na sani bace.”

Murmushi tayi itama sannan ta fita bayan ta dauki wayar shi. Kiran Khadija tayi. Ringing na farko ta dauka.

“Kana ina ne Kamal? Yanzu kusan awa daya da rabi kenan baka dawo ba.” Khadija ta fada rai a bace.

“Zahara ce.” Zahara ta bata amsa, haushi ne ya kara kama Khadija tace
“Me wayar Kamal take yi hannun ki?”

“Yana asibiti ne."

“What? Me ya same shi? Sai da na fada masa ba idea bace mai kyau zuwa wajen ki a yanayin da yake ciki. A wace asibiti kuke?”

“Yace zaki iya tafiya gida, zaki iya ajiye makullen karkashin carpet.”

“Tambayar ki nake a wace asibiti kuke? Bana jin zan iya tafiya gida alhali bestie na yana kwance asibiti.”

“Ok, muna Shareef Hospital ta babban titin...”

Bata ma karasa magana ba, Khadija ta katse kiran. Zahara a ranta tace Kamal da kwashe-kwashen abokai yake, da alamu ba zasu jitu ita da Khadija ba.

Komawa tayi cikin dakin da Kamal yake kwance, ta tarar da nurse tace mata bata dade da fita ba yayi bacci, dan haka ta dan kishingida kan doguwar kujera kafin ya tashi.

Zahara na tunanin ta dan jima tana bacci domin dariyar da su Kamal ce suke yi ta tashe ta. Firfigit tayi ta tashi, nan taga Khadija har ta iso shima Kamal ya tashi daga baccin. Khadija na zaune bisa gadon kusa da Kamal. Kishi ne ya turnuke Zahara ganin kusancin dake tsakanin su.

“Sorry mun tashe ki?” Cewar Kamal.

“Ba komai, ban yi tunanin baccin zai dauke ni haka da sauri ba.”

“Zaki iya tafiya idan kina so, ni zan tsaya nan.” Cewar Khadija.

“No, na fadawa mahaifiya ta zan zauna nan.”

“Eh, amma kuma kin gaji.” Cewar Khadija. “Kar ki damu ni zan zauna, ba wani abu zan yiwa Kamal din ba.”

“Khadija...” Cewar Kamal yana harar ta.

“Ok, wasa nake."

“Ku je gida ku duka, ba zasu barku ku kwana nan ba.”

“Amma..."

“Na fara samun sauki, leda daya ce ta rage min. Kuma zuwa gobe zasu sallame ni, dan haka kar ku damu. Yanzu Ammar zai zo.”

“Zaki iya kaita gida please, hankali na zai fi kwanciya idan kece kika mayar da ita gida.” Ya cewa Khadija.

Murmushi Khadija tayi masa.

“Shikenan, zan kaita gida. Zan dawo gobe zuwa karfe shidda na yamma.”

“Good, ko zaki bamu minti biyu zan yi magana da Zahara.”

Sai da ta kalle su kafin ta fita ba tare da ta rufo kofar ba.

“Na sani ba haka muka yi da ke ba amma ina son ki koma gida ki huta kema.”

“Bestie din nan taka ba sona take ba, ta yaya zan iya jure zama kusa da ita?"

“Kar ki damu zan yi mata magana, tana a dan takure ne domin ita kadai ce mace da nake tare da ita. Zan yi mata magana kar ki damu.”

“Shikenan."

“Toh ki saki fuskar mana. Da na samu sauki zan yi mata maganar ki.”

Gyada masa kai tayi a matsayin amsa.

“Zaki zo ne mu tafi ko kuwa?” Khadija ta fado dakin kamar daga sama da har ta dan tsorata Zahara.

Bye Zahara ta yiwa Kamal da hannu shi kuwa ya mayar mata da murmushi. A hankali ta rufo masa kofar sannan tabi bayan Khadija. Halin Khadija ya fara baiwa Zahara haushi, domin yanzu ta kara tabbatar da Khadija ba sonta take ba kuma bata da alamun shafa mata lafiya. Kallon ta, murmushin ta da duk wani motsi nata ba karamin tsorata Zahara suke ba.

Bude kofar motar Khadija tayi sannan tacewa Zahara ta shigo. A kan hanya babu wanda yacewa wani kala, amma Zahara lokaci- lokaci tana jin idanun Khadija a kanta ta yanda ta kagu ta sauka daga motar tareda alkawarin ba zata kara kadaicewa ba da Khadija ko na minti daya. Sosai take tsoron ta domin a yanda take ji kamar tayi ta kurma ihu amma kuskure ne ta nunawa Khadija tana tsoron ta. Akwai wani abu a Khadija da ke bata tsoro kuma ta kasa gane menene.

Ya kamata Kamal yayi saurin yi mata magana, domin ta shafa mata lafiya. A kira ta da kowanne suna amma ba zata iya ja da Khadija ba..

Nuna mata hanyar gidan su tayi. Koda suka kawo, Zahara da sauri ta fita daga motar. Koda ta shaki iskan unguwar su wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke. Ganin ta zo gida lami lafiya.

Shigewarta gida tayi ba tareda ta juyo ta kalli Khadija ba, tana shiga taji Khadija ta tayar da motar tayi tafiyar ta.

A BANGAREN KHADIJA

Ajiye candles din tayi kamar yanda matar ta fada mata ta yi sannan ta zauna a tsakiya. Matar ta fada mata ta rufe idanu.. har lokacin da zata ji alamun zuwan ta. Babu alamun tsoro ga Khadija domin ta tabbatar matar ba zata cutar da ita ba. Kamar yanda tayi mata wannan alkawarin.

Tattare doguwar rigarta tayi, tayi zaman indiyawa idan zasu yi bauta sannan ta shiga jiran zuwan matar. Ita kadai, cikin duhu, tana jiran zuwan matar da kowa bace face aljana Amriya. Idanun ta a rufe ta nutsu sakamakon duhun dare da kuma shurun da ya mamaye ko ina. Bayan wasu awanni.. taji sautin tafiya na nufo inda take. Bugun zuciyar Khadija na tafiya daidai da sautin kafafun wacce take jira.

Boom...Boom...Boom

Bayan matar wato Amriya ta karaso inda Khadija take... A hankali ta shafa wuyan Khadija. Khadija taji dumin numfashin Amriya da lallausar fatar hannun ta. Babu alamar tsoro tattare da Khadija.

“Kin kawo abinda na tambaye ki?” Amriya ta rada mata a kunne.

Gyada mata kai Khadija tayi.

“Good, ajiye shi a gabanki.”

Khadija ta aiwatar kamar yanda Amriya tace, T-shirt din Kamal ta fiddo da ta dauko cen gidan sa.

“Har yanzu kina kan bakan ki ba zaki canza shawara ba?” Amriya ta tambayi Khadija.

“Eh, ayi duk abinda ya dace.”

“Kinsan abinda ya rage kiyi.” Amriya tace mata.

Bude idanu Khadija tayi, ta dauki yar wukar dake kusa da ita, a hankali tayi yar karamar yanka a tafin hannunta, ta tara jinin dake zuba a jikin rigar Kamal. Bayan tayi hakan, ta dauki almakashi ta yanki dan kyalle jikin rigar sannan ta kona shi a cikin daya daga cikin wutar candle kamar yanda Amriya ta nuna mata.

Dan taku Amriya tayi, ta dan yi nesa da Khadija, sannan ta juyo a nutse tana nufo inda Khadija take. Tafiya take tana magana cike da nutsuwa.

“Kin shirya?” Ta tambayi Khadija.

“Eh.. na shirya.” Cewar Khadija.

“Kin bani izini, na shiga jikin ki?”

“Eh.” Khadija ta bata amsa.

“Kinsan duk wani abu da zan yi saboda farin cikin ki ne ko?”

“Eh, na sani.” Khadija ta bata amsa.

“Kin shirya domin karbata cikin jikin ki?"

“Eh.." Sai da Khadija ta dan yi jim sannan ta bata amsa. Tana tambayar kanta idan wannan abun da zata aikata, babu wani mummunan sakamako da zai biyo baya. Saidai lokaci ya kure na yin wani shakku. Ta riga da taba Amriya amincewar ta, kuma Amriya a shirye take ta taimaka mata.

“Na shirya."

Khadija ta bata amsa cike da kwarin gwiwa wannan karon.

“Rayuwar ki zata canza daga yau, nayi miki alkawari.”

A BANGAREN AMMAR

Yau ya tashi cike da kudirin tunkarar Salmah suyi magana. Yana ganin jiran ya isa haka. Ya kamata ya yi mata magana, domin sanin inda soyayyar su ta kwana. Yana sonta da iya zuciyar sa amma baya tunanin kara wani jiran. Yana jin kamar yanzu ta daina sonshi. Dan haka yana so tayi masa bayanin gaskiyar abinda ke zuciyar ta.

“Hello? Lafiya kuwa?”

Ya mayar da hankalin sa ga Sarat da ta shigo da wasu documents a hannunta.

“Tunanin me kake?” Ta tambaye shi.

“Ba wani abu ba ne mai muhimmanci.” Ya bata amsa tare da yi mata murmushi domin tabbatar mata.

“Idan kana bukatar wani abu ina nan ok." Cewar Sarat.

“Insha Allahu, nagode Sarat."

“Good, ni zan koma na cigaba da aiki. Ka huta lafiya."

Gyada mata kai yayi, tayi murmushi tare da rufo masa kofar.

Bai san me yasa ya kasa dakatar da komai tsakanin sa da Sarat ba alhali har yanzu yana son Salmah. Kawai abinda ya sani kasancewar Sarat a kusa da shi yana debe masa kewa.
Yana yin tamkar Sarat bata wuce spare tayar mota a wurin sa ba, saidai tafi hakan. Tana sauraron sa a duk lokacin da yake da bukatar yin magana.. kuma tana gamsar da shi game da sabuwar rayuwar da ya daukarwa kansa.

Yana ganin tana jiran fiye da haka a wurin sa, saidai bai shiryawa wannan ba...

Da yamma ya shirya yaje kofar gidan su Khadija. Ya tabbatar Salmah har yanzu cen gidan take. Dan nesa da gidan ya faka motarshi yana tunanin abinda zai fada mata.

Yana cikin tunanin ya hango wata mota ta faka kofar gidan Khadija. Bayan wasu mintuna kuma yaga Salmah ta fito daga gidan taci kwalliya. Tana sanye da doguwar riga mai daukar hankali, da takalma masu tsini da kuma yar karamar jaka a hannunta. Tayi kyau sosai, saidai yanayin sa sauyawa yayi lokacin da yaga ta shiga motar.

Wani masifaffen kishi ne ya rufe shi. Tambayoyi da dama na ta yi masa yawo, saidai wacce tafi tsaya masa itace : Da gaske Salmah ta shirya manta shi?

Ba zai iya kyalesu su tafi ba, Salman shi ce. Batada 'yancin kasancewa da wasu mazan...a'a.

Ba tare da yin wani dogon tunani ko sanin abinda zai biyo baya ba, ya fara bin motar su a baya. Yana tafe yana addu'ar mayar da hankalin sa ga tuki kar ya yi accident.

Bai ma san me Salmah zata ji idan ta gane alakar shi da Sarat ba. Yanzu yake tambayar kansa idan dama ta taba sonshi. Ba zata iya rufe babinsa haka ta sauki ba. Ba mai yiyuwa bane wannan, Salmah da ya sani ba zata taba yin hakan ba. Tayi alkawarin gara ta mutu da ta koma rayuwar ta ta baya.

A ransa yace wata kila wanda take tare da shi aboki ne ko dan uwa kawai, bai dace ya dinga irin wannan tunanin a ransa ba.

Bayan wasu mintuna sai gasu gaban wata babbar 4 stars restaurant. Mutumin ne ya fito daga motar ya zagayo ya budewa Salmah kofa. Duk da dan nisa dake tsakanin su, Ammar ya iya hango yanda Salmah ke ta zuba murmushi. Hakan ya kara tuna masa adadin yanda yayi kewarta. Komai nata yayi kewar sa : Murmushin ta, dariyar ta, yanda take zuba masa masifa idan tana tunanin ita ke da gaskiya. Yayi missing dinta sosai.

Koda yaga saurayin nan ya zagaya hannun sa ya riko kugun Salmah ya tabbatar masa da ba aboki bane kuma ba dan uwa bane.

Wani irin bakin ciki Ammar yaji a zuciyar sa. Bai jira ko na second daya ba. Yayin da yake fitowa daga cikin motar shi, su kuwa su Salmah har sun shiga farfajiyar restaurant din.

Kulle motar sa yayi yabi bayan su zuwa ciki.

Da shigar sa ciki bai ko tsaya kula daya daga cikin ma'aikatan wurin dake tambayar sa ko yayi reservation ne, ya nufi inda masoyan ke kokarin zaunawa. Sosai yake cikin bacin rai ta yanda yake jin zai iya dukan ko waye.

“Me kika zo yi nan?”

Ya karaso inda suke. Koda Salmah ta hada ido dashi tayi mamakin ganin sa kuma ta tsorata.

Hannun ta Ammar ya kamo da karfi.

“Muje, babu abinda zaki yi a nan.”

“Waye kai da ka isa ka yiwa budurwata haka?” Cewar saurayin da ke tare da Salmah.

“Baby kin sanshi ne?” Saurayin ya tambayi Salmah.

A daidai lokacin kuwa Ammar na kokarin fitar da Salmah daga wurin ta karfi.

“Mahaukaci ne kai? Sake ni Ammar, ni ba yar tsanar ka bace. Ka sake ni ! ”

Yana kokarin karasa fita da ita wani security yazo ya raba su. Salmah ta boye bayan security din.

“Bansan wannan mutumin ba, me yasa kuke barin kowanne mutum yana shigowa ciki?”

Security ba tareda ya kara jiran ko minti daya ba, ya damki Ammar ya fitar da shi waje. Bai kuwa sha wahalar fitar da shi ba domin yanda yake da girma. Duk da kokowar da Ammar yake amma saida security'n ya fitar da shi ba tare da wata matsala ba.

“Zamu hade Salmah, na rantse miki zamu hadu.” Ya kwalla kwarai yanda zata jishi.

Ba tareda ya jira jin gargadin da security yake masa ba, ya shiga mota ya nufi gidan Kamal.

(....)

“Dariyar me kake yi? Na fada maka fa Salmah taci amana ta.” Ammar ya fada cike da takaicin yanda dan uwan nashi bai dauki maganar da muhimmanci ba.

“Ni kuma na fada ma ba cin amanar ka tayi ba, daman ta fada maka bata bukatar ka yanzu.”

“Eh amma tana cikin fushi ne, ba hakan bane a zuciyar ta.”

“Sosai haka ne a ranta." Cewar Kamal yana kokarin rike dariyar sa.

“Shikenan, ni zan wuce gida na."

“Ka kwana nan, I need your help dan ban karasa warkewa ba."

“Je ka ga Zaharar ka, ni gida zan je."

“Kar kayi haka, da gaske I need your help."

“Shikenan amma gobe tun da safe zan yi tafiya ta, domin zan je in ga Dr. Abdallah daga nan in wuce gidan su Salmah domin ban kare da ita ba."

“Yaya akwai wani cigaba game da lamarin Afnan?"

“Eh, a yanda Dr. Abdallah yayi min bayani ta amince zata yi magana da shi. Shi yasa ma yake son gani na."

“Toh Allah yasa komai yaje daidai. Me zai hana ka mayar da ita gidan ka?” Kamal ya tambaye shi.

“Nayi wannan tunanin nima. Amma nafi son ka dawo da ita nan wurin ka, ganin ni inada aiki sosai ina tunanin zata fi sakewa nan."

“Ni akwai tafiyar da zan yi cikin makon nan, akwai wasu ayyuka da nake son kammalawa kafin na bude workshop dina."

“Ah, daman baka watsar da wannan project din ba?"

“A'a, ni ban taba tunanin haka ba. A ina kaji wannan?”

“Nayi tunanin zaka cigaba da zuwa kana dafa min a kamfani."

“Boye murnar ka, nasan ka jima kana mafarkin jagorantar wannan kamfanin kai kadai. Kuma kasan bani da ra'ayin harkar kamfanin nan, daman ina zuwa ne domin baka shawarwari ganin kai sabo ne a jagorantar babban kamfani kuma naga kana kokari sosai dan haka nima zan karkata gun nawa mafarkan.”

“I will support you whatever happens.” Cewar Ammar.

“Thanks." Kamal ya fada. “Kuma idan na dawo ina son zuwa neman auren Zahara.”

“What? Amma wasa kake ko?”

“A'a ! "

“It Zaharan ta amince ne? Bai yi wuri ba yanzu? Kay ! Yarinya ce fa har yanzu."

“Mun yanke zamu yi aure wata mai zuwa.”

“Amma tilasta ta kayi ko?”

“Kamar yaya, me yasa zan tilasta ta?”

“Abin ne da mamaki, ni dai nasan kai da ba son rayuwa kake da mutane ba, har ma da mu, yanzu kuma kace min zaka yi aure? Na tabbatar ka sihirce Zahara dan ta amince. Ko kuma ita ce ta sihirce ka dan ka fara tunanin aure.”

“Ba yaro bane ni yanzu kuma ina ganin Zahara ita ce matar da ta dace da ni. Ba zan so in batawa kaina lokaci ba.”

“Ita kuma Khadija fa?" Ammar ya tambaye shi.

“Khadija me?”

“Tana da labari?”

“A'a zan yi mata maganar idan na dawo. Kuma ina son yi mata magana game da abinda take wa Zahara, bana jin dadin hakan. Domin Zahara a takure take kuma na fahimci hakan.”

“Ba dai sun hadu ba?” Ammar ya fada da mamaki yana mai kara matsawa inda Kamal yake kwance.

“Eh.. akwai zafi-zafi tsakanin su.”

“Rayuwar ka kamar shirin film bro, ya kamata ka dinga yimin update duk sati. Me kake jira, na fada maka irin son da Khadija take maka. Amma ka ki ka bude ido.”

“Ta fada min, ta fahimci mu biyu ba mai yiyuwa bane, ta fahimta amma ni ba haka yanayin ta ya nuna min ba.”

“Haka ta fada ma? Da mamaki amma ina baka shawara da ka bata lokaci zata dawo daidai.”

“Zan yi mata magana. Ina son ta fahimta a yita ta kare.”

“Allah ya bada sa'a. Amma har yanzu mamaki nake wai zaka yi aure kuma Zahara zaka aura. Zan so kuwa ganin yanda rayuwar ku zata kasance as a couple.”

“Kaji da Salmah da Hafsat shi yafi ma. Yaushe zaka je ka ga Mom?”

“Daina min wannan zancen ko nayi tafiya ta."

“Kasan dai ba zaka cigaba da share ta ba, ko mai ta aikata maka ba zaka taba canza sunanta ba na mahaifiyar ka. Ba karamin hatsari bane abinda kake yi. Kasan darajar da iyayen suke da ita."

“Kai ni kaga tafiya ta, Allah ya koro sauki.” Cewar Ammar yana mikewa tsaye.

“Ka yiwa kanka karatun ta nutsu dai.”

“Zan je wajen Sarat, domin ita kadai ke fahimta ta a halin yanzu.”

“Wacece kuma Sarat?”

“Bar zancen, na tafi.”

To be continued...
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels http://www.ashblogg.com.ng/search/label/Hausa%20Novels

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
  2. 2 CHAPTER 1
  3. 3 CHAPTER 2
  4. 4 CHAPTER 3
  5. 5 CHAPTER 4
  6. 6 CHAPTER 5
  7. 7 CHAPTER 6
  8. 8 CHAPTER 7
  9. 9 CHAPTER 8
  10. 10 CHAPTER 9
  11. 11 CHAPTER 10
  12. 12 CHAPTER 11
  13. 13 CHAPTER 12
  14. 14 CHAPTER 13
  15. 15 CHAPTER 14
  16. 16 CHAPTER 16
  17. 17 CHAPTER 15
  18. 18 CHAPTER 17
  19. 19 CHAPTER 18
  20. 20 CHAPTER 19
  21. 21 CHAPTER 20
  22. 22 CHAPTER 21
  23. 23 CHAPTER 22
  24. 24 CHAPTER 24
  25. 25 CHAPTER 23
  26. 26 CHAPTER 25
  27. 27 CHAPTER 26
  28. 28 CHAPTER 27
  29. 29 CHAPTER 28
  30. 30 CHAPTER 29
  31. 31 CHAPTER 30
  32. 32 CHAPTER 31
  33. 33 CHAPTER 32
  34. 34 CHAPTER 33
  35. 35 CHAPTER 34
  36. 36 CHAPTER 35
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});