Chapter 28
CHAPTER 27
I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 27 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”
http://www.ashblogg.com.ng/2022/03/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-27.html
Sarat ta yanke shawarar tunkarar Ammar. Sai da tayi kokowa akan hakan sau ba adadi kafin ta yanke wannan shawarar. Ta ɓata dare da rana tana tambayar kanta idan yiwa oganta maganar aure ba zai sa shi ya gudu ba domin duka su biyun basu san wanne suna zasu baiwa alaƙarsu ba.
Idan da ta ita ce, bata ƙi su cigaba da rayuwarsu a haka ba, ba tare da tayi masa zancen aure ba, amma yanzu da mahaifiyarta ta shigo zancen, wani labarin ne kuma daban. Kuma mahaifiyarta ta sanar da ita cewa tayi kuka da kanta idan wani abu marar kyau ya biyo baya. Tana son itama a kirata matar wani, amma tana tsoron yi masa maganar dan kar ya gujeta kuma ta rasa shi gaba ɗaya.
Jiya tayi magana sosai tsakanin ta da mahaifiyarta. Tana son jin takamaimai makomar alaƙar ƴarta. Ta tambayi Sarat idan eh ko a'a wannan saurayin yana sonta ne da aure, saidai ko ita ƴarta bata san amsar wannan tambayar ba. Sai lallaɓa mahaifiyarta tayi akan wannan satin zata ji daga Ammar.
Dan haka Sarat ta yanke shawarar yi masa magana yau. Sasai take cikin zullumi. Tana jin tun ranar da mahaifiyarta ta rutsa su a gidanta, Ammar yake wasan ɓuya da ita. Amma yau ta ɗauki ƙwarin gwiwarta hannu biyu ta tsara musu inda zasu haɗu.
Bayan ta sauka daga aiki, ta jira shi bakin motarsa kamar yanda suka tsara. Bayan wasu mintuna Ammar yazo. Suka shiga kallon juna na wasu daƙiƙu kafin ogan nata ya yanke shurun ta hanyar jin yanda take. A sanyaye Sarat ta amsa sannan ta shiga motar bayan ya buɗe. Cikin motar shuru kowanen su yayi, babu wanda ya iya cewa ƙala. Wannan yanayin sabo ne gare su kuma yanayi ne mai cike da takura. Sarat yi tayi kamar hankalinta na ga wayarta shi kuma Ammar ga tuƙinsa.
Bayan sun ƙaraso hotel, suka wuce sama. Sarat bata nadamar zaɓar wannan wurin domin tana ganin nan ne zasu samu damar yin magana a nutse.
“So, how are you?”
Muryar Ammar ta dawo da ita daga duniyar tunani. Taji daɗi da shine ya fara magana.
“Fine, kai fa?" Ta bashi amsa.
“Komai lafiya, sai wasu ƴan matsaloli na cen da in da ba za'a rasa ba amma kin san ni, a koda yaushe ina managing situation.” Cewar Ammar.
“Yayi kyau, na lura tsawon watanni kenan bamu yi magana ba." Cewar Sarat.
Kallonta Ammar yayi sannan yayi murmushi.
“Nima yanzu nake lura gaki gani.”
“Ni nafi tunanin kana guduna ne tun ranar da mahaifiyata tace kazo ka nemi aurena."
“Ba gudunki nake yi ba, akwai wasu matsaloli ne da nake son gyarawa kuma da gaggawa. Har barin zuwa aiki nayi akan hakan."
“Kenan baida alaƙa da maganar aure?”
Ammar bai bata amsa ba. Bai gudunta haka kuma baya son aurenta. Bai san ta yaya zai faɗa mata ba ba tare da ya cutar da ita ba.
“Kina ji, a halin yanzu akwai abubuwa da dama a gabana, aure shine na karshe a list ɗina. Amma nayi miki alƙawari zan yi tunani a kai kin ji ko? A halin yanzu zan ji da kaina ne da kuma familyna.”
“Kenan..baka ce a'a ba..? Da gaske zaka aure ni?"
Wannan karon ma Ammar bai amsa mata ba amma Sarat ko a jikinta. Taji abinda take son ji. Yace zai yi tunani, zai iya auren ta kenan. Sosai ta cika da murna ta yanda bata lura da shi yanayin da yake ciki ba. Shi kuwa yayi hakan ne domin ya ɗauke mata hankali na wani lokaci kafin ya samo hanyar da zai bi ya datse wannan alaƙar tasu ba tare da wata matsala ba. A halin yanzu kula da ƙanwarsa Afnan shine a gabansa.
A BANGAREN KHADIJA
Har yanzu bata dawo daidai ba tun bayan wannan mafarkin da tayi. Tun wannan daren, bata sake kwana ita kaɗai ba. Tana iya yi ne kawai idan Salmah na nan. Mafarkin yayi mugun tsorata da yasa har yanzu bata samu kuzarin faɗawa Kamal cikin da ke gare ta ba. Amma yanzu jin ta ɗan samu sauki ta shirya musu haɗuwa a wata babbar restaurant domin yi masa maganar. Bayan abinda ya faru, bata son sanar da shi kai tsaye a kowanne irin wuri, tana son sai ta ɗan saki jikinta kuma ta manta da abinda ya faru. A yanzu, Khadija ta yanke biyewa zuciyarta da kuma ƙin bai wa maganganun Amriya muhimmanci.
Ko hakan shine daidai? Itama bata sani ba! Ta sanar da Kamal su haɗu ƙarfe takwas na dare. Da wannan damar, ta yanke shawarar zuwa kasuwa tayi ƴar siyayya. Taje central siyo kaya, kusan awowi huɗu ta ɓata cikin shaguna. Bayan ta ƙare tana ƙoƙarin komawa gida taji tana son zuwa toilet yin fitsari. Gashi da nisa zuwa gida dan haka ba zata iya riƙewa ba.
Tana ƙoƙarin fitowa daga toilet ɗin cikin babbar central ɗin, taji wani ya bangaje ta. Da niki-nikin ledojin da ke hannunta, ta kasa riƙewa ta faɗi ƙasa. Ɗago kai Khadija tayi cike da jin haushi, da niyyar balbale wacce ta bugeta da masifa saidai shuru tayi lokacin da taga wata dattijuwa ce kuma makauniya.
Tashi Khadija tayi tareda tattare ledojinta.
“Ki bi a sannu ƴata."
Khadija tayi tunanin dattijuwar tace hakan ne saboda faɗuwar da tayi. Har tana ƙoƙarin tacewa dattijuwar ai ita ce ta bangaje ta, ita ce kenan ya dace ta bi a sannu. Saidai Khadija bata ce komai ba, sai ma tambayar dattijuwar da tayi inda zata je.
“Ki bi a sannu ƴata, ki kare kanki. Ki gudu tun akwai sauran lokaci.” Cewar dattijuwar kafin ta faɗo jikin Khadija, ita kuwa Khadija sakin ledojin hannunta tayi ta taro tsohuwar.
Khadija kasa fahimtar komai tayi. Wata taji na ta faman ɗaga murya
“Mamaaaaa..wai kina ina ne!?"
“Ita ce kike nema?" Khadija ta tambayi matashiyar matar. Ƙarasowa matar tayi da ɗan gudunta inda su Khadija suke.
“Allah na gode ma, ashe tana nan. Me ya faru da ita? Alhamdulillahi, na ɗauka ba zan sake ganinta ba, kawai ɗan juya nayi kafin na waiwayo ban ganta ba." Matashiyar matar ta faɗa da ƙwalla a idanunta.
Khadija taji daɗi da ita taga dattijuwar, duk da har yanzu ta kasa fahimtar abinda dattijuwar take nufi.
“Ruƙayya kece?” Dattijuwar ke tambaya bayan ta dawo bisa ƙafafuwanta.
“Eh Mama gani nan, me yasa kika tafi?"
“Ke kika ce nayi gaba." Dattijuwar ta bata amsa.
“A'a Mama, ni ban ce miki komai ba. Kawai ɗan juyawa nayi naga baki nan. Na sha faɗa miki ki daina motsawa idan har baki ji hannuna cikin naki ba."
“Yi haƙuri ƴata."
“Dan Allah ji mana." Khadija ta katse su.
“Na'am." Cewar matashiyar matar.
“Ko zan iya magana da ita?" Khadija ta tambaye ta.
Sai da matashiyar matar ta ɗan yi jim kafin tace Khadija zata iya magana da mahaifiyarta ba matsala, ko ba komai ai ita ta cece ta.
“Me yasa kika ce na gudu, kuma na bi a sannu.” Khadija ta tambayi dattijuwar.
“Wacece ke? Ni ban ce miki komai ba. Ban ma san meke faruwa ba. Ruƙayya muje gida dan Allah, na gaji."
“Yi haƙuri dan Allah, mu zamu tafi, mahaifiyata bata jin daɗi. Mun gode da taimakonki.”
Khadija tana kallon mutanen biyu suka yi tafiyarsu da tambayoyi birjik a zuciyarta. Tafiyarta ita ma tayi tare da mantawa da zancen.
BANGAREN ZAHARA
Zahara ce ta sauko daga wurin aiki. Hankalinta na wani gu, wannan karon ba tunanin Kamal ba take yi. Yau, makarantar aikin jaridar da take burin shiga ce ta ga ta fiddo da gasa kuma zata baiwa mutum talatin wanda suka yi nasarar cin gasar scholarship. Tayi murna sosai amma daga baya tace shigarta gasar baida amfani domin ba zata taɓa zama ɗaya daga cikin mutane talatin ɗin nan da zasu ci gasar ba. Kawai ɓata lokaci da ruwan biro ne zata yi.
Ta zo gida tare da alƙawarin ba zata yi kuka ba. Koda ta saka ƙafarta falo, Maryam tayi tsalle ta maƙale mata. Bata ma barta tasan meke faruwa ba, ta jata zuwa cikin ɗaki.
“Wai me ya same ki ne?” Zahara ta tambayi ƙawar tata.
“Kamar yaya me ya same ni? Ke me ya same ki nayi miki kira kusan million baki ɗaga ba?"
Zahara fiddo wayarta tayi ta duba ta ga missed calls ɗin ƙawar tata duka duka sau biyar ne ta kira ta, amma ita da yake uwar zari ce sai tace sau million.
“Toh me yasa kika kira ni sau million?" Zahara ta tambaye ta tana ajiye jakarta. Zaunawa tayi bisa gado tana sauraron ƙawarta.
“Mijina ne ya shirya business dinner. Shine yake son muje tare." Ta faɗa har da ɗan tsallen murnarta.
“Kamar yaya mu?"
“Mu ! Ni dake mana!"
“Kun kwance daga ke har mijin naki. Toh ni me zan je nayi cen?"
“Meye ba zaki je kiyi ba? Shi yace na gayyace ki dan haka nayi kuma ki kiyayi cewa mijina mahaukaci ko kuma na fasa miki baki."
“Ki cewa mijinki naso zuwa amma.."
“A'a zan faɗa mishi kin ce masa mahaukaci kuma kin ce ba zaki zo ba saboda kin tsane shi. Tun da ya dawo daga tafiya, baki zo kika ganshi ba."
“Wallahi bakida hankali ! Toh ki faɗa masa duk abinda kika ga dama, ba zan je dinner ɗin ba domin na gaji."
Tashi Zahara tayi ta fara tuɓe kayanta.
“Wai Zahara me yake damunki ne?" Maryam ta tambaye ta.
“Komai, kawai na gaji ne kuma bacci nake son yi."
“Eh amma wannan dinner tanada muhimmanci gare ni. Ina son yinta ne da mutanen da nake so, idan baki zo ba zan shiga damuwa sosai." Cewar Maryam. “Business dinner ce amma gaskiya zai je ne ya ga babban abokinsa da nima na sanshi da daɗewa. Kuma ba muga juna ba tun bayan bikina. Yana nan garin kuma zai yi wata haɗaka ce da mijina akan wani project. Dan Allah ki zo."
“Kenan, so kike...”
“A'a... ba abinda kike tunani bane. Ba muna son haɗaki da abokinsa bane amma idan kin ganshi kika ga yayi miki kuma shima kika mishi ni banga abun damuwa ba a ciki."
“Maryam...kin..kin fi kowa sanin ba zan sake kula wani namiji ba." Cewar Zahara.
“Wai wa yayi maganar zaki kula namiji. Kin ga je kiyi wanka mu wuce gidana dan mu shirya."
“Ban fa ce EH ba Maryam ! "
“Eh amma ai zaki ce ko? Oya je kiyi wanka, za'a yi a kare kuma mu maido ki gida lami lafiya."
“Shikenan... A ina za'a yi dinner ɗin?"
“A wani ƙayataccen restaurant babu nisa da nan. Wurin akwai kyau, amma sai kin hanzarta domin ƙarfe bakwai da rabi na yamman nan ne muka yi da su."
Komai ya tafi kamar yanda suka tsara, Zahara ta raka ƙawarta gidanta, a tare suka yin shirin zuwa dinner. Maryam da kanta ta yiwa Zahara kwalliya sannan ta ara mata wata kyakkyawar doguwar riga tata. Zahara tayi kyau sosai kuma ba'a iya gane ta a cikin rigar.
“Yayi kyau amma jina nake duk wani iri." Cewar Zahara.
“Kamar yaya?"
“Kamar damfara ce wannan, ba kyakkyawa bace ni !! "
“Yaushe zaki daina irin wannan Zahara? Kyakyawa ce ke, kawai kiyi amfani da wannan damar..."
Knocking ƙofa suka ji ana yi.
“Kuyi sauri ƴan mata, ina jiranku a mota."
“Ok my love, gamu nan zuwa..."
“Kin shirya?” Maryam ta tambayi Zahara.
Sai da ta ja dogon numfashi ta sauke sannan ta bata amsa.
“Eh, Muje."
Kan hanya, tafiya na yin kyau tsakanin mata da miji da ke ta zuba surutu da kuma Zahara da take a ɗan takure. Bayan wasu ƴan mintuna suka ƙaraso, nan Zahara ta fahimci lallai shigarta tayi daidai da zubin wurin. Baki sake take kallon wurin. Bata taɓa ganin wuri mai kyau ba irin wannan.
“Kin gani... na faɗa miki kyakkyawan guri ne." Maryam ta raɗa mata a kunne.
Gyaɗa kai Zahara tayi tare da yin murmushi a matsayin amsa. A tare suka shiga ciki, wani ma'aikaci ya tarbe su yana tambayarsu ko suna da reservation.
Mijin Maryam ne ya bada sunansa tare da faɗa masa suna da appointment ne ƙarfe bakwai da rabi. Bincikawa ma'aikacin yayi kafin yace su biyo shi.
Babban table ne ke jiransu a tsakiyar hall ɗin. Koda suka kusan ƙarasawa suka hangi wani matashin saurayi na jira. Zungurar Zahara Maryam tayi, Zahara ta ɗago domin ganin abinda ƙawarta ke son nuna mata.
“Sannu ku da zuwa.” Cewar saurayin.
“Habib, fatan baka jima kana jiranmu ba?” Mansoor mijin Maryam ya faɗa tare da rungumar abokinsa.
Bayan sun yi ƴan gaishe-gaishensu cikin nishaɗi da zolaya na yaushe gamo. Da yake Habib abokin Maryam ne na yarinta kuma ta girme shi da kusan shekaru biyu, tayi ta tsokanarsa tana tuna masa sunan banzan da ake masa da suna yara. Sai daga ƙarshe, Maryam ta gabatar da Zahara da Habib ga junansu.
“Habib, an jima rabon da mu ga juna." Cewar Mansoor yayin da ita kuma Maryam ke kallon Zahara da alamun tambayar ta ya taga Habib.
Zahara tayi kamar bata ga me Maryam take yi ba. Maryam na zaune ne suna fuskantar juna ita da Zahara yayin da shi kuma Habib ke fuskantar mijin Maryam. Hakan ke nuna Zahara na zaune kusa da Mansoor ita kuwa Maryam kusa da Habib.
“Haka ne amma kai ma kana yawan tafiye-tafiye bamu samun lokacin haɗuwa. Kuma idan ka dawo sai Madam tayi kidnapping ɗinta."
“Me kake son kace? Ni ma ai ina son ganin sa a kusa da ni.." Cewar Maryam.
“Eh amma ya kamata ki dinga barin lokaci su ma wasu su gan shi."
“Zaka gane idan kaima kayi auren." Cewar Mansoor.
“Wa ya sani ko har na samu.."
“Wai wa kai? Wacece zata soka? Wai Kanada ma budurwa?” Maryam ta tambaye shi.
“Yanda kika ce ! Wacece zata soni? Da wannan aikin da ya tauye ni yaushe na samu damar yin budurwar? Na bar miki wuka da nama ki samo min tsadaddiyar gwal."
“Tsadaddiyar gwal fa kace?" Maryam ta faɗa tana kallon Zahara.
Wata kunya ce ta kama Zahara taji kamar ta tashi ta ruga da gudu, murmushi tayi dan ta ɓoye yanayin da take ciki tana mai kallon decorations ɗin hall ɗin. Tana cikin yawo da idanunta, ta kai ga wani wuri da yasa taji kamar tayi layar zana ta ɓace daga wurin.
To be continued...
AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story📖
By Malik al-Ashtar 🖋
Table of Contents
Chapters
- 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
- 2 CHAPTER 1
- 3 CHAPTER 2
- 4 CHAPTER 3
- 5 CHAPTER 4
- 6 CHAPTER 5
- 7 CHAPTER 6
- 8 CHAPTER 7
- 9 CHAPTER 8
- 10 CHAPTER 9
- 11 CHAPTER 10
- 12 CHAPTER 11
- 13 CHAPTER 12
- 14 CHAPTER 13
- 15 CHAPTER 14
- 16 CHAPTER 16
- 17 CHAPTER 15
- 18 CHAPTER 17
- 19 CHAPTER 18
- 20 CHAPTER 19
- 21 CHAPTER 20
- 22 CHAPTER 21
- 23 CHAPTER 22
- 24 CHAPTER 24
- 25 CHAPTER 23
- 26 CHAPTER 25
- 27 CHAPTER 26
- 28 CHAPTER 27
- 29 CHAPTER 28
- 30 CHAPTER 29
- 31 CHAPTER 30
- 32 CHAPTER 31
- 33 CHAPTER 32
- 34 CHAPTER 33
- 35 CHAPTER 34
- 36 CHAPTER 35